Taqaitaccen Bayani A Kan Aikin Hajji

8833

Makka A Da Da Yanzu

Makka

Suna ne da aka tsago shi daga kalmar "Bak" wadda take nufin kwari da yaren samiyyah.

Sunan Makkah ya zo da lafazin Bakkah, a cikin Faxin Allah Maxaukakin Sarki “Haqiqa farkon xakin da aka sanya wa mutane a bayan qasa shi ne wanda yake a garin Bakkah, mai albarka da kuma shiriya ga talikai” (Albaqara : 96).

Tarihin Makkah yana kowama wa zuwa qarni na sha tara kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) zamanin Sayyidina Ibrahim da Isma’il (A.S) waxanda su ne farkon waxanda suka zauna a cikinta,

Allah Ta’ala yana bamu labarin Annabi Ibrahim inda yake cewa “Ya Ubangiji na zaunar da zurriyata a wani kwari wanda ba shi da shuka wajen xakinka mai alfarma. Ya Ubangiji ka sanya zukatan mutane su riqa karkata zuwa garesu saboda su tsaida sallah, ka azurta su da ‘ya ‘yan itace ko sa yi godiya” (Ibrahim : 37).

Saboda falalar addu’ar Annabi Ibrahim ruwan zamzam ya vuvvugo daga qarqashin qafar Isma’il (A.S) lokacin da ruwa da abinci suka qare wa mahaifiyarsa Hajara, to tun daga wannan lokaci qabilu suka yi tururuwa zuwa wajen wannan ruwa, rayuwa ta miqe a cikin wannan gari.

Qabilu suka ci gaba da cincirondo da taruwa a wannan wuri, har lamarin ya kai quraishawa sune suke mulkin garin.

Haka quraishawa suka ci gaba da lura lamarin garin har zuwa bayyanar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ), wanda ya canza rayuwar Makkah da ma duniya gaba xaya.

An aiko Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a Makkah, Ka’aba kuma ta zama ita ce alqiblar Musulmi, Makka ta zama ita ce farkon wurin kiran musulunci, sai dai mutanenta sun fi kowa qin wannan kira, da guje masa, da azabtar da musulmi,

har lamarin ya kai musulmi suka yi hijira zuwa Madinah, daular musulunci ta kafu a can, sannan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya dawo ya buxe Makkah, ta zama babban garin musulunci tun daga wannan lokaci zuwa wannan zamani.

Garin Makkah ya samu kula mai yawa daga khalifofin musulmi da masu mulkinsu, musamman ma xakin Allah mai alfarma, sun yalwata garin Makkah, sun faxaxa shi, suka mayar da ita cibiyar da hasken musulunci yake fita daga cikinta zuwa duniya gabaxaya.

Falalar Makkah

1 – Aminci Ce Ga Wanda Ya Shige Ta

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wanda ya shige shi ya aminta” (Ali- Imran : 97).

Ana nufin Masallacin Makkah mai alfarma.

2 – Dujal Da Annoba Ba Sa Shiga Makkah

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Madinah da Makkah an kare su da Mala’iku, akan kowace qofa daga cikinsu akwai Mala’ika, Dujar ko Annoba ba sa shigar su” [Ahmad ne ya rawaito shi].

3 – Sallah A Masallaci Makkah Mai Alfarma Tana Daidai Da Sallah Dubu Xari.

An karvo daga Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Sallah a masallacin harami ta fi sallah dubu xari a wani masallacin wanda ba shi ba” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi].

4 – Ita Ce Wurin Da Allah Ya Fi So

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wallahi (makkah) ke ce mafi alherin qasar da Allah ya halitta, kuma ke ce mafi soyuwar qasa a wurin Allah” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

Makkah

Hukunce-Hukuncen Da Suka Kevanci Makka Da Masallacin Harami

1 – Alqawarin Azaba Mai Tsanani Ga Wanda Ya Yi Nufin Mummunan Aiki A Cikin Harami, Ya Yi Aikin Ko Bai Yi Ba.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Duk wanda ya yi nufin kaucewa da zalunci a cikinsa zamu xanxana masa azaba mai tsanani” (Al-Hajj : 25).

Kaucewa ana nufin savon Allah.

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mutanen da Allah da ya fi qi guda uku ne” daga cikinsu akwai ya ce : “Mai savo a cikin Harami” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2 – Haramta Yaqi Da Zubar Da Jini A Cikinta

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ka tuna lokacin da muka sanya xakin Allah ya zama matattarar mutane da aminci” (Albaqra : 125).

Duk wanda ya shiga Makkah to ya samu aminci a cikinta, saboda

haka Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Baya halatta ga wani ya xauki makami a cikin Makkah” [Muslim ne ya rawaito shi]

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa Allah ya haramta Makkah (ayi yaqi a cikinta) ba mutane suka haramta ta ba, don haka baya halatta ga wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya zubar da jini a cikinta, ko ya cire bishiya a cikinta” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Xaukar Makami A Cikin Harami

3 – Haramtawa Kafirai Da Mushirikai Shiga Cikin Harami

Allah ya ce, “Yaku waxanda kuka yi imani ku sani cewa Mushirika najasa ne, kada su kusancu masallaci mai alfarma bayan wannan shekarar da suke ciki” (Attaubat : 28).

Haka nan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni a yi shela a Mina cewa : “Bayan wannan shekarar kada wani mushiriki ya qara yin hajji, kada ya yi xawafin xakin Allah yana tsirara” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4 – Haramta Yin Farauta Da Yanke Bishiya Da Riqe Tsintuwa A Cikinta.

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Allah ya haramta Makkah, bata halatta ga wani ba gabani na ba, ko bayana ba, an halatta min ita wani xan lokaci na rana Ba a yanke ciyawarta, ba a yanke bishiyarta, ba a korar farautarta, ba a riqe tsintuwarta sai ga wanda zai yi sanarwa” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Wuraren Aikin Hajji

Wuraren Aikin Hajji

Su ne Alamomin zahiri da suka bambanta ibadar Hajji da waninta

1 – Arafat

Arafat, jam’i ne na Arafa, an kira ta da wannan suna saboda a nan ne Adamu ya gane Hauwa’u, ko kuma saboda mutane suna tabbatar da laifinsu a wurin.

Wuri ne da yake wajen harami, yana kudu maso gabas daga masallacin Harami da nisan kilo 22, tsawon faxinta Murabba’in kilo mita 10,4.Alhazai suna haxuwa a wurin ranar tara ga watan zulhijja.

Arafat

- Masallacin Namira

Namira wani dutse ne a yamma da masallaci, da sunan shi ne aka kira masallacin Namira.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sauka a cikin kwarin da ake kira «Wadi Urana» ya yi huxuba ya yi sallah, sai aka gina masallaci a

wurin da ya yi huxuba ya yi sallah a farkon zamanin khalifancin Abbasiyyah, an faxaxa shi da raya shi a zamanin daular Saudiya, har faxinsa ya kaisama da mita dubu xari da goma murabba’i.Alhazai suna haxuwa a cikinsa a ranar tara ga watan Zilhijja.

Masallacin Namira

- Masallacin Sakharat

Yana filin Arafat, qasa da dutsen rahama, a hannun damar mai hawa dutsen, a cikinsa akwai manya-manyan duwatsu, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya tsaya a wurinsu da yamma ranar Arafat. Alhazai suna haxuwa a wurin a ranar tara ga watan zulhijja.

Masallacin Sakharat

- Jabalur Rahma (Dutsen Rahama)

Wani dutse ne qarami, ya haxa da wasu manya-manyan duwatsu. Yana nisan kilo mita 20 daga gabashin Makkah, samansa a daidaice yake.

Kuma yana da faxi,faxin mita 640Alhazai suna haxuwa a kanshi a ranar tara ga watan zulhijjah.

Jabalur Rahma (Dutsen Rahama)

2 – Mina

An kira ta ne da wannan sunan saboda jinin da ake zubarwa a cikinta.

Tana tsakanin Makkah da Muzdalifa daidai nisan kilo mita 7 arewa maso gabas daga masallacin Harami.

Alhazai suna kwana biyu a wurin, daren 11 da 12 na watan zulhijja ga wanda ya yi gaggawa, da daren 13 ga wanda ya yi jinkiri.

Mina wurin aikin hajji ne da yake cikin iyakokin harami, akwai masallacin a Khaif da wuraren jifa a wurin.

Mina

- Wuraren Jifa

Lafazin «Jamrat» yana nufin qananan tsakuwoyi

Wuraren jifa guda uku da suke Mina su ne, qaramin Wurin jifa na tsakiya da qaramin kuwa ya yi mita 200., wurin jifa na tsakiya, da wurin jifa na qarshe. Wasu ginshiqai ne na duwatsu a tsakanin wani kewaye guda uku.

Kuma su alamomi ne na wurin da Annabi Ibrahim ya jefi Shaixan a wurinsu. Nisan dake tsakanin wurin jifan qarshe da na tsakiya ya kai mita 247, tsakanin wurin jifa na tsakiya da qaramin kuwa ya yi mita 200.

- Masallacin Khaif

Yana daidai saman dutsen kudancin Mina, kusa da qaramin wurin jifa

Masallacin Khaif

3 – Muzdalifa

Muzdalifa wuri ne tsakanin Mina da Arafat, Alhazai suna kwana a wurin bayan sun sauko daga hawan Arafa.

A tsakiyar filin Muzdalifa akwai wurin da ake kira «Mash’arul Haram» shi ne wurin da ake so Alhazai su tsaya a wajen, suna roqon Allah, suna ambatonsa, suna gode masa, shi ne wurin kwanan alhazai bayan sun sauko daga Arafa bayan faxuwar ranar tara ga watan Zulhijjah.

Muzdalifa

4 – Masallaci Mai Alfarma

Shi ne xakin Allah, a cikinsa akwai wuraren ibada da yawa, mafi mahimmancinsu su ne :

- Ka’aba Mai Girma

Ka’abah mai girma tana da kusurwa huxu

- Dutsen Annabi Isma’il (Hijru Isma’il)

Shi ne vangaren arewa na xakin Ka’abah, wanda kuxin quraishawa suka yi musu kaxan wajen haxawa da shi cikin ginin Ka’abah yayin da suka sake ginin xakin, don haka sai suka yi wani xan gini a wurin, don nuna cewa wannan wurin ma yana cikin xakin Allah, sai dai wannan suna da ake kiran shi da shi (Hijru Isma’il) suna ne da mutane suka sanya shi, ba shari’a ba ce da zo da shi ba.

- Baqin Dutse Ko Wurin Shan Nono (Al-hajrul Aswad)

Yana nan a vangaren kudu na Ka’abah, daidai hagun qofar Ka’abah mai girma, dutse ne daga Aljannah. Ya karye babu abin da ya ragu daga cikinsa sai ‹yan qananan duwatsu kamar girman dabino guda takwas.

- Ar-Ruknul Yamaniy

Shi ne rukunin vangaren kudu maso yamma na Ka’abah, ana kiran shi da «Ar-ruknul Yamaniy» saboda yana saitin Yemen. Yana cikin abin da ya kevanta da shi yana kan qa’idar ginin xakin tun na farko, wanda Annabi Ibrahim da Annabi Isma’il suka yi.

- Wurin Da Ake Runguma A Jikin Ka’abah (Almultazam)

Shi ne wurin da yake tsakanin baqin dutse (Al-hajrul Aswad) da qofar Ka’abah, faxin wurin gwargwadon mita biyu ne, wuri ne na amsa addu’a, don haka an sunna ne yin addu’a a wurin tare da saka kumatu da qirji da hannaye da tafuka a wurin.

Hijru Isma’il
Baqin Dutse (Al-hajrul Aswad)
Arruknul Yamaniy
Wurin Da Ake Runguma A Jikin Ka’aba (Almul’tazam)


Tags: