Game abu da ruwa
Game abu da ruwa
Shi ne gama jiki gabaxayansa da ruwa, a kan wata siffa kevantacciya, da niyyar bautawa Allah Mai tsarki
Maniyyi wani ruwa ne fari mai kauri, wanda yake fita tare da jin daxi, yana tunkuxar juna yayin fitowa, mutuwar jiki tana biyo bayan fitarsa, yana wari irin warin bara-gurbin qwai.
Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka” (Alma’ida : 6)
da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Aliyyu : “Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Fitar da ruwa ana nufin fitar maniyyi.
- Mas'aloli ..
1- Idan mutum ya yi mafarki amma bai fitar da maniyyi ba, to babu wanka a kanshi, idan kuwa maniyyin ya fito bayan ya farka daga barcin to wajibi ne ya yi wanka.
2- Idan ya ga maniyyi, amma bai iya tuna yaushe ya yi mafarki ba, to wanka ya wajaba a kanshi saboda fitar maniyyin. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ana tava ruwa ne saboda fitar ruwa” [ Muslim ne ya rawaito shi] Ma'ana ana yin wanka ne don fitar maniyyi.
3- Idan ya ji alamar zuwan maniyyi daga gabansa, amma bai fito ba, to babu wanka a kanshi.
4- Idan maniyyi ya fito saboda wani dalili ko rashin lafiya ba tare da sha'awa ba, to babu wanka a kanshi.
5- Idan mutum yana janaba ya yi wanka, sai kuma maniyyi ya fito bayan ya gama wankan, to ba sai ya sake wankan ba, saboda yawanci yakan fito ne ba tare da sha'awa ba, amma abin da ya fi ya yi alwala.
6- Idan mai barci ya farka, ya ji danshi a jikinsa, amma bai san dalilin zuwanta ba, to xayan abu uku ne :
A) Ya tabbatar da wannan danshin maniyyi ne, to wanka ya tabbata a gareshi, ya tuna ya yi mafarki ko bai tuna ba.
B) Ya tabbatar wannan danshin ba maniyyi ba ne, to wanka bai wajaba a kanshi ba, hukuncinsa hukuncin fitsari ne, sai ya wanke)
C) Ya yi shakka, maniyyi ne ko ba shi ba ne? To a nan wajibi ne a kanshi ya yi kirdado, idan ya tuna abin da zai nuna masa cewa wannan danshin maniyyi ne, to ya bar shi a kan maniyyi ne. in kuma ya tuna abin da zai nuna masa cewa maziyyi ne, to maziyyin ne, in kuma ya kasa tuna komai, to sai ya yi wanka don fita daga savani da ruxu.
7- Idan ya ga maniyyi, amma bai tuna yaushe ya yi mafarkinsa ba, to wanka ya wajaba a kanshi, ya kuma sake dukkan sallar da ya yi bayan tashinsa daga barcinsa na qarshe.
Shi ne haxuwar gaban namiji da na mace, wato shigar kan gaban namiji gabaxayansa cikin farjin mace, ko da kuwa bai zubar da maniyyi ba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“Idan kaciyar (namiji) ta shige kaciyar (Mace) to wanka ya wajaba” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Saboda “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarci Qaisu xan Asim ya yi wanka lokacin da ya musulunta” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]
Saboda hadisin Aisha cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya cewa Faximatu ‘yar Abi Hubaish “Idan al’adarki ta zo, ki bar sallah, idan ya wuce ki yi wanka ki yi sallah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Hukuncin jinin biqi kamar hukuncin jinin haila ne da ijma’in malamai.
Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a hadisin wanke ‘yarsa Zainab lokacin da ta rasu ya ce,“Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko fiye da haka, in kun ga akwai buqatar hakan” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Abin da yake wajibi a wajen wanka shi ne gama jiki gabaxayansa da ruwa, tare da yin niyya, koma yaya ya yi shi.
Sai dai abin da aka fi so ya yi koyi da siffar wankan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ), kamar yadda uwar muminai Maimunatu ta siffanta shi, ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sanya ruwa don yin wankan janaba, sai ya karkato abin ruwan da hannun damansa a kan hagunsa ya wanke hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke gabansa, sai ya doki qasa ko bango da hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan sai ya yi kurkurar baki ya shaqa ruwa, ya wanke fuskarsa da sangalin hannunsa, sannan ya kwara ruwa a kansa, sai ya wanke jikinsa, sannan ya matsa gefe guda ya wanke qafafunsa. Nana Maimunatu ta ce, “Sai na kawo masa wani qyalle (hankici) amma bai karva ba, sai ya riqa share ruwan da hannunsa” [Bukhari ne ya rawaito shi].
- Yadda ake wankan a taqaice shi ne :
1- Zai wanke tafukan hannayensa sau biyu ko sau uku.
2- Zai wanke gabansa
3- zai doki qasa ko bango da hannu sau biyu ko sau uku.
4- Sai ya yi alwala irin ta sallah, ba tare da shafar kai da kunne ba.
5- Zai kwara ruwa a kansa
6- Zai wanke jikinsa gaba xaya.
7- Zai koma gefe ya wanke qafafunsa.
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Yaku waxanda suka yi imani kada ku kusanci sallah alhali kuna cikin maye har sai kun san abin kuke faxa, ko kuma in kuna cikin janaba har sai kun yi wanka sai dai ga wanda zai qetare hanya ya wuce”. (Annisa’i : 43)
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Xawafi ga xakin (Allah, kamar) sallah ne” [Nasa’i ne ya rawaito shi]
Saboda faxinsa Maxaukakin Sarki “Ba waxanda suke shafarsa sai waxanda aka tsarkake” (Alwaqi’a 79)
da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada wanda ya shafi Alqur’ani sai mai tsarki” [Malik ne ya fitar shi a cikin «Almuxxa».].
An karvo daga Aliyyu – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana fitowa daga banxaki, sai ya karanta mana Alqur’ani, ya ci nama tare da mu, babu abin da yake hana shi ko ya kange shi daga karatun Alqur’ani sai janaba” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Yaku waxanda kuka yi imani kada ku kusanci sallah alhali kuna cikin maye har sai kun san abin kuke faxa, ko kuma in kuna cikin janaba har sai kun yi wanka sai dai ga wanda zai qetare hanya ya wuce”. (Annisa’i : 43).
saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Wanda ya yi alwala don juma’a to madallah da ita, wanda kuwa ya yi wanka to wanka shi ya fi” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
An karvo daga Zaidu xan Sabit – Allah ya yarda da shi – “Haqiqa shi ya ga Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya cire kayansa don yin niyya, ya yi wanka” [ Tirmizi ne ya rawaito shi].
saboda faxar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) cewa, “Wanda ya yi wa gawa wanka to shima ya yi wanka” [Ibn majah ne ya rawaito shi].
An karvo daga Abu Rafi’i – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) wata rana ya kewaya matansa gabaxaya, yana wanka wurin wannan da waccan, ya ce, sai na ce, ya Manzon Allah, ba za ka sanya shi wanka xaya ba?, sai ya ce, “Wannan shi ya fi tsarki ya fi daxi, ya fi tsarkakewa” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
1 – Jinkirta wankan janaba har lokacin sallah ya fita.
2 – Mace ta qi yin sallar da ta wajaba a kanta bayan ta tsarkaka. Da za ta tsarkaka kafin lokacin sallar azzahar ya fita da gwargwadon raka'a xaya, to ya wajaba a kanta ta yi wanka ta yi sallar azzahar. Manzon Allah (r) ya ce, “Wanda ya samu raka'a xaya daga asuba kafin rana ta vullo, to ya riski sallar asuba. Wanda ya riski raka'a xaya daga la'asar kafin rana ta faxi, to ya riski la'asar” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].