Sallar Kisfewar Rana Ko Wata

5981

Bayanin Mene ne Kisfewar Rana Da Wata

Kisfewar Rana

Shi ne, dishewar haskenta ko raguwarsa da rana

Kisfewar Wata

Shi ne dishewar haskensa ko raguwarsa da daddare

Hikimar Kisfewar Rana Ko Wata

Rana da wata ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, yana tsoratar da bayinsa da su, don su koma zuwa gare shi.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa Rana da Wata basa kisfewa don mutuwar wani ko rayuwarsa, kawai su ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, yana tsoratar da bayinsa da su, don haka idan sun kisfe ku ruga zuwa ga sallah” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Hukuncin Sallar Kisfewar Rana Da Wata

Sunna ce mai qarfi, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Haqiqa Rana da Wata ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, basa kisfewa saboda mutuwar wani ko rayuwarsa, don haka idan ku ga haka, ku roqi Allah, ku yi kabbara, ku yi sallah, ku yi sadaka” [Bukhari ne da Muslim suka rawaito shi].

Lokacin Sallar Kisfewar Rana Da Wata

- Lokacin Sallar Kusufi yana fara wa daga lokacin da aka samu kisfewar zuwa qarshenta.

- Mai sallar zai qarasa sallarsa koda kuwa kisfewar ta tafi. Ba a koma maimaita sallar idan an gama koda kuwa kisfewar bata tafi ba, kawai dai musulmi zasu ci gaba da addu’a da neman gafara.

Siffar Sallar Kisfewar Rana Da Wata

- An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Rana ta kisfe a zamanin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) , sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi wa mutane sallah. Ya tsaya, ya daxe a tsaye, sannan ya yi ruku’u, ya daxe a ruku’u, sai ya xago, ya daxe a tsaye amma ba kai tsawon tsayuwar farko ba. Sannan sai ya sake yin ruku’u, amma bai kai tsayin na farko ba, sai ya yi sujjada, ya daxe a cikin sujjada. Haka ya aikata a raka’a ta biyu kamar yadda ya yi raka’ar farko. Sannan ya juyo wajen mutane, a lokacin rana ta yaye, ya yi wa mutane huxuba, ya gode wa Allah, ya yabe shi, sannan ya ce, “Haqiqa Rana Da Wata ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, basa kisfewa don mutuwar wani ko rayuwarsa, idan kun ga haka, ku roqi Allah, ku yi kabbara, ku yi sallah, ku yi addu’a” [Bukhari ne ya rawaito shi].

- Saboda haka, idan aka samu kisfewar Rana Ko Wata :

1 – Za a kira mutane zuwa sallar da cewa : “Assalatu Jaami’ah”.

2 – Idan mutane suka taro, sai liman ya yi musu sallah raka’a biyu, zai bayyana karatu a cikinsu. A raka’ar farko zai karanta fatiha da sura mai tsawo, sannan ya yi ruku’u, ya tsawaita ruku’un, sannan ya xago ya ce, “Sami’al Lahu Liman Hamidah. Rabbana Wa Lakal Hamdu”.

- Sai ya sake karanta fatiha da surar da bata kai tsawon ta farko ba, sannan sai ya yi ruku’u, ya tsawaita ruku’un, qasa da na farko, sai ya xago yana mai cewa : “Sami’al Lahu Liman Hamidah. Rabbana Wa Lakal Hamdu”.

- Sannan sai yi sujjadu biyu masu tsawo, zai zauna a tsakaninsu ba tare da ya tsawaita zaman ba. Sai kuma ya tashi zuwa raka’a ta biyu, yana mai kabbara, ya yi raka’a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, wajen tsayuwa da ruku’u da sujjada, sai dai kada ta kai tsawon ta farko, sannan sai ya zauna, ya yi tahiya, ya yi sallama.

Sunnoni sallar Kisfewar Rana Ko Wata

1 – A yi ta a cikin jam’i. Idan mutum ya yi shi kaxai to babu laifi.

2 – Ta zama a masallaci, kuma babu laifi mata su halarceta.

3 – Tsawaita sallar. A daxe a tsayuwarta da ruku’unta da sujjadarta, sai dai in Ranar ko Watan ya yaye, sai a taqaita ta.

4 – Raka’a ta biyu tafi ta farko gajarta, a wajen tsayuwarta da ruku’unta da sujjadarta.

5 – Yin wa’azi bayanta, da tunatar da mutane ikon Allah, da bayanin hikimar kisfewar Rana ko wata, sannan da kwaxaitar wa wajen aikata xa’a da barin savo.

6 - Yawaita addu’a da qanqan da kai, da neman gafara, da yin sadaka, da sauran ayyukan nagari, har Allah ya yaye abin da ya samu mutane.

7 – Ya halatta a xaga hannaye sama a addu’ar sallar kisfewa, saboda hadisin AbdurRahman xan Samura – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Sai na zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) na same shi a gida, yana tsaye yana sallah, ya xaga hannayensa” [Muslim ne ya rawaito shi].

Faxakarwa :

1 – Ba a rama sallar khusufi idan ba a san da khusufin ba sai bayan tafiyarsa.

2 – Sanin dalilin yin khusufi ta hanyar ilimin zamani baya kore cewa ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah. Allah yana tsoratar da bayinsa da ita, saboda haka ya dace ga musulmi ya shagalta da bauta wa Allah da qasqantar da kai zuwa gare shi, ba wai ya shagalta da bibiyar khusufin ba. An karvo daga Abu Bakhrata – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Rana ta kisfe a zamanin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fito yana jan mayafinsa..” Wannan yana nuna tsananin tsoron Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga khusufi.

3 – Ana samun raka’a a sallar khusufi da riskar ruku’un farko, duk wanda ruku’un farko ya kubce masa, amma ya samu na biyu, to raka’ar ta wuce shi, sai ya ramata bayan liman ya yi sallama, kamar yadda aka yi ta.

4 – Ana yin sallar khusufi a cikin lokutan da hana sallah.

5 – Ba a shar’anta yin sallar khusufi ba, saboda samun labari kawai, har sai an gani quru-quru.



Tags: