rukunnan azumi| abubuwan da ke bata azumi| yadda ake azumi|

18682

Rukunan Azumi

Rukuni Na Farko : Kame Wa Daga Barin Abubuwan Da Suke Karya Azumi, Tun Daga Vullowar Alfijir Har Zuwa Faxuwar Rana

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ku ci, ku sha, har sai farin zare ya bayyana gare ku daga baqin zare. Sannan ku cika azumi zuwa dare” (Albaqara : 187).

Abin da ake nufi da farin zare da baqin zare shi ne, hasken rana da duhun dare.

Rukuni Na Biyu: Niyya

Ita ce mai azumi ya yi nufin kamewa daga abubuwan da suke karya azumi da niyyar ibada, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Dukkan ayyuka sai da niyya, kuma kowane mutum yana da sakamakon abin da ya niyyata” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Niyyar Azumi

Ya wajaba a kwana da niyyar azumi tun da daddare idan azumin na wajibi ne, amma idan azumin nafila ne to ba wajibi ba ne, saboda ya inganta a yi niyyar azumin nafila da rana indai bai yi abin da yake karya azumi ba, (kamar ci ko sha).

Saboda abin da aka rawaito daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya shigo wata rana, sai ya ce, “Ko kuna da wani abin ci? Sai muka ce, “A’a” sai ya ce, “To ina azumi” [Muslim ne ya rawaito shi].

Abubuwan Da Suka Halatta Ga Mai Azumi

1 – Yin wanka da zama a cikin ruwa don jin sanyi.

2 – Haxiye yawu da kaki.

3 – Xanxanar abinci da harshe, da sharaxin kada wani abu daga cikinsa ya wuce masa maqogwaro.

4 – Shaqar qanshi, da abubuwan da suke gyara yanayi

-Yin asawaki ga mai azumi

An shar’anta wa mai azumi ya yi aswaki a kowane lokaci, kafin zawalin rana ko bayansa, da xanye ko busasshe. Sai dai ya yi taka-tsantsan kada wani abu ya wuce masa maqogwaro, saboda hakan yana karya azumi.

An halattawa mai azumi ya yi wanka
An halatta wa mai azumi ya xanxana abinci
An halatta wa mai azumi ya shaqi qanshi
An halatta wa mai azumi ya yi asuwaki

Abubuwan Da Ake So Ga Mai Azumi

1 – Sahur Da Jinkirta Shi Zuwa Daf Da Kiran Sallar Asuba

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku yi sahur, a cikin sahur akwai albarka” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Hakan yana tabbata da cin abinci mai yawa ko kaxan, koda kuwa da kurvar ruwa ne, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Sahur abinci ne mai albarka, kada ku kyale shi, koda kuwa xayanku ya kurvi ruwa ne. Haqiqa Allah da Mala’ikunsa suna salati ga masu yin sahur” [Ahmad ne ya rawaito shi].

Ana son jinkirta sahur. An karvo daga Zaid xan Sabit – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun yi sahur tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) sannan muka tashi zuwa sallah” Anas xan Malik ya ce, “Yaya tazarar take tsakaninsu?” Sai ya ce, “Gwargwadon karanta aya hamsin” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

- Sha yayin da ake kiran sallah:

Idan mai azumi ya ji kiran sallah, kuma a hannunsa akwai abin sha, to zai iya qarasa shanye abin sa.

An karvo daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan xayanku ya ji kiran sallah, alhali kwanon sha yana hannunsa, to kada ya ajiye shi, har sai ya gama biyan buqatarsa daga gare shi” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Yin sahur koda kurvar ruwa ne

2 – Gaggauta Buxa Baki

Ana so mai azumi ya gaggauta buxa baki, da zarar ya tabbatar da rana ta faxi, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Mutane ba za su gushe da alheri ba, matuqar suna gaggauta buxa baki” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Ana son yin buxa baki da dabino wanda ba bushasshe ba, (Ruxab) , idan bai samu ba to sai ya yi da dabino bushasshe, kuma dabinon ya zama mara (uku, biyar d.s) idan bai samu ba,

to ya kurvi ruwa, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ya kasance yana buxa baki da dabino xanye kafin ya yi sallah, idan bai samu dabino xanye ba, sai ya yi da dabino busasshe, idan bai samu ba, sai ya sha ruwa” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Idan mai azumi bai samu abin da zai yi buxa baki da shi ba, to ya yi niyya a zuciyarsa cewa ya yi buxa baki, hakan ya isar masa .

Wanda ya karya azumi a bisa kuskure

Idan mai azumi ya ci abin ci, yana mai zaton rana ta faxi, ko kuma yana zaton alfijir bai vullo ba, amma sai savanin haka ya bayyana, to babu ramuwa a kansa, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Babu laifi a kanku cikin abin da kuka kuskure yin sa, amma abin da zukatanku suka yi da gangan (shi ne wanda Allah yake kama ku da shi) Allah mai yawan gafara ne mai jin qai” (Al-ahzab : 5).

Hakanan saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Haqiqa Allah ya xauke wa al’ummata laifin kuskure, da mantuwa, da abin da aka tilasta su a kai” [Ibn Majah ne ya rawaito shi].

3 – Addu’a Yayin Buxa Baki

Saboda ya tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan ya yi buxa baki yana cewa : “Qishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiqa, Lada ya tabbata in Allah ya so” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mai azumi yana da addu’ar da ba a mayarwa yayin buxa baki” [Ibn Majah ne ya rawaito shi].

4 – Barin Maganganun Banza Da Batsa

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan ranar azumin xayanku ce, to kada ya yi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi, ko ya yi faxa da shi, to ya ce, “ni mutum ne mai azumi” [Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi]

5 – Yawaita Ibada

Kamar karanta Alqur’ani, da ambato Allah (Zikiri) da sallar Asham, da tsayuwar dare, da tsayuwar daren lailatul Qadari, da nafilfili na yau da kullum, da sadaka, da kyauta, da bayar da buxa bakin ga masu azumi, da yin umara, saboda kyawawan ayyuka a cikin watan Ramadan ana ninninka su.

An karvo daga Xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi dukkan mutane kyauta, ya kasance lokacin da ya fi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake haxuwa da shi. Mala’ika Jibrilu yana haxuwa da shi a kowane dare a cikin Ramadan, ya yi karatun Alqur’ani tare da shi. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi kowa kyauta lokacin da Mala’ika Jibriru ya haxu da shi, ya fi iska sakakkiya kyauta” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Abubuwan Da Ake Qi Ga Mai Azumi

1 – Tsanantawa Wajen Kurkure Baki Da Shaqa Ruwa

Saboda kada ruwan ya wuce masa zuwa ciki, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ka shaqa ruwa sosai, sai dai idan azumi kake” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

2 – Sumbata Ta Sha’awa

Ba a so mai azumi ya yi sumbata idan da tsoron zubar da maniyyi ko ta da sha’awa.

Wajibi ne a kan mai azumi ya nisanci duk wani abin da zai tayar masa da sha’awa ya motsa ta. Idan ya amince da kansa cewa babu abin da zai faru gare shi in ya yi sumbar, to ba laifi ya yi.

An karvo daga Aishatu – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana sumbata, yana runguma alhali yana azumi. Ya fi kowa fin qarfin sha’awarsa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Saboda haka ba a so matashi ya yi rumguma. Amma tsoho babu komai. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Wani mutum ya tambayi Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) dangane da mai azumi ya yi rumguma, sai Manzon Allah ya yi masa rangwame. Sai wani mutumin daban ya zo, ya tambayi Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a kan hakan, sai ya hana shi. Sai ga shi wanda Manzon Allah ya yi wa rangwame tsoho ne, wanda Manzon Allah ya hana matashi ne” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Abubuwan da Suke Vata Azumi

1 – Ci da sha da gangan da rana a Ramadan

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ku ci ku sha, har sai farin alfijir ya bayyana gareku daga duhun dare, sannan ku cika azumin zuwa dare” (Albaqara : 187).

Ci da sha da gangan yana ba ta azumi
Shan Azumi Saboda Aiki

Ba ya halatta ga wanda yake aiki a gaban wuta, ko wani aiki mai wahala ya sha azumi, saboda daidai yake da kowa, shi ma an wajabta masa ya yi azumi.

Ba ya halatta ga wanda yake aiki a gaban wuta, ko wani aiki mai wahala ya sha azumi, saboda daidai yake da kowa, shi ma an wajabta masa ya yi azumi.

- Faxakarwa :

- Wanda ya manta ya ci ko ya sha azuminsa na nan, bai karye ba, sai dai ya wajaba a kansa ya kame (ya daina cin ko shan) lokacin da ya tuna. Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Wanda ya manta yana azumi ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa, Allah ne ya ciyar da shi ya shayar da shi” [Muslim ne ya rawaito shi]

- Azumi yana vaci da duk abin da ya isa cikin ciki, ta hanyar baki ko hanci, daga cikin abubuwan da suke xaukar ma’anar abinci ko abin sha, kamar allurar abinci.

Amma allurar da ba ta abinci ba ce, kamar allurar (Penicillin) da makamancinta, azumi ba ya vaci da ita, saboda ba ci ba ne, ba sha ba ne, ba kuma madadinsu ba ne.

Allurar (Penicillin) ba ta karya azumi
Maganin da yake kamar abinci yana karya azumi
Allurar lbinci ana karya azumi

- Abin da ya shiga ciki ta hanyar baki saboda wata buqata, kamar inhaler da sauransu ba ya vata azumi.

Inhaler (maganin Asma) ba ta karya azumi

- Kwalli da maganin ciwon ido da kunne da makamantansu ba sa karya azumi, saboda ba wani dalili da yake nuna vacin azumi da su.

Sannan kuma ido ba hanyar shigar abinci ba ce wanda aka saba da ita, haka ma maganin xigawa a kunne da hanci. Sai dai abin da ya fi a kiyaye wajen amafani da shi [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Kwalli ba ya karya azumi

- saboda Manzon Allah ya hana tsanantawa wajen shaqa ruwa ga mai azumi. Sannan kuma kafa ce ta kai abu zuwa ciki.

Idan mai azumi ya ci abin da ba abinci ba, ko kuma ya ci wani abin da yake cutarwa, kamar taba, to wannan azuminsa ya vaci, saboda ya ci abin ko ya sha ta hanyar da aka saba, ita ce baki, kuma wannan abin yana matsayin ci da sha.

Shan taba yana karya azumi

Azumi ba ya vaci da abin da yake da wahalar kauce masa ba, kamar qurar kan hanya, da abin da yake maqalewa na abinci a jikin haqora.

Sauran abincin da ya maqale a haqori ba ya karya azumi

2 – Saduwar Mace Da Namiji

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki: “An halatta muku saduwa da matanku a cikin daren azumi” (Albaqara : 187)

don haka duk wanda ya sadu da mace yana azumi, to azuminsa ya vaci, zai rama azumin wannan ranar, kuma akwai kaffara mai tsanani a kansa, ita ce ‘yanta baiwa, idan bai samu ba, sai ya yi azumin wata biyu a jere, idan ba zai iya ba, sai ya ciyar da miskinai sittin,

saboda hadisin da ya tabbata daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Na halaka”. Sai Manzon Allah ya ce masa “Me ye ya faru?” Sai ya ce, “Na aukwa wa matata a cikin watan Ramadan”. Sai Manzon Allah ya ce masa, “Za ka iya ‘yanta baiwa?” Sai ya ce, “A’a”. Sai ya ce masa, “Za ka iya azumi wata biyu a jere?” Sai ya ce, “A’a” sai ya ce masa “To za ka iya ciyar da miskinai sittin?” Sai ya ce, “A’a”. Sai Manzon Allah ya ce masa, “To zauna”. Sai ya zauna, sai aka kawo wa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) kwandon dabino, ya karva ya cewa wannan mutumin, “karvi wannan ka yi sadaka da shi”. Sai mutumin ya ce, “In bai wa wanda ya fi mu talauci!? Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi dariya har haqoransa suka bayyana, ya ce, “Ciyar da iyalanka da shi” [Bukhai da Muslim ne suka rawaito shi].

Ana jeranta matakan kafffara kamar yadda ta zo, mutum ba zai ciyar ba, har sai idan ba zai iya azumi ba, ba kuma zai yi azumi ba, sai in ba zai iya ‘yanta bawa ba”.

Kaffara tana wajaba a kan matar da mijinta ya sadu da ita da azumi idan da yardarta aka yi. Amma idan mijin nata ne ya tilasta ta, to azuminta ya karye, za ta ramuwa, amma ba za ta yi kaffara ba.



Tags: