Zakkar Kuxi

25519

Bayanin abin da ake nufi da kuxi

Kuxi

Su ne zinare da azurfa ko abin da yake a matsayinsu na kuxin takardu waxanda ake amfani da su a yau.

Hukuncin Zakkar Kuxi

Wajibi ce, saboda A’llah Mai girma da buwaya ya ce, “Waxanda suke taskance zinare da azurfa basa ciyar dasu saboda Allah, ka yi musu bushara da azaba mai tsanani” (Attauba : 34)

da faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “Babu wani ma’abocin zinare ko azurfa wanda ba ya bayar da haqqisu face sai ya kasance ranar alqiyama an mayar da su alluna na wuta, a gasa su a wutar Jahannama, sannan akan goshinsa da bayansa da gefensa da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a sake gasa masa su, a cikin wani yini tsawonsa shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai ya ga hanyarsa, ko dai zuwa Aljannah, ko kuma zuwa Wuta” [Muslim ne ya rawaito shi]

Sharuxxan Wajabcin Zakkar Kuxi

1 – Shekara ta kewayo a kansu.

2 – Cikakkiyar mallaka

3 – Su kai nisabi

Nisabin Zakkar Kuxi

1 – Nisabin zinare shi ne Dinari ashirin (85g).

Dirhami xaya na zinari = Giram huxu da kwata. Don haka lissafin nibin zinari da giram zai zama kamar haka: 4.25 × 20 = 85g na tacaccen zinari.

2 – Nisabin Azurfa shi ne Dirhami xari biyu (595g)

Dirhami xaya na azurfa = 2.975g. Don haka lissafin azurfa da giram zai zama kamar haka: 2.975g × 200 = 595g na tatacciyar a azurfa.

3 – Ana qaddara nisabin kuxin takarda ne a kan qimar zinare ko azurfa a lokacin da za a fitar da zakkar, idan kuxin ya kai nisabin xaya daga cikinsu (wato zinare da azurfa) to zakka ta wajaba.

Misali : Idan da za ce giram xin zinare shi ne yake daidai da Dala talatin ta amurka to zakka ta wajaba a kan wanda yake da Dala 85×30 = 2550 na dalar Amirika.

Zinare
Azurfa
Takardun Quxin

Gwargwadon Abin Da Ake Fitar Wa A Zakkar Kuxi

Abin da ya wajaba a fitar a zakkar zinare da azurfa da takardun kuxi shi ne rubu’in ushuri (2.5 %)

A cikin kowane dinari ashirin na zinare zai bayar da rabin dinare, sannan a ci gaba da xora lissafi a kan abin da ya qaru kaxan ko da yawa.

A cikin kowane dirhami xari biyu na azurfa zai bayar da dirhami biyar zakka. Sannan za a ci gaba da xora lissafi a kan abin da ya qaru, kaxan ko da yawa..

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan kana da dirhami xari biyu, shekara ta zagayo a kansu, to za ka ba da dirhami biyar, ba abin da za ka bayar idan kana da zinare har sai ya kai ashirin. Idan kana da dinare ashirin, shekara ta zagayo a kansu, to a cikinsu za ka ba da rabin dinare. Sannan abin da ya qaru a ci gaba da lissafi a kan haka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

- Misalin Yadda Ake Zakka A Aikace:

Mutum ne ya mallaki dala dubu tara, shekara ta zagayo wannan kuxin suna wajensa, shin zai ba da zakka?

Da farko za mu lissafa nisabin zakka a kan zinare da azurfa kamar haka :

Nisabin dai shi ne giram tamanin da biyar na tataccen zinare.

Sai mu qaddara cewa kowane giram na zinare ya yi daidai da dala talatin.

Sai mu buga giram 85 a kan 30, shi zai bamu dala 2550.

Don haka nisabin zakkarsa shi ne dala 2550, don haka dukiyar wannan mutumin ta kai yadda za a fitar mata da zakka, kuma shekara ta zagayo a kanta, zakka ta wajaba a kansa.

Na biyu : Sai mu lissafa abin da ya wajaba ya fitar :

Abin da zai bayar na zakkarsa shi ne rubu’in ushuri (2.5%)

Sai mu raba wannan kuxi da ya mallaka dala 9000 (2.5%) sai ya ba mu dala 225.

Don haka wajibi ne akan wannan mutumin ya fitar da zakkar dukiyarsa dala 225

Zakkar Kayan Adon Mata

Kayan adon mata kala biyu : kayan adon zinare da azurfa, da kayan adon da ba zinare da azurfa ba ne.

1 – Kayan Adon Zinare Da Azurfa

Kashi na farko : Kayan adon zinare da azurfa wadda aka tanada don ajiye wa da taskakewa, ko kuma don a yi kasuwanci da shi, to zakkar wajibi ce a cikinsa.

Kashi na biyu : Kayan adon zinare da azurfan da aka tanada don yin amfani da shi, abin da ya fi shi ne a fitar masa da zakka, don kuvutar da kai.

Saboda wata mata ta zo wajen Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) tare da ‘yar ta, ‘yar tana sanye da manya-manyan awarwaro na zinare a hannunta, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce wa matar: “Ko kina ba da zakkar waxannan awarwaron”. Sai matar ta ce, “A’a”. Sai ya ce mata : “Yanzu za ki so Allah ya yi miki awarwaron wuta da su ranar alqiyama” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Mai riwaya ya ce, “Sai ta jefa wa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) su, ta ce, “Na bayar da su ga Allah da Manzonsa ( صلى الله عليه وسلم )”.

Daga cikin malamai akwai wanda ba ya wajabta zakka a cikin kayan adon mata, saboda ba dukiya ba ce wadda take qaruwa, kurum wani abu ne na mutum da yake amfani da shi kamar riga da kayan gida, kuma kayan buqatar mata ne da adonsu. Ita kuwa zakka tana wajaba a qa’ida cikin dukiyar dake havaka.

Sai dai abin da ya fi taka-tsantsan shi ne fitar da zakkar kayan adon mata waxanda aka tanade su don amfani da kwalliya, don wannan magana, ta fi kuvutar da kai, sannan kuma Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce,“Ka bar abin da yake sa ka kokwanto zuwa ga abin bay a sa ka kokwanta” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Kayan Adon Zinare
Kayan Adon Azurfa

2 – Kayan Adon Da Ba Zinare Ba Ne Ba Azurfa Ba

Kamar dimond, yaqutu, lu’ulu’u da makamantansu, waxannan babu zakka a cikinsu, duk irin yawan da suka yi, sai dai in an tanade su don kasuwanci, sai su shiga cikin kayan kasuwancin da ake fitar wa da zakka.

lu'ulu'u da makamantansu
Dimond
yaqutu


Tags: