Zakkar Abin Da Yake Fitowa Daga Qasa

15318

Bayanin Abin Da Yake Fito Wa Daga Qasa

Abin Da Yake Fitowa Daga Qasa

Shi ne duk abin da yake fitowa daga qasa, kuma ana iya amfani da shi

Na Farko : ‘Ya ‘Yan Itace Da Qwayoyi

Bayanin Qwayoyi Da 'Ya'yan itace.

Qwayoyi

Shi ne dukkan qwayar da ake ajiyewa, ta sha'ir ko alkama da sauransu

'Ya'yan Itace

Su ne duk wani xan ice da ake ajiye wa, kamar dabino da zabibi da kwayar auduga

Hukincin Zakkar Qwaya Da ‘Ya’Yan Itace

Ba da zakkar qwaya ko ‘ya ‘yan itace wajibi ne, saboda faxin Allah mai girma da buwaya “Ku bayar da haqqinsa ranar girbinsa”(Al-an’am : 141)

Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Cikin abin da sama ta shayar, ko wanda yake da jijiya [Wanda yake da jijiya : Ita ce shukar da take shan ruwa da kanta, ko dai ta hanyar jijiyoyinta, ko kuma daga ruwan sama da qoramu] (yake shan ruwa da kansa) za a ba da kaso xaya bisa goma. Amma abin da aka shayar [Wanda aka shayar da ban ruwa, shi ne wanda aka sha wahala wajen fito da ruwan] da shi za a ba da rabin kashi xaya bisa goma” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Sharuxxan Wajabcin Zakkar Qwayoyi Da ‘Ya’yan Itace

1 – Ya zama za a iya ajiye shi :

Idan ya zama ba a ajiye shi ake ba, abinci ne na yau-da-gobe, to babu zakka a cikinsa, saboda abin da ba ajiye shi ake ba to ba dukiya ba ce cikakkiya, don ba za a iya amfanuwa da shi ba a gaba.

2 – Ya zama abin da ake aunawa ne :

Ma’ana ta zama ana aunata da ma’auni, don a qiyastawa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Babu Zakka a cikin qwaya ko dabino har sai ya kai wusiki biyar [Wuski shi ne : Sa’i Sittin] ” [Muslim ne ya rawaito shi] .

Saboda haka idan ba a auna abun kamar ganye (Salak da danginsa) ko kayan lambu, to babu zakka a cikinsu.

3 – Ya zama mutum ne ya shuka shi a gonarsa.

Idan abin ya fito da kansa ne to babu zakka a cikinsa.

4 – Ya kai nisabi :

Shi ne wusiki biyar, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Babu Zakka a cikin qwaya ko dabino har sai ya kai wusiki biyar” [Muslim ne ya rawaito shi].

Don haka nisabin sai ya zama sa’i xari uku, wanda ya yi daidai da (612kg) na kykkyawar alkama.

Ana iya haxa kala-kala idan dai iri xaya, don a samar da nisabi, kamar a haxa dabino wanda ake cewa “Sukkari” da wanda ake kira “Burji” misali, saboda duk dangi xaya ne.

Amma ba a haxa wani dangi daban da wani dangi don a samar da nisabi, kamar a haxa shinkafa da dabino.

- Ba a Sharxanta ba :

Ba a sharxanta cewa sai shekara ta kewayo a kan zakkar kayan gonaa da ‘ya’yan itace ba, saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “Ku ba da haqqinsa ranar girbinsa”. (Al an’am : 141)

Lokacin Da Yake Wajaba A Ba da Zakkar Qwayoyi Da ‘Ya’yan itace.

Zakkar qwaya na kayan gona tana wajaba daga lokacin da qwayar ta yi qwari. ‘Ya’yan itace kuma idan sun fara nuna, ta yadda za su iya zama yadda za a iya ci.

Wanda duk ya sayar da qwayar kayan gona bayan zakka ta wajaba a a kansu, to wannan zakkar tana kan mai sayarwa, saboda shi ne ya mallaki abin lokacin da zakkar da wajaba a cikinsu.

Gwargwadon Zakkar Da Ta Wajaba A Cikin Qwayar Kayan Gona Da ‘Ya’yan Itace.

1 – Kashi xaya bisa goma (10%) yana wajaba a cikin abin aka shayar da shi ba da wata wahala ba, kamar wanda ya aka shayar da ruwan sama ko qoramu.

2 – Rabin kashi xaya bisa goma (5%) yana wajaba cikin abin da aka shayar da wahala, kamar wanda aka shayar da ruwan rijiya.

3 – Kashi uku cikin kashi xaya bisa goma (7.5%) yana wajaba a cikin abin da aka shayar das hi da duka biyun, kamar wanda aka shayar da ruwan sama a wani lokaci, wani lokaci kuma da ruwan rijiya.

Dalili faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Cikin abin da sama da qoramu suka shayar za a ba da kashi xaya bisa goma, a cikin abin da aka shayar da raqumi kuma za a ba da rabin kashi xaya bisa goma” [Muslim ne ya rawaito shi].

Lalacewar Qwaya Ko 'Ya'yan Itace :
Idan qwayar kayan noma ko ‘ya’yan itace suka lalace ba tare da sakacin mai kayan ba, to babu zakka a kansa. Idan kuma shi ne ya lalata su da kansa bayan zakka ta wajaba a cikinsu, to zakkar tana nan a kanshi, wajibi ne ya bayar da ita.

Na biyu : Ma’adinai Da Dukiyar Da Aka Tsinta A Qasa

Bayanin Abin Da Ake Nufi Da Ma'adinai Da Dukiyar Da Aka tsinta A qasa.

Ma'adinai :

Su ne duk abin da ake fitar wa daga qasa, wanda ba jinsinta ba, kamar zinare, azurfa, qarfe, Jauhari, dalma da waninsu na abubuwan da ake fitar wa daga qasa.

Dukiyar Da Aka Tsinta A Qasa

Ita ce dukiyar da aka samu mutum ya binne ta, kamar zinare, azurfa, da sauransu.

Hukuncin Zakkar Ma’adinai Da Dukiyar Da Aka Tsinta A Qasa

Wajibi ce, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Yaku waxanda suka yi imani ku ciyar daga daxaxan abubuwan da kuka samu da kuma abin da muka fitar muku daga cikin qasa”(Al-baqarah : 267)

da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “A cikin dukiyar da aka tsinta a qasa za a ba da kashi xaya bisa biyar” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Sharuxxan Zakkar Dukiyar Da Aka Tsinta A Qasa

Babu wasu sharuxxai wajen fitar da zakkar dukiyar da aka tsinta a qasa, da mutum ya tsinta zai fitar da zakkarta kai tsaye.

Gwargwadon Zakkar Da Ta Wajaba Cikin Ma’adinai Da Dukiyar Aka Tsinta A Qasa

Kaso xaya bisa biyar ne ya wajaba, kaxan ce dukiyar ko da yawa, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “ A cikin dukiyar da aka tsinta a qasa za a ba da kashi xaya bisa biyar” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Zinare
azurfa
Ma’adanin Neckel
qarfe
Mas'aloli :

1 – Babu zakka a cikin Zuma, saboda babu wani abu da ya zo daga Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a kan haka, kaxai an samu wani abu ne da ya zo daga Umar – Allah ya yarda da shi – cewa ya kular masu da wuraren zuma, ya karvi kashi xaya bisa goma a wurinsu.

Don haka babu zakka a cikin zuma. Amma idan mutum ya fitar da ita don neman lada to wannan alheri ne, kuma zai iya zama dalilin havakar zumarsa.

Amma a ce wajibi ne mutum ya bayar da zakka a cikin zuma, idan bai yi ba ya yi laifi, wannan babu wani dalili a kan haka.

2 – Wanda ya karvi hayar gona, ya nomata, to zakkar gonar tana kan mai haya, ba a kan mai gonar ba.

3 – Karvar qimar zakka, ko karvar zakka daga kuxin dabino ko shuka idan an sayar, wannan bai sava wa shari'a ba, yana ma cikin shari'a idan akwai buqatar hakan ko wata maslaha.



Tags: