Sallar Nafila

87063

Bayanin Mece ce Sallar Nafila

Sallar Nafila

Ita ce sallar da aka shar’anta yin ta amma ba ta wajibi ba

Falalar Sallar Nafila

1 – Sallar nafila sababi ne na Allah ya so bawa, ya zo a cikin hadisi qudisi Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Bawana ba zai gushe yana kusanta ta da nafilfili ba har sai na so shi, idan na so shi sai in zama jin sa da yake ji da shi, in zama ganinsa da yake gani da shi, in zama hannunsa da yake damqa da shi, in zama qafarsa da yake tafiya da ita. Idan ya roqe ni in ba shi. Wallahi idan ya nemi tsari na, wallahi zan tsare shi” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2 – Sallar Nafila tana cike gibin farillai. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Farkon abin da za a fara wa mutane hisabi da shi ranar alqiyama daga cikin ayyukansu shi ne sallah. Ubangiji mai girma da buwaya zai ce wa Mala’ikunsa – Alhali ya sani – “Ku duba sallar bawana shin ya cika ta ko ya rage?”. In ta cika, sai a rubuta masa ita cikakkiya, in kuwa wani abu ya ragu daga cikinta. Sai Allah ya ce, “Ku duba ku gani bawana yana da nafila?” Idan yanada nafila sai ya ce, “Ku cika wa bawana farillarsa daga nafilarsa”. Sannan a karvi sauran ayyukan akan haka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

3 – Sallar Nafila A Gida Ta Fi Falala :

Sallatar nafilfili a gida ta fi falala akan a masallatai, sai in nafilar da aka shar’anta wa jam’i ce, kamar sallar asham a watan Ramadan. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, «Mafificiyar sallar mutum, ita ce wadda ya yi a gidansa, sai dai in sallar farilla ce” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Ire-iren Sallar Nafila

Sallar nafila iri da yawa ce, mafi mahimmancinsu waxanda za su zo:

Na Farko : Nafilfili na dindindin

Su ne nafilolin da suke tare sallolin farillai, raka’o’i goma ne ko goma sha biyu, su ne :

- Raka’a biyu kafin asuba.

- Raka’a biyu ko huxu kafin sallar azzahar, da raka’a biyu bayanta.

- Raka’a biyu bayan sallar Magariba.

- Raka’a biyu bayan sallar Isha. An karvo daga Xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Na kiyaye raka’a goma daga wajen Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) : Raka’o’i biyu kafi azzahar, da raka’a biyu bayanta, da raka’a biyu bayan magariba a gidansa, da raka’a biyu bayan isha a gidansa, da raka’a biyu kafin sallar asuba” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Hakan nan irin wannan hadisi ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – sai dai ta ambaci raka’a huxu ne bayan sallar azzahar [Muslim ne ya rawaito shi].

Nafilar da ake yi kafin Sallolin Farillah Nafilar da ake yi bayan
Raka’a biyu Asuba --
Raka’a huxu Azzahar Raka’a biyu
-- La’asar --
-- Magariba Raka’a biyu
-- Isha Raka’a biyu

Mafi falala a cikin sunnonin dindindin, su ne waxanda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kiyayesu a zaman gida da tafiya, ita ce raka’a biyu kafin asuba (rakatayil Fajri) saboda hadisin Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) bai kasance yana tsananin kiyaye wani abu ba, kamar yadda yake kiyaye raka’a biyu kafin asuba (Raka’atayil Fajri)” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Ya hallata a taqaita su ba tare da barin wajibanta ba, saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana taqaita raka’o’in nan guda biyu na kafin sallar asuba, har ma ina cewa “Shin ya karanta fatiha kuwa?!” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Kamar yadda ya halatta a rama su, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Wanda bai yi nafilar asuba ba, to ya yi ta bayan rana ta vullo” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Bayan Isha
Rama Nafilar Asuba Da Rana
Bayan Magariba
Kafin Alfijir
Bayan Azzahar Da Bayanta

Abu Na Biyu : Sallar Wutiri

Hukuncin Sallar Wutiri Da Falalarsa

Sallar wutiri sunna ce mai qarfi, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa Allah wutiri ne, yana son wutiri, ku yi sallar wutiri yaku ma’abotan Alqur’ani” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Yadda Ake Sallar Wutiri

1 – Mafi qarancin wutiri shi ne raka’a xaya. Mafi yawancinsa kuma raka’a goma sha xaya ko sha uku. Zai sallaceta raka’a biyu biyu, sannan sai ya yi wutiri da raka’a xaya.

2 – Mafi qarancin cikakken wutiri shi ne raka’a uku : ya sallaci raka’a biyu sannan ya yi sallama, sannan sai ya sallaci raka’a xaya ya yi sallama. Kuma zai iya sallatar waxannan raka’o’in guda uku a haxe da tahiya xaya.

Ana so bayan ya karanta fatiha a raka’ar farko ya karanta suratul A’ala. A raka’a ta biyu ya karanta suratul Kafiruun, a ta uku ya karanta suratul Ikhlas, saboda abin da ya tabbata daga Ubayyu xan Ka’abu- Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana karanta “Sabbih hisma Rabbikal Aala” a raka’ar farko a wutiri, a cikin ta biyu yana karanta “Qul ya Ayyuhal Kafiruun”, A ta uku yana karanta “Qul Huwal Lahu Ahad” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Lokacin Sallar Wutiri

Tun daga sallar isha zuwa vullowar alfijir, amma yin sallar wutiri a xaya bisa ukun dare na qarshe shi ya fi falala, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Saboda Sallar qarshen dare ana halartarta” [Muslim ne ya rawaito shi].

Addu’a A Cikin Wutiri

An shar’anta yin addu’a a cikin sallar wutiri a raka’ar qarshe kafin yin ruku’u,[Abu Dawud ne ya rawaito shi] ko kuma bayan an xago daga gareshi,[Bukhari ne ya rawaito shi]

sai ya xaga hannayensa ya yi addu’a da abin da ya zo, daga cikin abin da ya zo faxin “Allahummah dini fiman hadaita, Wa’afini fiman aafaita, watawallani fiman tawallaita, wabarik li fima a’axaita, waqini sharra ma qadaita, fa innaka taqdi wala yuqda alaik, wala ya izzu man adaita, tabarakta rabbana wata aalaita”[Tirmizi ne ya rawaito shi].

Mas’aloli :

1 – A sunnah bayan ya gama wutiri zai ce,“Subhanal Malikil Quddus” [Ahmad ne ya rawaito shi]

sau uku, ya xaga muryarsa a na ukun, zai iya qara wa da cewa “Rabbil Mala’ikati Warruhu”.

2 – Ba a shar’anta shafar fuska bayan addu’a ba, a cikin wutiri ko a waninsa, saboda hakan bai zo daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) .

Rama Wutiri Da Rana
An shar’anta rama wutiri da rana, amma ana rama shi ne a cike, saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan sallar dare ta wuce shi, saboda ciwo ko waninsa, sai ya yi salla da rana raka’a goma sha biyu” [Muslim ne ya rawaito shi].

Abu Na Uku : Sallar Tarawihi

Tarawihi shi ne : sallar dare a cikin Ramadan, an kirata ne da (Tarawihi) saboda sun kasance suna hutawa a cikinta, a tsakanin kowace raka’a huxu, saboda tsawon sallar.

Falalar Sallar Tarawihi

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda duk ya tsaya a cikin Ramadan, saboda da imani da neman lada a wurin Allah, An gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi].

Hukuncin Sallar Tarawihi

Sallar Tarawihi sunna ce mai qarfi, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya shar’anta ta a watan Ramadan mai albarka, yayin da Manzon Allah ya yi ta a masallaci, shi da sahabbansa, a wasu darare, sannan ya barta saboda tsoron kada a wajabta ta a kansu, sannan sahabbai suka yi ta a bayansa [Muslim ne ya rawaito shi].

Adadin Raka’o’in Sallar Tarawihi

Abin da ya fi shi ne raka’a goma sha xaya, saboda shi ne adadin da ya fi yawa wanda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aikata, saboda faxin Aisha – Allah ya yarda da ita – lokacin da aka tambayeta,

yaya Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yake sallah? Sai ta ce “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) bai kasance yana qara wa ba, akan raka’a sha xaya, a cikin Ramadan ko a waninsa” [Bukhari da Muslim ne suka ya rawaito shi].

Sallar Tarawihi Da Niyyar Isha
Wanda ya makara bai yi sallar isha ba, ya zo ya samu mutane suna sallar tarawihi, to ya shiga tare da su da niyyar sallar isha, idan liman ya yi sallama sai ya cika sallarsa.

Mas’aloli

1 – Makaruhi ne mutum ya bar abin da ya saba yi na tsayuwar dare. An karvo daga Abdullahi xan Amru xan Asi – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ya Abdallahi kada ka zama kamar wane, da yana tsayuwar dare, sai ya daina” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Ana son idan mutum ya farka da daddare don yin sallar dare, ya tayar da matarsa, hakanan ita ma mace ta tayar da mijinta, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan mutum ya tayar da iyalansa suka yi sallah raka’a biyu gabaxayansu, za a rubuta su cikin masu ambaton Allah da yawa maza da mata” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Farkawa Daga Barci Don Yin Sallah

3 – Wanda barci ya rinjaye shi a cikin sallar dare, to ya bar sallar, ya kwanta, har barcin ya tafi daga gareshi. An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan xayanku ya yi gyangyaxi a cikin sallah, to ya kwanta har barcin ya sake shi” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Wanda barci ya rinjaye shi

4 – Mustahabbi ne yin istighfari da addu’a a xaya bisa ukun dare na qarshe, saboda abin da Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya rawaito, ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Allah yana saukowa sama ta duniya, a xaya bisa ukun dare na qarshe, ya ce, “Waye zai roqe ni in amsa masa? Waye zai nemi gafara in gafarta masa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Addu’a A Sulusin Dare Na qarshe

Na Huxu : Sallar Walha

Sallah ce da aka shar’anta ta a lokacin walaha.

salla lokaci

Lokacin Walaha shi ne, idan rana ta vullo ta xan xaga daidai tsawon mashi har zuwa da daf da karkacewar rana

Falalar Sallar Walha

Allah Maxaukakin Sarki ya ce a cikin hadisi qudusi : “Ya kai xan adam, ka yi min sallah raka’a huxu a farkon rana, ni kuma zan isar maka da qarshenta” [Muslim ne ya rawaito shi].

Adadin Raka’o’in Walha

Ya halatta a sallace ta raka’a biyu, ko huxu, ko shida, ko takwas, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aikata haka.

Na Biyar : Sallar Gaisuwar Masallaci

Raka’a biyu ce, an shar’anta ta ga wanda ya shiga masallaci kafin ya zauna.

Dalilinta faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan xayanku ya shiga masallaci, to ya yi raka’a biyu, kafin ya zauna” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Sallar farillah ko nafilar kafin sallah tana wadatar wa daga gareta, misali wanda ya shiga masallaci don sallar azzahar, sai ya yi nafilar kafin azzahar to ta isar masa, babu gaisuwar masallaci a kansa.

Na Shida : Sallar Istihara

Raka’a biyu ce da bawa zai yi idan ya ruxe cikin wani lamari, kafin ya yi abun. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana koya wa sahabbansa ita, kamar yadda yake koya musu sura daga cikin Alqur’ani.

Addu’ar Istikhara

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan xayanku ya yi nufin wani al’amari, to ya yi raka’a biyu, bana farillah ba, sannan ya ce, “Allahumma Inni Astakhiruka Bi ilmika, Wa astaqdiruka bi qudratika, wa as’aluka min fadlika, fa innaka taqdiru wala aqdiru, wata’alamu wala a’alamu, wa anta allamul Guyuub. Allahumma in kunta ta’alamu anna hazal amra khairul li fi deeni wa aamashi wa’aqibati amrii, au qala ajilu amri wa ajilihi, faqdurhu li, wayassirhu li, summa barik li fihi, wa inkunta ta’alamu anna haza amra sharrul li fi deeni, wa ma’ashi, wa aqibati amrii, au qala fi aajili amri wa ajilihi, fasrifhu anni, wasrifni anhu, waqdur liya khaira haisu kana, summar dini”. Sai ya faxi buqatarsa” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Alamomin Istikhara :
Ba laifi a maimata Istikhara, kuma ba sharaxi ba ne mai istikhara ya yi mafarkin da zai bayyana masa al’amarin da ya yi istikhara a kansa, kurum zai ci gaba da al’amarin da ya zava, wanda ya bawa Allah zavi a cikinsa, kuma babu zunubi a cikinsa ko yanke zumunci, in abun ya samu, to alheri ne, in kuma bai samu ba to hakan shi ya fi alheri.

Na Bakwai : Sallatar Raka’a Biyu Bayan Gama Alwala

Saboda abin da ya tabbata daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce wa Bilal a lokacin sallar Asuba “Ya Bilal faxa min aikin da ka fi sa rai a kansa a cikin musulunci [Qarar Takalmanka], saboda Ni na ji qaran takalmanka a gabana a cikin Aljannah”. Sai ya ce, “Babu wani aiki da na yi, na fi sa rai a kansa face Ni duk lokacin da na yi tsarki (alwala) da dare koda rana sai na yi sallaci abin da (Allah) ya rubuta min da wannan alwalar” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Na Takwas : Sakakkiyar Nafila

Ita ce nafilar da ba ta da lokaci da sababi qayyadadde.

An shar’anta yin sallar nafilar da bata da lokaci da sababi qayadadde a kowane lokaci, sai dai a lokutan da aka hana sallah a cikinsu.

Misalin Nafilfili Sakakku (Tsayuwar Dare)

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mafificiyar sallar bayan sallar farillah ita ce sallar dare” [Muslim ne ya rawaito shi].

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sake cewa : “A cikin aljannah akwai wasu xakuna, ana ganin bayansu daga cikinsu”. Sai wani mutumin qauye ya tashi tsaye ya ce, “Xakunansu waye ya Rasulallahi?” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Na wanda ya daxaxa zance ne, ya ciyar da abinci, ya lazimci azumi, ya yi sallah da dare a lokacin mutane suna barci” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Tsayuwar Dare A Likitance

Tsayuwar dare tana kawo qarancin sinadarin (cortisone) musamman ma kafin

farkawa daga barci da yan wasu lokuta, lokacin da ya dace da lokacin sahur (sulusin dare na qarshe) wanda hakan yana kare xagawa sikari a cikin jini, abin da yake da haxari ga masu ciwon suga.

musamman ma kafin farkawa daga barci da ‹yan wasu lokuta, lokacin da ya dace da lokacin sahur (sulusin dare na qarshe) ……..

Lokutan Da Aka Hana Sallah A Cikinsu

1 – Tun daga bayan sallar Asuba zuwa vullowar rana, har zuwa xagawarta daidai da tsawon mashi, mafi yawanci daidai da minti sha biyar da vullowarta.

2 – Daga Daidaituwar rana a sama har zuwa karkacewarta

3 – Daga Sallah la’asar har zuwa faxuwar rana.

Dalili akan haka hadisin Uqbatu xan Amir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Lokuta uku, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana hana mu sallah a cikinsu [Mu binne], ko mu binne mamatanmu a cikinsu (su ne) lokacin da rana da vullo har sai ta xaga [Ta bayyana a fili], da lokacin da garjin rana ya yi [Ta karkace], har sai ta karkace, da lokacin da ta karkace don faxuwa har sai ta faxi” [Muslim ne ya rawaito shi]

Yin Nafiloli Masu Dalili A lokutan Da Aka Hana
Ya halatta a yi sallah mai dalili – kamar gaisuwar masallaci da sallar jana’iza – koda a lokutan da aka hana ne.


Tags: