Shafa Akan Huffi Da Safa Da Karan-Xori Da Bandeji Da Makamancin Haka

9068

Na farko : Shafa a kan huffi da safa

Bayanin menene huffi da safa

Huffi

Shi ne takalmin fata

Safa

Ita ce wata aba saqaqqiya da ake sawa a qafa kafin sa takalmi.

Hukuncin Shafa a kan huffi da safa

An shar’anta yin shafa a kan huffi da safa, saboda hadisai masu yawa, daga cikinsu akwai hadisin da aka rawaito daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – lokacin da aka tambaye shi dangane da shafa a kan huffi, sai ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana shafa a kan huffinsa biyu” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito].

Sharuxxan Shafa a kan huffi da safa

1- Sanya su bayan an gama alwala : An karvo daga Mugiratu - Allah ya yarda da ita - ya ce, “Na kasance tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a wata tafiya, sai na yi nufin in cire masa huffinsa (yayin da zai yi alwala) sai ya ce, “qyale su, na sanya qafafuwa ne a cikinsu suna masu tsarki” Sai ya yi shafa a kansu” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito].

2- Ya zama (huffin ko safar) sun rufe idon sau, ba a shafar qasa da idon sawu, saboda nan ba ya cikin qafa.

3- Ya zama an yi (huffin ko safar) da abu mai tsarki.

4- su zama ya halatta a yi amfani da su, kada su zama da haramtattun abubuwa, kamar alhariri ga maza.

5- Shafar ta kasance a cikin lokacin da aka iyakance, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya iyakance lokacin shafa (Dare xaya da yini ga wanda yake zaune a gida, kwana uku ga matafiyi) ba ya halatta a qetare su.

6- Shafar ta zama yayin tsarki ne daga qaramin kari, ba babban kari ba, An karvo daga Safwan xan Assal - Allah ya yarda da shi - ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana umartar mu idan muna matafiya, mu yi shafa a kan huffinmu, kada mu cire su don bayan- gida ko fitsari, ko barci, har tsawon kwana uku, sai dai idan mun yi janaba” [Bukhari ne ya rawaito shi].

A nan ana nufin wajibi a kan mai janaba ya cire huffinsa idan zai yi wanka, ya mayar da su bayan ya gama.

Yadda Ake Shafa A Kan Huffi Da Safa

Ana shafar saman huffi ne da hannaye guda biyu, bayan an jiqa su da ruwa, tun daga ‘yan ‘yatsun qafa zuwa qwauri (idon sau) sau xaya, zai shafi qafar dama da hannun dama, qafar hagu da hannun hagu.

Ba a shafar qasan huffi, haka nan diddige, Aliyyu – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Da a ce addini ra’ayi ne, da qasan huffi shi ya fi cancanta a shafa fiye da samansa. Haqiqa ni na ga Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana shafar saman huffinsa” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Shafa da hannaye biyu

Tsawon Lokacin Shafa A Kan Huffi Da Safa

Dare xaya da yini ga wanda yake zaune a gida, kwana uku da dararensu ga matafiyi

Dalili a kan haka faxin Aliyyu – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sanya kwana uku da dararensu ga matafiyi, kwana xaya da dare xaya ga mazaunin gida” [ Nasa’i ne ya rawaito shi]

Yadda Ake Lissafa Lokacin Shafa

Lokacin shafa yana farawa daga shafar farko bayan yin kari, idan mutum ya sanya safarshi bayan ya yi alwala, sai ya yi kari (abin da yake warware alwala, da ya zo alwala) sai ya shafa a karon farko, to daga wannan shafar sai ya lissafa kwana xaya da darensa (wato awa ashirin da huxu).

Misali : Mutum ne ya yi alwala, bayan ya wanke qafafunsa, sai ya sanya safar shi, ya yi sallar asuba. Da qarfe goma na safe sai ya yi kari, alwalarsa ta warware, da qarfe sha xaya na safe sai ya yi alwala don ya yi sallar walha, ya yi shafa a kan safarsa, to daga wannan lokaci ya halatta ya ci gaba da shafa a kan safarsa har zuwa qarfe goma sha xaya na washegari. Wannan ga wanda yake mazaunin gida ba matafiyi ba, shi matafiyi yana da kwana uku da dararensu.

