Shi ne abin da ya rage a cikin kwano bayan an sha
Shi ne abin da ya rage a cikin kwano bayan an sha
A qa’ida duk abin da aka sha aka rage mai tsarki ne, sai dai abin da dalili ya nuna cewa najasa ne.
Saboda abin da ya tabbata na cewa “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana shan sauran Aisha – Allah ya yarda da ita – alhali tana cikin jinin al’ada, yana sanya bakinsa a inda ta sa bakinta ”[ Muslim ne ya rawaito shi]
Saboda abin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya faxa game mage yayin da ta sha ruwa daga wata kwarya, ya ce, “Lallai ita ba najasa ba ce, ita tana cikin masu kai-kawo a cikinku” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
sha ta rage, da abin alfadari da jakuna da namun daji da tsuntsaye suka sha suka rage mai tsarki ne, saboda qa’ida dukkan abubuwa masu tsarki ne, babu wani dalili da ya nuna najasar wannan abun, saboda kuma Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana hawan jakuna, kuma ana hawansu a zamaninsa.
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Tsarkin kwanon xayanku idan kare ya yi lallage [ Lallage : shi ne kare ya sanya harshensa a cikin kwano ya jujjuya shi, ko ya sha abin da yake ci ko bai sha ba.] a cikinsa, ya wanke shi sau bakwai, na farko da qasa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Qiyasi a kan kare, saboda alade da kare dukkansu najasa ne.