Ita ce (sallar) neman Allah ya shayar da ruwa bayan fari da qarancin ruwan sama
Ita ce (sallar) neman Allah ya shayar da ruwa bayan fari da qarancin ruwan sama
Sallar roqon ruwa sunnah ce mai qarfi, saboda aikin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) kamar yadda yake a hadisin Abdullahi xan Zaid – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fita zuwa wajen sallah, sai ya roqi (Allah ) shayar da ruwa, ya fuskanci alqibla, ya juya mayafinsa, ya yi salla raka’a biyu” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
An shar’anta sallar roqon ruwa idan qasa ta bushe, aka rasa ruwa, ko kuma ruwan qoramu da rijiyoyi suka qafe da makamancin haka.
Ana so ta zama bayan vullowar rana da xagawarta daidai tsawon mashi. Wannan lokaci galiban ya kasance bayan vullowar rana da minti ashirin, kamar lokacin sallar idi.
A sunna ana yin wannan sallah ne a fili, ba a masallaci ba, saboda haka Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aikata, sai dai in da larura.
1 – Sallar roqon ruwa raka’a biyu ce, ba tare da kiran sallah ko iqama ba, ana bayyana karatu a cikinta
2 – Mai sallar zai yi kabbara bakwai bayan kabbarar harama a raka’a ta farko, a raka’a ta biyu zai yi kabbara biyar, banda kabbarar xagowa daga sujadda.
3 – Mai sallar zai xaga hannayensa a kowacce kabbara, sannan ya godewa Allah, ya yabe shi, ya yi salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a tsakanin waxannan kabbarori.
4 – Bayan gama sallah liman zai yi huxuba guda xaya, zai yawaita istigfari da karatun Alqur’ani a cikinta, sannan ya yi addu’a da addu’o’in da aka samo daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) tare da naci da bayyana qasqantar da kai, da nuna buqata da qanqan ga Allah Maxaukakin Sarki. Ya xaga hannayensa sosai a wajen addu’ar.
5 – Liman zai fuskanci alqibla, ya juya mayafinsa, ya mayar da na vangaren dama a hagu, na hagu a dama, ya tsaya ya yi ta addu’a tsakaninsa da Ubangijinsa
1 – A fara da gabatar da wa’azi da tunatar da mutane kafin a yi ta, a faxa musu abin da zai tausasa zukatansu, da ambaton tuba daga zunubai, da mayar da kayan zalinci zuwa ga masu su, saboda savo sababi ne na hana ruwa, tuba da istigfari kuwa sababi na amsa addu’a da samun alheri da albarka.
Hakanan (liman) ya kwaxaitar da su akan sadaka, saboda sababi ce ta samun rahama.
2 – A sanya ranar da za a fita don yin sallar, saboda mutane su shirya.
3 – Sunna ne a fita zuwa sallar cikin nutsuwa da tsoron Allah da qasqantar da kai, da bayyana tsananin buqata ga Allah, saboda haka ba shar’anta yin ado da sanya turare ba saboda ita.
Abdullahi xan Abbas yana siffata fitar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) zuwa sallar roqon ruwa ya ce, “Haqiqa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fita ba a cikin ado ba, yana mai qasqantar da kai, da komawa ga Allah, har ya zo wurin da ake sallah” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
4 – Yawaita neman gafara da addu’a tare da xaga hannaye a huxubar sallar roqon ruwa.
Ana so a tsaya a cikin ruwa a farkon saukarsa, saboda aikin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) kamar yadda ya zo a hadisin Anas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Ruwan sama ya same mu, muna tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) . Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yaye rigarsa har ruwan saman ya tava shi. Sai muka ce, “Ya Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) Me yasa ka aikata haka?” Sai ya ce, “Saboda ruwan bai daxe da rabowa daga Ubangijinsa ba Maxaukakin Sarki” [Muslim ne ya rawaito shi].