Tsarki Da Ruwa

21982

Ma’anar Tsarki

Ma’anar Tsarki A Larabci.

Tsafta Da Tsarkaka Daga Kazanta

Ma’anar Tsarki A shari’a

Kawar da kari da gusar da Najasa

Kashe – Kashen Tsarki

1- Tsarki Na Voye

Shi ne tsarkake zuciya daga shirka da sabo, da duk wani abin da yake bata zuciya, babu yadda tsarki zai tabbata matukar akwai shirka a cikin zuciya, kamar yadda Allah ya ce, “Yaku wadanda suka yi imani ku sani cewa Mushirikai najasa ne, kada su kusanci masallaci mai alfarma daga wannan shekarar, idan kuna jin tsoron talauci to da sannu Allah zai azurta ku daga falalarsa in ya so. Haqiqa Allah Masani ne Mai hikima.” (At-Tauba : 28).

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mumini ba ya zama najasa”. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

2- Tsarki Na Zahiri

Shi ne tsarkake jiki daga abubuwan da suke warware alwala da najasa, ya kasu gida biyu :

1- Tsarkin Kari

Kari shi ne : Abin da yake hana mutum yin ibadar da aka sharxanta tsarki a cikinta, kamar sallah, dawafi da waninsu. Kari ya kasu kashi biyu :

Kari yana hana yin sallah.

- Qaramin Kari

Shi ne wanda yake wajabta yin alwala, kamar fitsari da kashi da sauran abubuwan da suke warware alwala. Tsarki daga kari yana samuwa ne ta hanyar alwala.

Allah ya ce, “Yaku waxanda kuka yi imani idan kun tashi za ku yi sallah, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwar hannu, ku shafi kawunanku ku wanke kafafunku zuwa idon sawu” (Al-ma’ida :6).

Alwala tsarki ce daga qaramin kari

- Babban Kari

Shi ne wanda yake wajabta wanka, kamar janaba, haila, da wanin haka, ana tsarkaka daga gare shi ta hanyar wanka.

Allah ya ce, “Idan kuna da janaba to ku yi tsarki” (Al-ma’ida : 6).

Tsrkin jiki

2- Tsarkaka Daga Najasa

Gusar da najasa wajibi ne, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Ka tsarkake tufafinka” (Al-Muddassir 4).

Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Mafi yawancin azabar qabari daga rashin yin tsarki ne idan an yi fitsari”. [ Ibn Majah ne ya rawaito shi]

Da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya zo masallaci to ya duba takalmansa, idan ya ga qazanta ko najasa to ya goge, sannan ya yi sallah da su”. [ Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Tsarkin jiki
Tsarkin wurin sallah
Tsarkin tufafi

Kashe-Kashen Ruwa

Na farko : Ruwa Mai Tsarki

Shi ne ruwan da najasa ba ta canza kamaninsa, ko xanxanonsa ko qanshinsa ba, kamar:

1- Ruwa Tsantsa

Shi ne ruwan da yake akan siffar shi da aka halicce shi da ita, kamar ruwan sama, ko qanqara, ko rava, ko kuma wanda yake gudu ne a bayan qasa, kamar ruwan teku, da qoramu da na sama, da rijiya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mun saukar da ruwa mai tsarki daga sama” (AlFurqan : 48)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Yana saukar muku da ruwa daga sama don ya tsarkake ku da shi” (Al-anfal : 11)

Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana addu’a yana cewa: “Ya Allah ka wanke ni daga zunubaina da rava da ruwa da qanqara[ Qanqara: Ita ce qanqarar da take zuba ya yin saurkar ruwan sama.]”. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Manzon Allah ya ce dangane da ruwan teku “Shi ruwa ne mai tsarki, kuma mushensa halal ne”. [ Ahmad da Abu Dawud ne suka rawaito shi]

Rijiyoyi
Ruwan sama
Qoramu
Tekuna

2- Ruwan Da Aka Yi Amfani Da Shi

Shi ne ruwan da yake zubowa daga jikin gavvan mai al’awa ko mai wanka, babu laifi a yi amfani da shi wajen yin tsarki, saboda abin da ya tabbata daga Abdullahi xan Abbas Allah ya yarda shi ya ce, “Xaya daga cikin matan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ta yi wanka wata kwatanniya, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya zo yana son ya yi alwala da sauran wannan ruwan, sai ta ce masa, “Ya Manzon Allah ni fa ina da janaba” sai ya ce, “Ai lalle wannan ruwan bai zama najasa ba”. [ Tirmizi ne ya rawaito shi]

3- Ruwan Da Ya Gauraya Da Abu Mai Tsarki

Shi ne ruwan da ya gauraya da wani abu mai tsarki, kamar ganyen bishiya, ko turvaya, ko ya haxu da tsatsa, kamar ruwan tankuna, amma abin da ya haxu da shi bai yi tasiri a kansa ba, tasirin da zai fitar da shi daga sunanshi na ruwa.

Saboda abin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya faxa wa matan da suke shirya ‘yarsa wadda ta mutu, ya ce musu : “Ku wanketa da ruwa da magarya sau uku, ko biyar, ko fiye da haka in akwai buqata [ Magarya: A nan ana nufin ganyen bishiyar magarya. ana dandaqa shi a yi amfani da shi wajen tsaftace abubuwa] . Ku sanya Kafur a wanki na qarshe”.[ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Ruwa da ya haxu da qasa
Tsatsar tankunan ruwa
Ruwan da ya gauraya da ganyen bishiya
Canzawar Ruwa
Idan ruwa ya canza da abin da ya yi masa tasiri, ya fitar da shi daga kasancewarsa ruwa zuwa wani abu daban, kamar ruwan shayi, lemo, ko waninsu, to ba ya halatta a yi tsarki da shi, saboda ba a kiransa ruwa.
Romo
Tauwada
Lemo
Shayi

4- Ruwan Da Ya Gauraya Da Najasa Amma Ba Ta Canza Shi Ba

Shi ne ruwan da najasa ta faxa masa, kamar fitsari, ko mushe da makamantansu, amma najasar ba ta canza wani abu daga siffofin ruwan ba, to wannan ruwan mai tsarki ne, saboda faxar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) game da wata rijiya mai suna “Buda’a” ya ce, “Lallai ruwanta mai tsarki ne, babu abin da ya mayar da shi najasa” [ Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito shi].

Abin nufi, mutane sun kasance suna jefar da qazanta kusa da wannan rijiyar, sai ruwan sama ya kora ta cikin rijiyar, amma ruwan saboda yawansa waxannan abubuwa ba sa tasiri a cikinsa, ba ya canza wa.

Na Biyu : Ruwa Mai Najasa

Shi ne wanda wani abu na najasa ya faxa cikinsa, kamar fitsari, ko mushe, ya kuma canza xaya da cikin siffofinsa uku – qanshinsa, ko xanxanonsa ko launinsa – to wannan ruwan ya zama najasa da ijma’in malamai, ba ya halatta a yi amfani da shi.

Mushe wanda ya canza ruwa
Mushe ya faxa ruwa bai canza shi ba
Mas’aloli

1 – Asali shi ne kowanne ruwa mai tsarki ne,saboda haka idan aka samu ruwan da ba a sani ba mai tsarki ne ko mai najasa ne? to asali shi ne mai tsarki ne, bai kamata a xorawa kai wata wahala ba.

2 – Ya halatta a yi alwala da ruwan zamzam,saboda Manzon Allah ya sa an kawo masa ruwan zamzam cikin guga xaya, ya sha ya yi alwala da shi.



Tags: