Sallar Masu Uzuri

11584

Bayanin Su Waye Masu Uzuri

Ma’abota Uzuri

Rashin lafiya, tafiya, tsoro

1 – Sallar Maras Lafiya

Dole ne akan maras lafiya ya yi sallah daidai iyawarsa, idan zai iya yin ta kamar yadda mai lafiya zai iya to ya zama wajibi a kansa ya yi, in kuwa ba zai iya ba, to sai ya yi yadda zai iya.

Wajibi ne akan maras lafiya ya yi sallah a tsaye in zai iya tsayuwa, idan ba zai iya tsayawa ba, to ya yi sallah a zaune, idan ba zai iya zama ba, to ya yi sallah a kwance akan gefensa, fuskarsa tana fuskantar alqibla, idan ba zai iya kwance akan gefe ba, to ya yi a rigingine, qafafunsa suna fuskantar alqibla in zai iya, in kuwa ba zai iya ba, to ya yi a gwargwadon halinsa.

Dalili kuwa shi ne abin ya gabata na faxin Allah “Ku ji tsoron Allah iya iyawarku” (Attagabun : 16).

Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Imran xan Husain – Allah ya yarda da shi – ya ce masa “Ka yi sallah a tsaye, in baza ka iya ba to a zaune, in baza ka iya ba, to a kwance akan gefenka” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Wasu Daga Hukunce-Hukuncen Sallar Maras Lafiya

1 – Idan maras lafiya yana salla a zaune, amma zai iya yin sujjada, to sujjada ta wajaba a kansa.

2 – Idan kuwa yana sallah a zaune, amma ya kasa yin sujjada, to ya yi nuni da jikinsa a ruku’u da sujjada, sujjadarsa tafi ruku’unsa qasa-qasa, idan nuni da jikinsa zai masa wahala, to sai ya yi da kansa, haka ma zai yi idan ya yi salla a rigingine, zai yi nuni da kansa.

3 – Idan yin alwala a kowace sallah zai yi wa maras lafiya wahala, ko kuma yin salloli a kan lokacinsu zai masa wahala, to yana iya haxa sallar azzahar da la’asar, magariba da isha, a lokacin xaya daga cikinsu, ko dai a lokacin ta farkon ko ta biyun, gwargwadon yadda ya fi masa sauqi.

4 – Sallah bata saraya daga kan maras lafiya matuqar yana cikin hankalinsa, saboda haka bai dace ga maras lafiya ya yi sakaci da sallah ba, don da’awar bashi da lafiya, don haka ya yi iyakar qoqarinsa wajen yin sallah.

5 – Idan maras lafiya yana suma tsawon wasu kwanaki sannan ya farfaxo, to zai yi sallah ne a lokacin da ya farfaxo gwargwadon yadda zai iya, kuma ba zai rama sallolin da suka wuce shi ba a lokacin sumansa, amma idan suman kaxan ne, na yini xaya ne ko kwana biyu, to wajibi ne a kansa ya rama sallolin da suka wuce shi, a duk lokacin da hakan ya sauwaqa a gare shi.

Yana sallah a zaune
Karatu
Ruku’u
Sujjada

2- Sallar Matafiyi

An shar’anta wa matafiyi yin qasarun sallloli masu raka’a huxu (Azzahar, La’asar, Isha) zuwa raka’a biyu, haka kuma zai iya haxa sallar azzahar da la’asar, magariba da isha, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Idan kuka yi tafiya a bayan qasa to babu laifi a kanku ku rage (qasaru) sallah, in kuna jin tsoron kada waxanda suka kafirta su fitine ku, haqiqa kafirai maqiyanku ne masu bayyana qiyayya”. (Annisa’i : 101).

Da abin da ya tabbata daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun fita tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) daga Madinah zuwa Makkah, ya kasance yana mana sallah raka’a bibiyu, har muka dawo” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Abin Da Ake Nufi Da Tafiya

Ita ce duk tafiyar da za a kirawo ta tafiya a al’adance, to wannan tafiya za a yi mata qasaru.

Sallar Qasaru

1 – Matafiyi zai fara qasaru da ya bar gidajen garinsu. Ba ya halatta ya yi qasaru a cikin gidan da yake zaune, saboda bai tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi qasaru ba har sai bayan ya fita (daga gari).

2 – Idan matafiyi ya isa wani gari, kuma ya yi niyyar zama kwana huxu ko sama da haka, to wajibi ne a kansa ya cika sallah.

In kuwa ya yi niyyar qasa da kwana huxu to ya hallata ya yi qasaru, idan kuwa bai niyyar wasu kwanaki qididdigaggu ba, kawai dai yana da wata buqata ce, duk lokacin da ya qare ta zai koma, to wannan ya halatta ya yi ta qasaru har sai ya dawo, koda kuwa lokacin ya wuce kwana huxu.

3 – Wajibi matafiyi ya cika sallah idan ya yi sallah bayan liman mazaunin gida, koda kuwa raka’a xaya ya samu a tare da shi.

4 – Idan mazaunin gida ya yi sallah bayan matafiyin da yake qasaru, to wajibi ne a kansa ya cika sallah bayan liman ya yi sallama

Haxa Salloli Biyu

1 – Ya halatta matafiyi da mara lafiya su haxa salloli biyu, azzahar da la’asar a lokacin xaya daga cikinsu, magariba da isha a lokacin xaya daga cikinsu. Idan ya haxa sallar ne a lokacin ta farko, to wannan shi ne “Jam’u Taqdim”, in kuwa ya haxa a lokacin sallah ta biyu, to wannan shi ne “Jam’u Ta’akhir”.

2 – Ya halatta ga wanda ya yi sallah a masallaci ya haxa sallah saboda ruwan saman da zai sha wahala da qunci (wajen dawowa masallaci a cikinsa).

Amma wanda yake yin sallah a cikin gidansa, kamar mata, ba a yi musu rangwamen haxa sallah ba .

3 – Ba dole ba ne qasaru da haxa sallah biyu su haxu a lokaci guda ba, za a iya haxa wa ba tare da qasaru ba, za a kuma iya yin qasaru ba tare da haxawa ba.

Sallar Matafiyi A Cikin Mota

1 – Idan sallar nafila ce ta inganta

da uzuri ko ba uzuri, saboda abin da ya tabbata cewa “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana yin sallar nafila a kan abin hawansa, duk inda abin hawan ya yi da shi” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2 – Idan kuwa sallar farilla ce

tana inganta idan ya kasance baya iya sauka kan qasa, ko kuma ba zai iya hawa ba idan ya sauka, ko kuma yana jin tsoron abokin gaba, da makamancin haka.

Sallar anan tana da kamanni da yawa, daga cikinsu akwai :

A – Ya zama zai iya fuskantar alqibla, kuma zai iya ruku’u da sujjada, kamar a ce yana cikin jirgin ruwa, to anan wajibi ne ya yi sallah yadda take, saboda zai iya yi.

B – Ya zama zai iya fuskantar alqibla, amma ba zai iya ruku’u da sujjada ba, to wajibi ne ya fuskanci alqiblar yayin kabbarar harama, sanna ya ci gaba da sallar duk inda motar ta yi da shi, yana mai nuni wajen ruku’unsa da sujjadarsa.

3- Sallar Tsoro

An shar’anta yin sallar tsoro a cikin kowane yaqi halattacce, a halin zaman gida ko a tafiya. Alqur’ni da Sunnah sun nuna halaccinta :

1 – Daga Alqur’ni faxin Allah Maxaukakin sarki : “Idan kana cikinsu, ka tayar musu da sallah, to wasu jama’a daga cikinsu su tsaya tare da kai, su xauki makamansu, idan suka raka’a xaya to su koma bayanku, xaya jama’ar waxanda ba su sallah ba su zo tare da kai, su shiga taitayinsu, su xauki makamansu” (Annisa’i : 102).

2 – Daga sunnah kuma : Aikin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) , a inda ya yi sallar tsoro da sahabbansa, haka ma sahabbansa sun yi bayansa.

Sallar Tsoro

Tsoron bai da tasiri akan adadin raka’o’i, idan a zaman gida ne za yi sallar kamar yadda take, idan kuwa a tafiya ne to za a yi ta ne qasaru, kurum abin da yake canza wa shi ne yadda ake yinta.

Siffofin daban-daban sun zo a kan yadda ake yin ta, kuma duk sun halatta.

Tsoron da yake sa ayi sallar tsoro, baya wuce xayan biyu :

Hali na farko : Tsoron harin Abokan Gaba

Za a iya sallar da kowacce siffa cikin siffofin da suka zo daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) . Siffar da ta fi shahara kuwa ita ce wadda ta zo a hadisin Sahlu xan Abi Hasmah – Allah ya yarda da shi – ita ce, liman ya kasa su kashi biyu,

kashi na farko su tsaya su fuskanci abokan gaba, suna gadin musulmi, xaya kashin kuma ya yi sallah raka’a xaya da su.

Idan liman ya miqe zuwa raka’a ta biyu, sai wannan jama’a xin ta yi niyyar barin liman, ta cika da kanta, ta yi sallama, sannan ta tafi ta fuskanci abokan gaba, don tsare musulmi, sai xaya jama’ar ta zo, ta yi raka’a ta biyu tare da liman,

idan ya zauna tahiya sai su tashi, su ciko da kansu, shi kuma yana jiransu, idan suka zauna suka yi tahiya, sai ya yi musu sallama. [Bukhari ne ya rawaito shi]

Wannan siffar ana yin ta ne idan a halin tafiya ake, ko kuma a halin zaman gida idan sallar asuba ce, amma idan a halin zaman gida ake, ko kuma sallar magariba ce, to sai liman ya yi raka’a biyu tare da jama’ar farko, sai su yi niyyar barinsa, su cika da kansu, su yi sallama, sannan su tafi, xaya

jama’ar ta zo, liman ya yi sallaci abin da ya rage tare da su, sannan sai su barshi idan ya zauna tahiyar qarshe, su cika sauran da kansu, sai idan sun zauna zaman tahiyar qarshe, sai ya yi salllama tare da su”.

Hali Na Biyu : Tsoron ya yi tsanani, ya zama ba za su iya yin sallar tsoro a irin siffofin da suka zo ba L

To irin wannan hali za su sallah ne a tsaye ko a kan abin hawansu, suna fuskantar alqibla in sun samu dama, in kuma ba su samu ba, to ko’ina su kalla, kamar yadda Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Idan tsoron ya fi haka tsanani su yi sallah a kan qafafuwansu ko akan ababen hawansu, suna fuskantar alqibla ko basa fuskanta” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Za su yi nuni ne a wajen ruku’u da sujjada. Zai yi sallah yana tafiya ko kuma yana cikin jirginsa ko kan dabbarsa, gwargwadon halinsa.

Misali a ce a cikin tsananin yaqi ko wanin haka, ta yadda liman ba zai iya yin sallah da waxanda suke tare da shi ba, kamar yadda aka saba, faxin Allah Maxaukakin Sarki yana nuna haka : “Idan kun ji tsoro to ku yi sallah a kan qafafuwanku ko a kan abin hawa”. (Al-baqra : 239).

Yana sallah a cikin jirgin sama
Yana sallah a cikin jirgin ruwa
Yana sallah a kan dabba
Sauqin Shari’ar Musulunci
Yana daga cikin babban abin da shari’ar musulunci da bambanta da shi sauqi da rangwame, da kawar da qunci. Wannan qa’ida ce gamammiya a shari’ar musulunci cewa «Wahala tana jawo sauqi».


Tags: