Su ne : Xabi’u da abubuwan da Allah ya halicci mutane a kansu, waxanda da su ne mutum yake cika, ya zama mai kyan siffofi da kyakkyawar kama.
Su ne : Xabi’u da abubuwan da Allah ya halicci mutane a kansu, waxanda da su ne mutum yake cika, ya zama mai kyan siffofi da kyakkyawar kama.
An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Abubuwa goma suna cikin sunnonin Fixira : Rage gashin baki, cika gemu, yin aswaki, shaqa ruwa, yanke farce, wanke bayan gavvan ‘yan yatsu, cire gashin hammata, aske gashin mara, tsarkin ruwa, kurkurar baki”[Muslim ne ya rawaito shi].
Xan qaramin ice ne na itaciyar bishiyar Arak, da ake amafani da shi wajen goge haqora, don kawar da abin da ya maqale musu na abinci ko wari.
Asuwaki sunna ne a kowane lokaci, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Aswaki tsarki ne ga baki, kuma samun yarda ne daga Ubangiji” [ Ahmad ne ya rawaito shi].
Amm yin aswaki yana qarfafa a wurare masu zuwa :
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Ba don kada in matsantawa al’ummata ba, da na umarce su da yin aswaki a yayin yin kowace alwala” [Ahmad ne ya rawaito shi].
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Ba don kada in matsantawa al’ummata ba, da na umarce su da yin aswaki a wajen kowace sallah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
An karvo daga Miqdamu daga babansa – Allah ya yarda da su – ya ce, “na ce wa Aisha – Allah ya yarda da ita – me Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yake farawa da shi idan ya shigo gidansa?” Sai ta ce, “Aswaki” [Muslim ne ya rawaito shi.].
An karvo daga Huzaifa – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge [ yana goge bakinsa ana nufin yana cuccuxa shi da aswaki] bakinsa da asuwaki” [ Bukhari ne ya rawaito shi]
An karvo daga Aliyyu – Allah ya yarda da shi – ya yi umarni da yin asuwaki ya ce, Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa idan bawa ya yi aswaki, sannan ya tashi yana sallah, sai mal’iku su tsaya bayansa suna jin karatunsa, sai mala’ikan ya matso kusa da shi, har ya sanya bakinsa akan bakinsa, babu wani abu da zai fito daga bakinsa na Alqur’ani face sai ya zama a cikin cikin mala’ikan, don haka ku tsarkake bakunanku saboda Alqur’ani” [ Bazzar ne ya rawaito shi]
Shi ne shigar da ruwa cikin baki tare da jujjuya shi
Shi ne, shaqar ruwa zuwa hanci
Gusar da abin da ya fito daga gaba ko dubura da ruwa mai tsarkie
Abin da ake nufi a rage shi sosai, saboda ado da tsafta da savawa kafirai da yake cikin yin hakan.
Shi ne barin gemu da rashin tava shi
Shi ne aske gashin gaba
Shi ne gusar da fatar da ta lulluve kan azzakarin namiji
Ita ce rage xan naman dake gaban mafitsarar mace
Ana yi wa maza kaciya, su kuma mata ana xan rage wa ne, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Ummu Axiyya – Allah ya yarda da ita – “Ki rage xan kaxan kada ki cire gaba xaya (wajen yi wa mata kaciya) saboda ya fi sa kyawon fuska, kuma ya fi daxi ga miji” [ Hakim ne ya rawaito shi]
Kaciya wajibi ce ga maza, sunna ce ga mata.
Hikimar yi wa xa namiji kaciya shi ne, tsarkake gaban namiji daga najasar dake cikin wannan fatar da ta rufe gaban nasa. Ita kuwa mace hikimar yi mata kaciya shi ne samun kyawon fuskarta.
Shi ne yanke shi, kada a bar shi ya yi tsawo.
Shi ne gusar da gashin da ya fito a hammata, saboda tsaftace hamata da gusar da warinta.
Su ne, bayan gavvan ‘yan yatsu waxanda suke bayan tafin hannu
Wasu malamai sun qara duk wani wuri da qazanta ke taruwa, cikin kunne, wuya, da sauran sassan jiki