Sadakar Taxauwu’i

5914

Bayanin Mece ce Sadakar Taxauwu'i.

Sadakar Taxauwu'i

Ita ce, sadakar nafila, ana yin ta ne don neman kusanci ga Allah da samun lada.

Da wannan bayani ne zamu ga kyauta da makamantanta na abin da ake bayar wa saboda qauna da soyayya ba sa cikin sadakar taxauwu’i, don haka hukunce-hukuncen sadaka bai shafe su ba.

Hukuncin Sadakar Taxawwa’i

Sadakar nafila Mustahabbi ce a kowane lokaci, musamman ma lokacin buqata, Allah Maxaukakin Sarki ya kwaxaitar da yin ta a cikin littafinsa mai girma, haka Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) shi ma ya kwaxaitar akan yin ta, misali :

- Faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Wanene zai bawa Allah rance, rance mai kyau, Shi kuma (Allah) ya ninninka masa zuwa ninki mai yawa”. (Al-baqara : 245)

- An karvo daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino na dukiyar halal – Allah ba ya karva abu sai mai tsarki – to Allah zai karvi wannan sadaka da hannun damansa, sannan ya rene ta ga mai ita, kamar yadda xayanku yake renon xan dokinsa, har ta zama kamar dutse don girma” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

- Hakanan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya lissafa wanda ya ba da sadaka a voye cikin mutum bakwai da Allah zai yi musu inuwa, ranar da babu inuwa sai inuwarsa, inda Manzon Allah( صلى الله عليه وسلم ) yake cewa : “Da Mutumin da ya yi sadaka ya voye ta, har ma hannun hagunsa bai san abin da hannun damansa ya ciyar ba” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi] .

- An karvo daga Ka’abu xan Ujrah – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Sadaka tana kashe laifuka kamar yadda ruwa yake kashe wuta” [Tirmizi ne ya rawaito shi] .

Ladubban Sadakar Taxauwu’i

1-Ladubban Tilas

A – Tsarkake niyya ga Allah Maxaukakin Sarki, ya ba da zakkarsa don neman yardar Allah, ba don riya ba ko don aji ba.

B – Nisantar gori da cutarwa ga wanda ake ba sadakar, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Yaku waxanda suka yi imani kada ku vata sadakarku da gori da cutarwa” (Albaqara : 264).

2-Ladubban Mustahabbi

A – Ana son musulmi ya yi sadaka ga 'yan uwansa mabuqata waxanda bai wajaba ya ciyar da su ba, kamar baffaninsa, da kawunnansa, da matar da mijinta faqiri ne da sauransu.

Yin hakan shi ya fi akan ya ba wasu, saboda Allah Maxaukakin Sarki yana cewa akan waxanda za a ciyar “Maraya ma'abocin kusanci” (Al-balad : 15)

Ya zo a cikin hadisi : “Haqiqa sadaka ga miskini sadaka ce guda xaya. Sadaka ga makusanci kuwa abu biyu ce, sadaka ce da sada zumunci” [Nasa'i ne ya rawaito shi].

B – Gaggauta bayar da ita, saboda hakan ya fi kusa da tsarkake niyya, kuma ya fi nisa daga faxawa cikin riya da son a ji, kuma ya fi zama girmama wa ga talakawa.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “In kun bayyana sadakarku to madallah da ita, in kuwa ku voye ta kuka bawa talakawa to wannan shi ya fi alheri”. (Albaqara : 271).

Idan a cikin bayyana sadaka akwai maslaha, kamar yin koyi da shi, da qarfafa waxanda suke wurin, to ana son bayyanawar, tare da lura da niyya da kiyaye ta.

C– Yin sadaka da abin da ya samu, koda kaxan ne. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, "Ku ji tsoron wuta koda kuwa da rabin dabino ne”[Bukhari ne ya rawaito shi].

Fa'idojin Sadakar Taxauwu'i

Na farko : Fa’idojin Sadakar Taxauwu’i Akan Mutum

1 – Tsarkake zuciya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu, ka tsarkake su ka gyara su da ita” (Attauba : 103)

2 – Koyi ne da Shugabanmu Muhammad ( صلى الله عليه وسلم ), saboda yana cikin halayensa kyauta da alheri, yana yin kyautar wanda ba ya tsoron talauci, yana cewa Bilal “Bilal ka ciyar, kada ka ji tsoron kaxan daga wajen Ma’abocin Al’arshi (Allah) [Talauci]” [Al-bazzar ne ya rawaito shi].

3 – Allah yana mayar da abin da aka ciyar, kuma wanda ya bayar ya qara samun xaukaka. Allah yana cewa : “Babu wani abin da zaku ciyar face sai Allah ya mayar da shi, shi ne mafi alherin masu azurtawa” (Saba’i : 39).

4 – Tsarkake dukiya ne daga haniyar ciniki. An karvo daga Qais xan Abi Garazata – Allah ya yarda da shi ya ce, “Mun kasance a zamanin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ana kiranmu dillalai, sai Manzon Allah ya wuce ta wurinmu, ya sanya mana sunan da ya fi kyau, ya ce mana “Ya taron attajirai, a cikin kasuwanci akwai yasassun maganganun da rantse-rantse, to ku gauraya shi da yin sadaka” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

5 – Samun lada da kankarewar zunubai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino na dukiyar halal – Allah ba ya karva abu sai mai tsarki – to Allah zai karvi wannan sadaka da hannun damansa, sannan ya rene ta ga mai ita, kamar yadda xayanku yake renon xan dokinsa, har ta zama kamar dutse don girma” [Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

6 – Ci gaba da amfanuwa da ladan sadaka mai gudana bayan mutuwa, An kavo daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Idan mutum ya mutu, ayyukansa sun yanke sai guda uku, sai sadaka mai gudana, ko ilimi da ake amfanuwa da shi, ko xa na gari da yake masa addu’a” [Muslim ne ya rawaito shi].

Na biyu : Fa’idodin Da Suka Shafi Al’umma Gabaxaya.

1 – Sadaka tana cika saqon da zakka take isarwa a cikin mutane.

2 – Samar da haxin kai da taimakon juna da soyayyya a cikin al'ummar musulmi



Tags: