Yadda Aikin Hajji Da Umara

20814

Yadda Ake Hajji

Ayyukan hajji sukan fara daga ranar tara ga watan zul-hijja, ga yadda abun yake :

Ranar takwas ga watan zul-hajji (Ranar Tarwiyyah)

1 – Maniyyaci zai yi niyya daga inda yake, ya yi wanka, ya sanya turare, ya sanya kayan ihraminsa, ya ce, “Labbaikal Lahumma Hajjan, Labbaikal Lahumma Labbaik, Labbaika La Sharika Laka Labbaik, Innal Hamda Wanni’imata Lak Wal Mulk, La sharika Lak”[Bukhari ne ya rawaito shi]

2 – Maniyyaci zai tafi Mina, ya yi sallar Azzahar da la’asar, da magariba da isha da asubar wayewar gari. Kowace sallah zai yi ta a lokacinta, zai yi qasarun mai guda huxu, zai zauna a mina har zuwa vullowar alfijir xin ranar tara ga wata.

Wanka
Turare
Tufafin Ihrami
Mina

Ranar Tara ga Watan Zul-hijja (Ranar Arafa)

1 – Bayan rana ta vullo alhaji zai tafi Arafat, ya yi sallar azzahar da la’asar qasaru kuma a lokacin azzahar, ya isa masallacin Namira kafin rana ta yi zawali, in ya samu dama.

2 – Bayan ya gama sallah, sai ya shagaltu da zikiri da addu’a, yana mai fuskantar alqibla da xaga hannaye, zai zauna a arafa har zuwa faxuwar rana.

3 – Bayan rana ta faxi sai ya tafi zuwa Muzdalifa, ya yi sallar magariba da isha, ya yi wa isha qasaru, ya kwana a nan har zuwa vullowar alfijir.

Filin Arafat
Namira
Muzdalifa

Ranar Goma Ga Watan Zul-hijjah (Ranar Idi)

1- Zai sallar Asuba, sannan ya yi ta zikiri da addu’a har zuwa daf da vullowar rana.

2- Zai tafi Mina kafin rana ta vullo

3- Idan ya isa Mina, zai tafi wurin jifa, ya yi jifa da tsakuwowi guda bakwai a jere, xaya bayan xaya, yana yi kabbara tare da kowace tsakuwa.

4- Ya yanka hadayarsa idan akwai hadaya a kansa.

5- Ya aske kansa, ko ya yi saisaye, ya cire ihraminsa karo na farko, ya sanya kayan gida ya sa turare, duk abin da aka hana shi saboda ihrami ya halatta ya yi, amma ban da saduwa da mata.

6- Zai je Makkah, ya yi xawafin ifadah, shi ne xawafin hajji, ya yi sa’ayi tsakanin safa da Marwa idan tumattu’i yake yi, idan kuwa ba Tamattu’i yake ba, kuma dama can bai yi sa’ayi ba lokacin da ya zo yin xawafin qudum, to sai shi ma ya yi sa’ayi a wannan lokaci. Daga nan komai ya halatta a gare shi.

7- Zai koma Mina ya kwana a can.

Jifan Wurin Jifan Farko (Jamratul Aqaba)
Yanka Hadaya
Aski Ko Saisaye
Xawafi
Sa'ayi Tsakanin Safa Da Marwa
Kwana A Mina

Ranar Sha Xaya Ga Watan Zul-hijjah (Farkon Kwanakin yanyana)

1 – Zai jefi wuraren jifa guda uku, kowace majefa da duwatsu bakwai a jere, yana kabbara tare da kowace tsakuwa, zai jefi waxannan majefu ne bayan rana ta karkace ga sama (lokacin Azzahar) jifa baya hallata gabanin wannan lokaci.

Zai yi addu’a bayan ya jefi wurin jifa na farko da na tsakiya.

Wasu malaman sun iyakance girman tsakuwar da cewa ta fi kwayar wake kuma ba ta kai kwayar gujiya ba.

2 – Ya kwana a Mina

Wurin Jifa Na Tsakiya
Wurin Jifa Na Farko
Wurin Jifa Na Qarshe

Ranar Sha Biyu Ga Watan Zulhajji (Rana Ta Biyu A Kwanakin Yanyane)

1 – Zai jefi wuraren jifa guda uku, kamar yadda ya jefe su a jiya.

2 – Zai bar Mina kafin faxuwar rana in yana so ya gaggauta, ko kuma ya qara kwana in yana so ya jinkirta.

3 – Zai tafi Makkah don yin xawafin ban-Kwana.

Rana Ta Sha Uku Ga Watan Zul-hajji (Kwanar Qarshe A Kwanakin Yanyane)

Wannan rana ce da ta kevanta ga wanda ya jinkirta, zai yi abubuwa kamar haka :

1 – Zai jefi wuraren jifan nan guda uku, kamar yadda ya yi a jiya da shekaran jiya.

2 – Zai bar Mina, ya tafi xawafin ban-kwana.

Da ya yi wannan hajjinsa ya cika, ya gama aikin hajji.

Yadda Ake Yin Umara

1 – Idan mai umara ya isa miqati, sai ya yi wanka ya sanya turare, ya sa tufafin ihraminsa, ya yi niyyar umara ya ce, “Labbaika Umratan”.

2 – Zai fara talbiya yana cewa : “ Labbaikal Lahumma Labbaik, Labbaika La Sharika Laka Labbaik, Innal Hamda Wanni’imata Laka Wal Mulk, La Sharika Lak”[Bukhari ne ya rawaito shi] .

Ba zai gushe ba yana ta yin talbiyyah, har sai ya ga Ka’abah ya sumbaci baqin dutse.

3 – Idan zai shiga masallacin harami, ya fara da sa qafar damarsa, ya yi addu’ar shiga masallaci.

4 – Zai daina talbiyya, ya fara xawafi, ya fara da baqin dutse, ya sumbace shi in ya samu dama, in kuma bai samu ba sai nuna shi da hannunsa, ya ce, “Bismillahi, Wallahu Akbar, Allahumma Imanan bika, Wa tasdiqan bi kitabika, wa wafa’an bi ahdika, wattiba’an bi sunnati nabiyyika Muhammad (SAW)”[Baihaqi ne ya rawaito shi]

5 – Ya sanya xakin Ka’abah a hagunsa, ya yi xawafi sau bakwai, ya fara da baqin dutse ya qare da shi.

6 – Sunna ne namiji ya yi sarsarfa a xawafi uku na farko na xawafi.

Wanka
Turare
Tufafin Ihrami

7 – Zai yi addu’a a xawafinsa da abin da ya so, idan ya zo daidai da rukunul Yamani, sai ya tava shi ya yi kabbara, amma ba zai nuna shi ya yi kabbara ba idan bai samu dama ba, zai riqa cewa tsakanin rukunul yamani da baqin dutse “Rabbana Atina fit dunya hasanatan, Wa fil akhirati hasanatan, waqina azaban Nar”[Abu Dawud ne ya rawaito shi]

8 – Zai fita zuwa Safa, idan ya kusa zuwa wajenta, sai ya karanta faxin Allah “Lallai Safa da Marwa suna cikin wuraren ibada na Allah, duk wanda ya yi hajji ko umara babu laifi don ya yi xawafi gare su, wanda kuma ya yi aikin alheri na ganin dama to haqiqa Allah mai godiya ne masani” (Al-baqra : 158).

9 – Zai hau kan Safa, ya fuskanci alqibla, ya xaga hannayensa, ya yi kabbara ya gode wa Allah, ya ce, “La’ilaha Illal Lahu Wahadahu La Sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli shai’in qadir, Ayibuna, abiduna, sajiduna, lirabbina hamidun, sadaqal Lahu wa’adahu, wa nasara Abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu”[Bukhari ne ya rawaito shi]

Sannan ya yi addu’a bayan haka, ya maimiata wannan zikiri karo na biyu, ya yi addu’a, ya sake maimaitawa karo na uku.

10 – Zai sauka daga Safa ya fuskanci Marwa, ya yi gaggawa a tafiyarsa idan ya zo tsakanin alamomin nan koraye guda biyu, ya hau Marwa, ya yi kwatankwacin abin da ya yi a Safa.

11 – Zai yi sa’ayi tsakanin Safa da Marwa sau bakwai.

12 – Bayan gama sa’ayi namiji sai rage gashin kansa, ta yadda za a iya ganin kansa. Mace kuwa zata rage gefen gashin kanta daidai saman xan xan ‘yatsa.

Abi da ya fi ga namiji shi ne ya yi aski, saboda abin da ya tabbata daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah ka jiqan masu aske kansu gaba xaya (QwalQwal)” Sai sahabbai suka ce, “Da masu saisaye” sai Manzon Allah ya ce, “Allah ka jiqan masu aske kansu gabaxaya (Qwalqwal)” sai sahabbai suka ce, “Da masu saisaye” sai Manzon Allah ya ce, “Allah ka jiqan masu aske gashin kansu gaba xaya (qwalqwal) sai sahabbai suka ce, “Da masu saisaye” Manzon Allah ya faxi Masu aske gashinsu gaba xaya (qwalqwal) sau uku, sannan ya ce, “Da Masu saisaye”[Bukhari ne ya rawaito shi]

13 – Zai fita daga ihraminsa.

Da haka ne ya cika umararsa.



Tags: