Sadaka ce da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya farlanta ta yayin da aka gama azumi.
Sadaka ce da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya farlanta ta yayin da aka gama azumi.
An kira ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gabaxaya.
Zakkar Fidda kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i xaya na abinci (kamar kwano xaya kenan) wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa.
Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma xan jaririn da yake cikin ciki.
Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga Xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i xaya na dabino, ko sa'i xayan da sha'ir, an wajabta ta a kan bawa, da xa, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya vullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana xaya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin Xan Umar wanda ya gabata in da yake cewa : “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.
Haka ma a cikin hadisin Abdullahi xan Abbas, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karvavviya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Kowane mutum sa'i [Sa'i xayan na Alkama yana daidai da kilo biyu da giram arba'in.] xaya ne, daga cikin abincin da xan mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ranar qaramar sallah”
Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi da cukwi [Cukwi : Shi ne nonon da ya bushe, a na girki da shi.], da dabino " [Bukhari ne ya rawaito shi].
Ana bawa waxannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin faxin Allah Maxaukakin Sarki “Kaxai Sadaka a bawa faqirai …”. (Attauba : 60)
1- Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa'ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin waxanncan maganganun haramun da ya yi, waxanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
2- Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake xauke da qasqanci da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.