Abubuwan Da Suke Vata Shafa A Kan Huffi Da Safa

1- Qarewar lokacin shafar

2- Cire safar duka guda biyu ko xaya daga cikinsu

3- Samuwar babban kari. An karvo da Safwan xan Assal- Allah ya yarda da shi- ya ce, “ Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana umartar mu idan muna matafiya, mu yi shafa a kan huffin, kada mu cire su don bayan- gida ko fitsari, ko barci, har tsawon kwana uku, sai dai idan mun yi janaba” [ Tirmizi ne ya rawaito shi].

Shafar qasan huffi
Shafar diddige
Tuve safa yana vata shafar

Na Biyu : Shafa A Kan Karan-Xori Da Bandeji, Da Filasta.

Bayanin menene karan-dori da bandeji da filasta

Karan-xori

Shi ne abin da ake xaure karaya da shi, kamar filasta da karare da makamantansu

Bandeji

Shi ne abin ake lulluve ciwo ko quna da shi, na tsumma ko makamancinsa, don yin magani

Filasta

Abin da ake liqawa akan ciwo don yin magani

Dalilin Halaccin Shafa A Kan Karan-Xori

An karvo daga Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun fita wata tafiya, sai dutse ya samu wani mutum daga cikinmu ya fasa masa kai sannan kuma sai ya yi mafarki, sai ya tambayi abokansa “Shin akwai wani rangwame in yi taimama?” Sai suka ce masa “Ba wani rangwame, tunda dai za ka samu ruwa”. Sai ya yi wanka kuma ya mutu. Lokacin da muka zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) sai aka ba shi labari, sai ya ce, “Sun kashe shi, su ma Allah ya kashe su, ba za su tambaya ba tunda ba su sani ba, maganin jahilci tambaya. Kaxai ya ishe shi ya yi taimama, ya xaure wurin ciwon da qyalle ko tsumma, sannan ya yi shafa a kansa, ya wanke sauran jikinsa” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Sharuxxan Shafa A Kan Karan-Xori Da Bandeji Da Filasta

1- Sharaxi wajen yin shafa a kan bandeji kada a wuce wajen da ake yi maganin da kewayensa.

2- Ba sharaxi ba ne sanya karan-xori da bandejin ana cikin tsarki (alwala) kamar yadda ba sanya wani lokaci ba na shafar, matuqar dai yana da buqata to ya halatta ya yi shafar, a lokacin tsarki daga kari babba da qarami. Idan buqatar da gushe to wajibi ne ya cire, ya wanke gavar yayin da zai yi tsarki.

3- Dangane da filasta ko bandejin da za a iya cire shi cikin sauqi, za duba a gani :

A) Idan cire bandejin zai yi wu cikin sauqi, a wanke wurin ciwon ba tare da cutuwa, ko jinkirin warke wa ba, to sai ya cire ya wanke wurin, sannan ya mayar da shi.

B) Idan cirewar da wanke wurin ba zai yi wu, ba tare da an cutu ba ko an samu jinkirin warkewa ba, to sai ya yi shafa akan gavar da bandejin yake.

Yadda Ake Shafa A Kan Karan-Xori Da Bandeji

Idan mai yin tsarkin ya zo gavar da take da karan-xori ko bandeji sai ya wanke gefen wurin, sannan ya shafi dukkan kan karan-xorin ko bandejin, babu buqatar ya shafi bandejin da yake kan gavar da ba wajibi ba ne ya wanketa ba a cikin tsarkinsa.

Misali : Mutum ne aka sa masa bandeji a kan qafarsa har zuwa qwaurinsa, to zai shafi kan qafarsa ne, ba zai shafi qwaurinsa ba.

Yadda ake shafa akan filasta
Yadda ake shafa akan bandeji
Shafa a kan karan-xori


Tags: