Rukunai Da Wajibai Da Sunnonin Umara

3214

Rukunan Umara

1 – Harama

saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “ Dukkan ayyuka basa karvuwa sai da niyya, kuma kowane mutum yana da sakamakon abin da ya yi niyya” [Bukhari ne ya rawaito shi]

2 – Sa'ayi Tsakanin Safa Da Marwa,

saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku yi sa’ayi, haqiqa Allah ya wajabta muku sa’ayi” [Ahmad ne ya rawaito shi]

3 – Xawafi,

saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “ Su yi xawafi ga xaki daxaxxe”. (Al-hajj : 29).

Xawafi
Sa'ayi Tsakanin Safa Da Marwa
Tufafin Ihrami

Wajiban Umara

1 – Sanya Ihrami daga miqati,

saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) bayan ya faxi wuraren miqati ya ce, “Waxannan miqatan na mutane garin ne, da waxanda suka zo da hanyarsu, ga wanda yake da niyyar hajji da umara” [Bukhari ne ya rawaito shi]

2 – Aske kai gabaxaya ko saisaye,

saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Tabbas zaku shiga masallacin harami – in sha Allahu – kuna masu aske kanku gabaxaya ko kuna masu saisaye” (Al-fathu : 27).

Sunnonin Umara

Duk abin da ba rukuni ko wajibi ba, to sunna ne, kamar abubuwan da za su zo :

1 – Yin wanka yayin sanya ihrami

2 – Yin ihrami da kwarjalle da mayafi farare.

3 – Yin talbiyya da xaga murya da ita.

4 – Yaye kafaxar dama a wajen xawafi, shi ne sanya mayafi qarqashin hammatar hannun dama.

- Faxakarwa:

1 – Wanda ya bar rukuni daga cikin rukunan umara, umararsa ba ta yi ba, har sai ya zo da shi.

2 – wanda ya bar wajibi daga cikin wajiban umara, to wajibi ne a kansa ya yi yanka, (wato ya yanka akuya, ko ya ba da xaya bisa bakwai na saniya ko raqumi)

3 – Wanda ya bar sunna daga cikin sunnonin umara babu komai a kansa, umararsa ta inganta.

Ihrami (Harama)
Aski Ko Saisaye


Tags: