Sallar Jam’i

12236

Hukuncin Sallar Jam’i

Shari’a ta umarci maza masu iko da yin sallar Jam’i, ta tsawatar a kan barinta, kuma Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi niyyar ya qona gidajen waxanda basa zuwa sallar jam’i, haka kuma bai yi izini ga barin zuwanta ga makaho ba, dalili akan haka :

1 – Faxin Allah Mai girma da buwaya game da sallar tsoro : “Idan kana tare da su, ka tsayar musu da sallah, to wasu jama’a daga cikinsu su tsaya tare da kai” (Annisa’i : 102).

Anan zamu ga Allah Maxaukakin Sarki ya yi umarni da sallar jam’i a halin tsoro da tafiya, to halin zaman lafiya da aminci shi ya fi cancanta da sallar jam’i.

2 – Hadisin Abu Hurairata – Allah ya yarda da ita – ya ce, “Sallar da ta fi nauyi akan munafikai ita ce sallar isha da sallar asuba. Da sun san abin da yake cikinsu da sun zo musu koda da rarrafe. Haqiqa na yi nufin in umarci a yi kira sallah, a tayar da ita, sai in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan sai in tafi tare da wasu mutane, da tarin qirare a tare da su, in je wurin mutanen da basa zuwa sallah, in qona musu gidajensu da wuta” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ba zai qona gidajen waxanda ba sa zuwa jam’i ba sai don zuwa jam’in wajibi ne, haka nan ba sa a siffata waxanda basa zuwa jam’i da munafikai ba sai don wajibi ce.

3 – Hadisin makaho, wanda ya nemi izinin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a kan ya yi sallah a gida, saboda bai da jagora, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce masa, “Shin kana jin kiran sallah? Sai ya ce, “Eh” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “To ka amsa” [Muslim ne ya rawaito shi].

4 – Abin da ya tabbata daga Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Wanda yake son ya gamu da Allah gobe qiyama yana musulmi to ya kiyaye waxannan salloli (biyar) duk lokacin da aka yi kiran sallarsu. Haqiqa Allah ya shar’anta wa Annabinku hanyoyin shiriya, waxannan salloli suna cikin hanyoyin shiriya. Da zaku yi su a gidajensu da kun bar sunnar Annabinku, idan kuwa kuka bar sunnar Annabinku to kun vace. Babu wani mutum da zai yi tsarki, ya kyautata Tsarki, sannan ya tafi masallaci daga cikin masallatai, face sai Allah ya rubuta masa kyakkyawa da duk takun da ya yi, ya xaga masa daraja da wannan taku, an kankare masa zunubai da shi. Na gan mu babu wanda yake qin zuwa sallah sai munafiki sannanne. Tabbas ana zuwa da mutum yana tafiya tsakanin mutane biyu har a tsaida shi a cikin sahu”[Muslim ne ya rawaito shi].

Hikimar Sallar Jam’i Da Falalarta

1 – Sanin Juna da ‹yan uwa da abokai suke yi, da qarfafa danqon soyayya tsakaninsu, soyayyar da imani basa samuwa sai da ita, saboda babu wata hanya zuwa ga imani ko zuwa ga Aljannah sai soyayya saboda Allah.

2 – Kuvutar bawa daga munafunci da wuta ga wanda ya riski kabbarar harama tsawon kwana arba’in a jere, saboda abin da Anas – Allah ya yarda da shi – ya rawaito daga Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi sallah saboda Allah kwana arba’in a cikin jam’i, yana riskar kabbarar farko, za a rubuta masa kuvuta kala biyu : kuvuta daga wuta, da kuvuta daga munafinci” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

3 – Haxa kan musulmi, d a haxa zukatansu akan alheri da nagarta.

4 – Samun Taimakon juna tsakanin musulmi.

5 – Bayyana ayyukan addini da qarfafa shi

6 – Haxa kan zukatan musulmi, ta yadda za su haxu a sahu xaya, baqi da fari, balarabe da wanda ba balarabe ba, babba da qarami, mawadaci da talaka, zasu tsaya gefe da juna, a bayan liman xaya, a lokaci xaya, suna fuskantar alqibla xaya, da wuri xaya.

7 – Baqantawa maqiya Allah, saboda musulmai ba za su gushe ba da qarfi da kariya matuqar suna kiyaye sallah a masallatai.

8 – Kankare zunubai da xaga daraja, An karvo daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Bana nuna muku abin da Allah yake kankare zunubai ya xaga daraja da shi ba? Sai suka ce “Eh nuna mana ya Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ” Sai ya ce, “Kyautata alwala akan gavvai, da yawan taku zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wannan shi ne (Ribaxi) zama don Allah” [Muslim ne ya rawaito shi].

9 – Sallar jam’i tafi sallar mutum xaya da daraja ashirin da bakwai.

An karvo daga Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Sallar jam’i ta fi sallar mutum xaya da daraja ashirin da bakwai” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Sallar Jam’i a Gida
Bai halatta ga wani ko jama’a ba su yi sallar jam’i a gida alhali ga masallaci kusa da su. Amma idan masallacin yana da nisa, basa jin kiran sallah, to babu laifi a kansu su yi sallarsu jam’i a gida.


Tags: