Zakkar Dabbobin Ni’ima

7662

Bayanin Abin Da Ake Nufi Da Dabbobin Ni'ima

Dabbobin Ni'ima

Su ne, Raquma, Shanu, Awaki Da Tumaki.

Hukuncin Zakkar Dabbobin Ni'ima

Wajibi ce, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Babu wani ma’abocin Raquma ko Shanu, ko awaki da tumaki, wanda ba ya bayar da zakkarsu, face sai sun zo masa ranar alqiyama da girma da qiba da tozo, suna tunkuyinsa da qahonsu, suna taka shi da kofatansu, duk lokacin da na qarshensu suka qare sai na farko su dawo, har a yi wa mutane hukunci” [Muslim ne ya rawaito shi].

Sharuxxan Wajbacin Zakkar Dabbobin Ni'ima

1 – Dabbobin su shekara guda a wurin mai su, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Babu zakka a cikin dukiya har sai ta shekara”. [Ibnu Majah ne ya rawaito shi].

2 – Ta zama mai fita kiwo ce, saboda faxin Manzon Allah (r) “A cikin kowanne raqumi arba'in da suke fita kiwo za a ba da taguwa 'yar shekara biyu”. [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Abin da ake nufi da mai kiwo, ita ce dabbar da take kiwo a makiyaya, tana cin tsirran da suka fito a qasa, da ciyawar da Allah ya fito da ita ba tare da wani ya shuka ta ba. Amma idan abincin dabbar shuka shi aka yi, to wannan ba mai kiwo ba ce, babu zakka a cikinta.

3 – Dabbobin su zama an tanade su ne don samun nono da 'yaya, ba waxanda suke aiki ba ne. Masu aiki su ne wanda mai su yake amfani da su wajen noma ko ban ruwa, xaukar kaya ko xaukar abubuwa masu nauyi.

Raquman da ake aiki da su babu zakka a cikinsu, saboda suna cikin abin da mutum yake da buqata na yau da kullum, kamar kayan sawarsa.

Idan kuma an tanadi dabbobin ne don sayarwa, to zakkarsu za ta zama daga cikin kuxin da ake samu, cikin zakkar kayan kasuwanci idan shekara ta zagayo.

4 – Dabbobin su kai nisabin da shari'a ta ayyana

Nisabin Zakkar Dabbobin Ni’ima

Da farko : Nisabin Zakkar Raquma, Da Abin Da Ya Wajaba A Fitar Daga Cikinsu

An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Abubakar Assidiq – Allah ya yarda da shi – ya rubuto masa cewa : “Wannan ita ce farillar da Allah ya wajabtawa dukkan musulmi, Manzon Allah ya yi umarni da ita. A cikin kowane raquma guda ashirin da huxu zuwa qasa, cikin kowane guda biyar za a ba da akuya ko tunkiya, idan suka kai ashirin da biyar zuwa talatin da biyar za a ba da taguwa ‘yar shekara xaya, idan suka kai talatin da shida zuwa arba’in da biyar za a ba da taguwa ‘ya shekara biyu, idan suka kai arba’in da shida zuwa sittin za a ba da taguwa ‘yar shekara uku, ita ce wadda ta isa barbara. Idan suka kai sittin da xaya zuwa saba’in da biyar za a ba da ‘yar shekara huxu. Wanda bai da komai sai raquma huxu kawai, to babu zakka a cikinsu, sai dai in ya ga dama. Idan raquma suka kai biyar to za a ba da akuya ko tunkiya” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Nisabin Zakkar Raquma

Adadin Raquma Abin Da Za A Bayar A Cikinsu
5 – 9 Akuya ko tunkiya
10 - 14 Akuya biyu ko tunkiya biyu
15 –19 Akuya uku ko tunkiya uku
20 –24 Akuya huxu ko tunkiya huxu
25 – 35 Taguwa ‘yar shekara xaya
36 – 45 Taguwa ‘yar shekara biyu
46 – 60 Taguwa ‘yar shekara uku
61 – 75 Taguwa ‘yar shekara huxu
76 – 90 Taguwa biyu ‘yan shekara biyu – biyu
91 –120 Taguwa biyu ‘yan shekaru uku – uku
120 zuwa sama A cikin kowane arba’in za a ba da ‘yar shekara biyu, a cikin kowane hamsin yar shekara uku

Na biyu : Nisabin Zakkar Shanu, Da Abin Da Za A Fitar A Cikinsu

An karvo daga Mu’azu xan Jabal – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aike ni zuwa qasar Yaman, ya umarce ni in karva daga cikin kowanne shanu talatin saniya ‘yar shekara xaya, daga cikin kowane arba’in saniya ‘yar shekara biyu” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Nisabin Zakkar Shanu

Adadin Shanu Abin Da Za A Fitar Daga Ciki
30 - 39 Saniya ‘yar shekara xaya
40 - 59 Saniya ‘yar shekara biyu
60 - 69 Saniya guda biyu ‘yan shekara xai-xai.
70 – 79 Saniya ‘yar shekar xaya da ‘yar shekara biyu.

Na Uku : Nisabin Awaki Da Tumaki, Da Abin Da Za a Fitar

Hadisi ya zo daga Anas – Allah ya yarda da shi – wato hadisin da ya gabata, “Zakkar tumaki da awaki waxanda suke kiwo idan sun kai arba’in zuwa xari da ashirin za a ba da akuya ko tunkiya xaya, idan sun qaru a kan haka xari da ashirin zuwa xari biyu, za a ba da akuyoyi ko tunkiya biyu, idan suka wuce xari biyu zuwa xari uku, za a ba da guda uku, idan suka qaru a kan xari uku, to a kowanne xari za a ba da akuya xaya. Idan dabbobin da ake kiwo basu kai arba’in ba, guda xaya ce ta rage, to babu zakka a ciki, sai dai in mai su ya ga dama” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Nisabin Zakkar Awaki Da Tumaki

Adadin Tumaki Da Awaki Abin Da Za Bayar
40 – 120 Tunkiya ko Akuya
121 – 200 Tunkiya biyu ko Akuya biyu
201 – 300 Tunkiya biyu ko akuya biyu, idan su qara a kan haka, to a cikin kowanne xari za a ba da guda xaya.


Tags: