Zakkar Kadarar Kasuwanci

4968

Bayanin Abin Da Ake Nufi Da Kayan Kasuwanci

Kadarar Kasuwanci

Su ne duk abin da aka tanada don saye da sayarwa da nufin cin riba

An kira su da «Urudh” da larabci ne saboda ba sa tabbata, suna zuwa ne suna tafiya, don xan kasuwa ba hajar yake so ba, kawai yana son ribar ne da zai samu.

Kadarar kasuwanci ta haxa dukkan kayayyaki, banda tsabar kuxi, kamar motoci, kayan sawa, yadika, qarfe, katakwaye, da sauran duk abin da ka tanada don kasuwanci da shi.

Kayan sawa
Mota
Katakwaye
Qarfe

Hukuncin Zakkar Kayan Kasuwanci

Wajibi ce, saboda Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani ku ciyar da daxaxan abin da kuka nemo” (Albaqarah : 267).

Malamai sun ce wannan ayar tana nufin zakkar kayan kasuwanci. Hakanan da faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ka karvi sadaka daga cikin dukiyoyinsu” (Attaubah : 103)

dukiyar kasuwanci tana daga cikin dukiya, don haka zakka ta wajaba a cikinya.

Sharuxxan Wajabcin Zakkar Kadarar Kasuwanci

1 – Kuxin kayan ya kai nisabi. Ana qaddara nisabin ne da zinare da azurfa.

2 – Shekara ta zagayo a kansu.

3 – Ya zama an tanadi kayan ne don kasuwanci, da nufin neman kuxi da su, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Dukkan Ayyuka sai da niyya” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Idan ya canza niyya daga kasuwanci zuwa yin amfani da su, to lissafin shekara ya yanke, idan ya dawo ya yi niyyar kasuwanci sai ya fara sabon lissafin shekara, sai dai idan ya yi haka don dabarar qin zakka, to lissafin ba zai yanke ba.

Misali: Mutum ne ya sayi fili a cikin watan Muharram don kasuwanci, sai ya canza niyyar sayarwa zuwa ginawa don ya zauna a cikin watan Sha’aban, to lissafin shekararsa ya yanke.

Sai kuma a watan Shawwal ya dawo ya yi niyyar kasuwanci da wannan fili, to sai ya sake sabon lissafin shekara daga wannan wata na Shawwal.

In kuwa ya yi haka ne don dabarar kada ya ba da zakka, to lissafin shekarar ba zai yanke ba.

Yadda Ake Fitar Da Zakkar Kayan Kasuwanci

Idan shekara ta zagayo, sai a lissafa kayan a yi musu kuxi da farashin da ake sayarwa a wannan lokaci a kasuwa, sannan sai a fitar da zakkar daga kayan ko daga qimarsu, gwargwadon buqatar talakawa.

Yaya Xan Kasuwa Zai Lissafa Kayan Kasuwancinsa Don Yin Zakka?

1 – Zai qimanta duk abin da yake wurinsa na kayan sayarwar sa da farashinsu na wannan lokacin.

2 – Zai haxa da kuxin da yake da shi na kasuwanci, da waxanda ba na kasuwanci ba.

3 – Zai haxa da bashin da yake bi wanda ya san za a biya shi.

4 – Zai fitar da bashin da ake bin sa.

5 – Sai ya fitar da zakkar abin da ya rage, abin da zai fitar shi ne rubu’in ushuri (2.5%).

Ga yadda abin yake a taqaice : Abin da ake fitar wa da zakka (qimar kuxin kayan kasuwanci + kuxinsa + bashin da ya san za a biya shi – bashin da ake binsa) × (Abin da zai bayar (2.5%).

Zakka Daga Jarin Da Ake Juyawa :
Abin da ake ba da zakkarsa daga dukiyar kasuwanci shi ne kuxin da yake kai-kawo, wanda aka tanada don saye da sayarwa don neman riba, amma kuxin da yake kafe a wuri xaya, ba a lissafi da shi, ba a fitar masa da zakka, kamar kantocin kayan, da firjin da ake zuba kayan, da motocin da suke dakon kayan, da abubuwan da suke loda kayan, da makamantansu.
Mallakar Nisabi :

Shin sharaxi ne mallakar nisabi a tsawon dukkan shekara, tun daga farkonta har qarshenta. Ko kuwa za a wadatu da cikarsa a farkon shekara da qarshenta? Ko kuwa qarshen kawai za a kalla?

Amsa: Abin lura a wajen nisabi shi ne farkon shekara da qarshenta, domin akwai wahalar lissafi gabaxayan shekara. Sai aka yi la’akari da farkon shekara don lokacin ne zakka take wajaba. Shi kuma qarshekar shi ne lokacin fitar da ita. Abin da ya fi kamata musulmi ya tsayar da watan da zai riqa qimanta dukiyarsa da ba da zakkarta a cikinsa, kamar watan Ramadan. Yaya Xan

Zakkar Hannun Jari

Bayanin Hannun Jari

Hannun Jari

Wani Kaso ne daga cikin jarin Kamfani wanda aka raba daidai wa dai da.

Misali :A ce kamfani mai hannun jarin yana da jarin dala miliyan uku, Sai kamfanin ya kasa jarinsa zuwa kashi dubu goma, kowane kaso a dalar amuruka (300).

To wannan kason shi ake kira hannun jari. Duk wani mai kaso a nan to yanada tarayya tarayya a wannan kamafanin gwargwadon hannayen jarin da yake da a kamfanin.

Hukuncin Karvar Zakkar Hannun Jari

Halal ne, in dai kamfanin aikinsa ba na haramun ba ne, ko kuma yana mu’amala da riba.

Fitar Da Zakkar Hannun Jari

1 – Idan kamfanin ya fitar da zakka, to shike nan mai hannun jari a kamfanin ya huta, an sauke masa nauyi.

2 – Idan kuwa Kamfanin ba ya fitar da zakka, to sai a qimanta wannan hannun jari da farashinsa na lokacin, idan ya kai nisabi, kuma shekara ta zagayo a kansa to zai ba da zakkarsa rubu’in ushuri (2.5%), saboda kamar kayan kasuwanci ne.

Misali:Mutum ne yake da hannun jari dubu xaya, farashin hannun jari a lokacin zakkar shi ne dala dubu goma, sai ya zama farashin hannayan jarinsa shi ne dala dubu goma, wadda ta wuce nisabi, to zai ba da zakkar wannan hannun jari idan shekara ta zagayo.



Tags: