Sallar Jana’iza

35062

Shirya mamaci

Ana son halattar wurin wanda alamun mutuwa suka bayyana a gare shi, da tuna masa faxin «La’ilaha Illal Lahu» saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku laqqanawa mamatanku Laa’ilah Illal Lahu” [Muslim ne ya rawaito shi].

Idan ya mutu a rufe idanunsa, a lulluve shi da mayafi, a gaggauta shirya shi da yi masa sallah da binne shi.

Hukuncin Yi Wa Mamaci Wanka Da Shirya Shi Da Binne Shi

Wanke mamaci da sanya masa likkafani, da yi masa sallah da binne shi, Farilla ne, idan wasu suka yi, sun xauke wa sauran laifi.

Hukunce-Hukuncen Jana’iza

1- Ya dace a zavi adali amintacce wanda ya san hukunce-hukuncen wanka, don yi wa mamaci wanka.

2- Za a gabatar da wanda mamaci ya yi wasiyya ya wanke shi, a wajen wanka, sannan makusantansa, idan sun san hukunce-hukuncen wanka, in kuwa ba su sani ba, a gabatar da wanda ya sani a kansu.

3- Namiji zai wanke maza, mace kuma zata wanke mata, miji da mata kowa zai wanke xan uwansa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ga Aisha – Allah ya yarda da ita – ya ce mata : “Mene ne zai dameki idan kika mutu kafina, in wanke ki, in sanya miki likkafani, in miki sallah, sannan in binne ki” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi].

Maza ko mata za su iya wanke yara qanana waxanda ba su kai shekara bakwai ba.

Baya halatta namiji ko mace su wanke kafiri, ko su xauki jana’izarsa, ko sanya masa likkafani, ko yi masa sallah, koda kuwa xan uwansu ne, misali kamar babansu.

4- Ba a yi wa wanda ya yi shahada a yaqi wanka, ba a sanya masa likkafani, ba a yi masa sallah, ana binne shi ne da tufafinsa.

5- Idan vari ya kai wata huxu, to za a yi masa wanka, a sanya masa likkafani, a yi masa sallah, saboda bayan wata huxu ya riga ya zama mutum.

6- Sharaxi ne ruwan da za a wanke mamaci da shi ya zama mai tsarki halatacce. Kuma ya zama an yi masa wankan a wuri kevantacce. Baya halatta duk wanda bai da alaqa da wankan ya zo wurin.

Yadda Ake Wa Mamaci Wanka

1- A sanya mamaci akan wani gado, sannan a rufe al’aurarsa, a cire masa kayansa, a rufe shi daga ganin mutane a wani xaki ko makamancinsa.

2- Ana son mai wanka ya lulluve hannayensa da wani qyalle a yayin wankan.

3- Mai wanka zai xaga kan mamaci, kamar zai zaunar da shi, ya sanya hannunsa akan cikinsa, ya tatsa, sannan ya tsaftace masa gabansa da duburarsa, ya wanke abin da yake wurin na najasa.

4- Zai yi niyyar wanka, ya yi bisimillah

5- Mai wanka zai yi wa mamaci alwala irin alwalar sallah, sai dai banda shaqa ruwa da face wa, kurum zai shafa ruwa ne a bakinsa da hancinsa.

6- Zai wanke kan mamaci da gemunsa da ruwan magarya, ko sabulu, ko makamancin haka.

7- Zai wanke vangaren dama, sannan vangaren hagu, sannan ya qarasa wanke sauran jikin

8- Ana so a wankin qarshe ya sanya kafur.

9- Za shafe jikin mamaci da tawul

10- Za kawar wa mamaci abin da aka shar’anta kawar wa, na farce da gashin hammata da na mara.

11- Ana kitsa gashin mace, a jefa shi bayanta.

Mai Wanka Yana xaga Kan Mamaci
Za a kwantar da mamaci akan wani gado
Wanda zai yi wa mamaci wanka zai nade hannayensa da qyalle
Mai wanka zai xan danna cikin mamaci da hannunsa ya tatse shi
Mai Wanka Yana Yi Wa Mamaci Alwala Irin Alwalar Sallah
Zai wanke kan mamaci da gemunsa da ruwa da magarya
Zai wanke vangarensa na dama sannan na hagu
Yana Tsane Mamacin Daga Ruwa

Faxakarwa

- Wajibi shi ne wanki xaya, idan an samu tsafta da shi. Amma mustahabbi ne a yi guda uku, koda kuwa xaya ya tsaftace mamacin.

- Idan wanke mamaci ya gagara saboda rashin ruwa, ko kuma saboda qunar dake jiki, to za a yi masa taimama da qasa.

- Ana son wanda ya yi wa mamaci wanka shi ma ya yi wanka, bayan ya yi masa

Sanya wa mamaci likkafani

1- Sunnah a yi wa namiji likkafani da mayafi uku, farare na auduga, wanda baya siffata fata, kuma yana rufe dukkan jiki, babu kuma wuce gona da iri a cikinsa.

Mace kuwa ana mata likkafani da tufafi biyar, na auduga, a sa kwarjalle da mayafi, da riga da mayafi biyu waxanda za a lulluveta da shi.

Yaro kuma ana yi masa likkafani da tufa xaya, amma halal ne a yi masa da uku, yarinya kuma a sa mata riga da mayafi biyu.

2- Za a kawo mayafan guda uku, ya sanya musu turaren wuta, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan zaku sawa mamaci turaren wata, ku sa masa shi wutiri” [Ibnu Hibban ne ya rawaito shi].

3- Za a sanya mayafan na guda uku, xaya kan xaya, sannan a sanya turaren kaafur ko anbar ko almisk ko makamancinsa, sai dai in mamacin yana cikin Ihrami ne, to shi baza sa masa turare ba, ba za a shafa masa ba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Kada ku shafa masa turare” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4- Za a kwantar da mamaci a kan waxannan mayafai, sannan sai a nannaxe shi a cikinsu, a xora bangaren hagu a dama, vangaren dama a hagu, haka ma za nannaxe mayafi na biyu, haka ma na uku, a sanya sauran a kansa a xaure don kada su watse. A kunce su yayin da za a binne shi.

5- Rufe dukkan jiki shi ne wajibi, idan ba a samu ba, sai ‹ya guntuwar tufa, wadda baza ta rufe dukkan jiki ba, sai rufe kai, a sanya ciyawar «Izkhir» a wajen qafafun, saboda abin Khabbab ya rawaito na qissar Mus’ab xan Umair ya ce, “Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarce mu mu rufe kansa, mu sanya ciyawa a wajen qafafunsa” [Bukhari ne ya rawaito shi]

6- Wanda ya mutu yana cikin Ihrami ana yi masa likkafani da tufafin ihraminsa, ba a rufe kan namiji, saboda faxin Manzo Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku wanke shi da ruwa da magarya, ku yi masa likkafani a tufafinsa biyu, kada ku sanya masa turare, kada ku rufe kansa, saboda za a tashe shi ranar alqiyama yana mai talbiyya” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Rufe dukkan jiki
Ana yi wa mai ihrami likkafani a cikin tufafinsa
Sanya wa mayafin likkafani turare
Mayafi fari na auduga

Sallar Jana’iza

Rukunan Sallar Jana’iza

1- Tsayuwa idan da iko

2- Kabbarori huxu

3- karanta Fatiha

4- Salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم )

5- Yi wa mamaci addu’a

6- Jerantawa

7- Sallama

Sunnonin Sallar Jana’iza

1- Yin A’azu kafin fara karatu

2- Addu’a ga kansa da sauran musulmi

3- Voye karatu

4- Yawaita sahu, su zama uku ko fiye.

Siffar sallar jana'iza

Liman zai tsaya daidai kan mamaci in namiji ne, a tsakiya in mace ce, mamu kuma zasu tsaya a bayansa, kamar yadda ake sauran salloli, sannan ya yi kabbara huxu, kamar yadda zai zo:

1- Zai yi kabbarar farko, wadda ita ce kabbarar harama, ya yi A’azu, ya yi bismillah, ba zai yi addu’ar buxe sallah ba, sannan ya karanta fatiha.

2- Zai yi kabbara ta biyu, ya yi salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) irin salatin da ya zo a wajen tahiyar qarshe

3- Zai kabbara ta uku, ya yi wa mamaci da kansa addu’a, da sauran musulmi gabaxaya, daga cikin abin da zai ce, “Allahummag fir lahu, War’hamhu, wa’afihi wa’afu anhu, wa akrim nuzalahu, wawassi madkhalahu, wagsilhu bil ma’i wassalj, wal bard, wanniqihi minal khaxaya kama yunaqqas saubul abyadu minad danas, wa abdilhu daran khairan min darihi, wa ahlan khairan min ahlihi, wa zaujan khairan min zaujihi, wa adkhilhul Jannah, wa aizhu min azabik qabri au min azabin nar”. Ma’ana : “Allah ka yi masa gafara, ka jiqansa, ka ba shi lafiya, ka yi masa afuwa, ka girmama masaukinsa, ka yalwata mashigarsa, ka wanke shi da ruwa da qanqara da sanyi, ka tsarkake shi daga zunubai kamar yadda ake tsarkake tufa fara daga datti, ka canza masa gidan da ya fi na shi, da iyalan da suka fi na shi, da matar da tafi ta shi, ka shigar da shi Aljannah, ka tseratar da shi daga azabar qabri, ko kuma azabar wuta” [Muslim ne ya rawaito shi].

Idan mamacin yaro ne ko vari ne, sai ya ce, “Allahummaj alhu zukhran Li walidaihi, wa faraxan, wa ajaran, wa shafi’an li mujaban” Ma’ana : Ya Allah ka sanya shi ya zama tanadi ga iyayensa, da xan gaba (zuwa Aljannah) mai ceto, wanda ake amsa wa addu’a” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4- Zai yi kabbara ta huxu, sai ya yi xan shiru, sannan sai ya yi sallama xaya a damarsa, ko sallama biyu.

Xaukar Mamaci Da Raka Shi Da Binne Shi

Idan aka gama sallah, to sunna ne a yi gaggawar xaukansa zuwa qabari. Ana son wanda ya bi jana’izar ya yi tarayya wajen xaukanta, hakanan sunnah ne ga wanda zai shigar da mamaci qabari ya ce, “Bismillah, Wa’ala Millati Rasulillahi” Ma’ana : “Da sunan Allah, a kan addinin Manzon Allah” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Ya sanya mamacin a cikin lahadinsa (qabarinsa) a kan vangaren dama, fuskarsa tana kallon alqibla, sannan ya kwance qullin likkafanin, sai kuma a rufe bakin qabarin da bulo.

Sunna ne ga wanda ya zo wajen binnewa ya cika hannunsa da qasa, ya zuba a cikin qabarin sau uku, sannan zai rufe qabarin da qasa, a xaga shi daidai tsawon xani xaya, a sanya tsakuwowi da duwatsu a kai, a yayyafa ruwa, ba laifi a sanya dutse a gefen qabarin don ya zama alama.

Tarayya wajen xaukar jana’iza
Qabari (lahad)
Alama a kan qabari
Yana cika hannayensa da qasa yana zuba wa a kan qabari

Ta’aziyya

Ana son a yi wa dangin mamaci ta’aziyya, saboda hakan yana kwantar musu da hankali, ya sauwaqa musu musiba, da kwaxaitar da su a kan haquri.

Ta’aziyya tana inganta da kowanne lafazi, da zai biya buqata, kamar ya ce, “Abin da Allah ya karva na shi ne, abin da ma ya bayar na shi ne, kuma komai a wajensa yana da lokacin sanannane” [Bukhari ne ya rawaito shi] da makamancin haka.

Fitar Mata Zuwa Jana'iza
Fitar mata zuwa jana’iza ba shari’a ba ne, saboda abin da ya tabbata daga Ummu Axiyya – Allah ya yarda da ita – ta ce, “An hana mu bin jana’iza, amma ba tsananta mana ba” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi].

Ziyarar Maqabarta

An shar’anta wa maza ziyartar maqabarta don wa’azantuwa da addu’a ga mamaci, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Da na hanaku ziyartar maqabarta, ku ziyarce ta, haqiqa tana tuna muku lahira” [Muslim ne ya rawaito shi].

Daga cikin abin da ya zo na addu’a yayin ziyarar maqabarta akwai faxin “Assalamu Alaikum Dara qaumin mumina, wa inna in sha Allahu bikum lahiquna” [Muslim ne ya rawaito shi]

Ko kuma ya ce, “Assalamu ala ahlil diyari minal mumina wal muslimeena, yarhamullahu mustaqdimina minna wal musta’akharina, wa inna in sha Allahu bikum lahiquuna” [Muslim ne ya rawaito shi].

“As’alu Laha lana wa lakumul Afiya” [Muslim ne ya rawaito shi]

Idan ya yi musu da addu’a da rahama da gafara da makamancin haka, ya halatta.

Abin Da Aka Hana A Jana’iza

1 – Kuka da ihu, da bayyana raki, da fushi da hukuncin Allah da qaddararsa.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mai kuka da ihu idan bata tuba ba kafin ta mutu, za a tashe ta ranar alqiyama, tana sanye da wandon narkakkiyar dalma” [Muslim ne ya rawaito shi].

2 – Yaga riga, da marin kumatu da ihu, da tsige gashi ko aske shi (saboda nuna baqin ciki).

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Baya cikinmu wanda ya doki kumatu, ko ya yaga riga, ko ya yi da’awa irin ta jahiliyya” [Muslim ne ya rawaito shi]

3 – Haskaka Maqabarta.

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya tsinewa mata masu ziyartar maqabarta, da waxanda suke riqon maqabarta masallaci da waxanda suke sa mata fitilu” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Baya halatta a haskaka maqabarta ko a yi mata fenti.

4 – Zama a kan qabari, ko yi masa fenti, ko gini a kansa

An karvo daga Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya hana a yi wa qabari filasta, ko a zauna a kansa, ko a yi gini a kansa” [Muslim ne ya rawaito shi].

5 – Neman albarka da qabarurruka, da yi masa xawafi, da roqon matattu biyan buqata,

yin hakan shirka ne idan ya qudurce cewa hakan zai amfane shi ko ya cutar da shi, saboda babu wani mai amfanarwa ko cutarwa sai Allah. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ka ce ni bana mallakar wa kaina amfani ko cuta, sai dai abin da Allah ya so” (Al-aaraf : 188).

Baya halatta a yi xawafi ga qabururruka

6 – Binne mamaci a masallaci, ko gina masallaci a kan qabarurruka, ko yin sallah zuwa gare su.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Allah ya la’anci Yahudu da Nasara, sun riqi qaburburan Annabawansu masallatai” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Wasu Daga Hukunce-Hukuncen Jana’iza

1- Wanda sallar jana’iza ta wuce shi, to sai ya yi wa mamacin salla kafin a binne shi, ko bayan an binne shi, saboda abin da ya tabbata daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a cikin qissar matar nan da take tsaftace masallaci, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi mata sallah a qabarinta [Bukhari ne ya rawaito shi].

2- Ana so a yi wa iyalan mamaci abinci, saboda sun shagala da abin da ya same su, ba za su iya yin abinci ba.

Dalili abin da aka rawaito cewa iyalan Ja’afar da wani ya mutu a cikinsu, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ku yi wa iyalan Ja’afar abinci, saboda abin da zai shagaltar da su ya zo musu” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Shirya abinci ga iyalan mamaci

3- Halal ne a yi wa mamaci kuka idan babu xaga murya a cikinsa, da fushi da qaddarar Allah. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) lokacin da xan sa Ibrahim ya mutu, ya ce, “Haqiqa ido yana hawaye, zuciya tana baqin ciki, ba zamu faxi wani abu ba, sai wanda Ubangijinmu zai yarda da shi. Haqiqa mu muna baqin cikin rabuwa da kai ya Ibrahim” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4- Wanda ya yi shahada a fagen yaqi, ana binne shi da tufafinsa da ya yi shahada da su, ba a masa wanka, ba a masa sallah, saboda abin da ya tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni abin ne shahidan Uhud a cikin jininsu, ba a yi musu wanka ba” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Ana binne shahidi a cikin tufafinsa

5- Idan mai ihramin aikin hajji ko umara ya mutu, to za a yi masa wanka, amma ba za a sa masa turare ba, ba za a rufe kansa ba, za a yi masa sallah, saboda abin da ya tabbata daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce dangane da mutumin nan da ya mutu yana cikin ihramin aikin hajji, ya ce, “ Ku wanke shi da ruwa da magarya, ku yi masa likkafani a tufafinsa biyu, kada ku sanya masa turare, kada ku rufe kansa, saboda za a tashe shi ranar alqiyama yana mai talbiyya” [Bukhari ne ya rawaito shi]



Tags: