Masu Cin Zakka Da Fitar Da Zakka

24045

Waxanda Ake Ba Zakka

Masu cin zakka su ne waxanda suka cancance ta, su ne rukunai guda takwas da Allah ya iyakance su a cikin faxinsa : “Kaxai sadaka ta faqirai ce da miskinai da masu aiki a kanta, da waxanda ake jan zukatansu, da bayi, da waxanda ake bi bashi, da tafarkin Allah, da matafiya, rabo ne na dole daga Allah, Allah Masani ne mai hikima” (Attauba : 60)

1 - Talakawa (Faqirai)

Faqirai

Lafazin "Fuqara'u" jam'i ne na "Faqiri" Shi ne wanda bai da abin da zai biya masa buqatarsa, da buqatar iyalansa, ta abinci abin sha, tufafi, wurin zama.

Za a ba shi abin da zai ishe da iyalansa tsawon shekara xaya daga zakka

2 - Miskinai

Miskinai

Lafazin "Masakin" jam'i ne na "Miskin" shi ne wanda ya mallaki rabin abin da zai ishe shi, ko fiye da rabi, kamar wanda yake da xari, alhali yana buqatar xari biyu, to sai a bashi abin da zai ishe shi da iyalansa tsawon shekara guda.

3 - Masu aiki a kan Dukiyar Zakkar

Masu Aiki A Kanta

Su ne waxanda suke tattara zakka, waxanda shugaba ya naxa, kuma suke raba ta ga mabuqata.

Ba da Zakka Ga Masu Aiki A Kanta

Wanda yake aikin tattara zakka da wanda ake bi bashi a basu zakka koda kuwa masu wadata ne, hakanan a ba wanda yake da qarfi mai nema idan ya zama ya shagalta da neman ilimin addini, kuma bai da kuxi, saboda neman ilimi jihadi ne a kan tafarkin Allah. Haka ma za a iya bawa mai jihadi da waxanda za a jawo zukatansu ga musulunci.

Amma idan wanda zai iya nema ya bar aiki ya shagalta da nafilfili to ba za a bashi zakka ba, saboda amfanin ibada ya tsaya a akan mai yin ta, savanin ilimi.

4 - Waxanda Ake Jan Zukatansu Zuwa Musulunci

Waxanda Ake Jan Zukatansu Zuwa Musulunci

Su ne shugabannin mutanensu, waxanda ake wa biyayya, kuma a ke sa ran musuluntar su idan an ba su zakka, ko kuma a samu kamewarsu daga sharri ga musulmi, ko kuma a qara musu qarfin imani, ko su kare wa musulmi wasu maqiyansu.

Za a ba su abin da zai jawo zukatansu daidai gwargwado daga zakka.

5 - Bayi

Bayi

Bawa da wanda aka rubuta masa fansa

Saboda kowanne daga cikinsu ya zama xa, mai ikon tasarrufi, ya zama mutum mai amfani a cikin al’ummarsa, ya kuma samu damar bautawa Allah kamar yadda ya dace. Waxanda aka kama musulmi a wajen yaqi suma suna shiga qarqashin bayi, za a iya fansarsu da kuxin zakka

6 - Waxanda ake Bi Bashi

Waxanda Ake Bi Bashi

Lafazin "Gaarimun" Jam'i ne na "Gaarim" shi ne wanda ake bi bashi

Waxanda ake bashi kala biyu ne:

Na Farko : wanda ake bi bashi, saboda wata buqatarsa ta kansa da ya yi, sai a bashi a abin da zai biya bashinsa daga zakka indai talaka ne.

Na biyu : Wanda ake bi bashi saboda wani sulhu da ya yi tsakanin musulmi, sai a bashi abin da zai biya bashinsa daga zakka, ko da kuwa mai wadata ne.

7 - A kan Tafarkin Allah (Fi sabilillihi)

Saboda Allah (Fisabilillahi)

Su ne waxanda suke jihadi saboda Allah

Za a ba su abin da zai ishe su don yin jihadi saboda Allah. Sauran ayyukan da’awa waxanda suke cikin jihadi za su shiga cikin wannan vangare, idan ba su samu abin da za su yi aikin da shi daga sadaka.

8 - Matafiyi

Matafiyi

Shi ne matafiyin da guzuri ya yanke masa a tafiya, ba shi da wani kuxi.

Za a ba shi abin da zai kai shi garinsu daga zakka, koda kuwa mawadaci a garinsu.

Faxakarwa :

1 – Waxanda ba a waxanann rukunai takwas xin ba ba a ba su zakka, ko da kuwa cikin ayyukan alheri ne, kamar gina masallaci, makarantu, asibitoci, da sauransu na ayyukan alheri, waxanda za a iya yin su da sadaka.

2 – Ba sharaxi ba ne sai an bawa dukka takwas xin nan da aka ambata a yayin raba zakka, a'a ya wadatar idan aka ba kowane xaya daga cikin takwas xin.

Waxanda Ba A Basu Zakka

1 - Mawadata Da Masu Aiki Qarfafa

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Babu rabon madawaci ko mai aiki mai qarfi a cikinta” [Abu Dawud ne ya rawaito shi] wato zakka.

2 - Iyaye, 'Ya'ya, Mata, Da Waxanda Ciyarwarsu Da Wajaba A Kanka

Ba ya halatta a ba da zakka ga wanda ya wajaba mutum musulmi ya ciyar da su, kamar iyaye maza, da iyaye mata, kakanni maza, kakanni mata, ‘ya’ya, da ‘ya’yan ‘ya’ya maza (jikoki).

Saboda ba waxannan zakka zai wadatar da shi daga ciyarwar da ta wajaba a kanshi, ya sarayar da ita daga kanshi, sai amfanin zakka ya koma gare shi.

3 - Kafiran Da Ba Waxanda Ake Jan Zukatansu Ba Ne Zuwa Musulunci

Ba ya halatta a ba kafiri zakka matuqar dai ba jan zuciyarsa za a yi zuwa musulunci ba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Za a karvi zakka daga mawadatansu, a mayar da ita ga talakawansu” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Ana nufin madawatan musulmi da talakawansu, ba waxanda ba su ba, saboda yana cikin maqasudin zakka wadatar da talakawan musulmi, da qarfafa son juna tsakaninsu, hakan kuwa ba ya halatta ga kafirai.

4 - Iyalan Gidan Annabi (صلى الله عيه وسلم)

Zakka ba ta halatta ga iyalan gidan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) don girmamasu da basu daraja, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Waxannan sadakoki xin qazantar mutane ce, ba ta halatta ga Muhammad, ko iyalan gidan Muhammad [Iyalan Annabi su ne Banu Hashim]” [Muslim ne ya rawaito shi].

5 - Bararrun Bayin Iyalan Annabi (صلى الله عيه وسلم)

Su ne bayin da iyalan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) suka ‘yanta su, saboda hadisin da yake cewa :“Sadaka ba ta halatta garemu, kuma bararrun bayin mutane suna cikinsu” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Wato hukuncinsa irin hukuncinsu ne, don haka zakka ta haramta a kan bararrun bayin Bani Hashim.

6 - Bawan Da Aka Mallaka

Ba a ba da zakka ga bawa, saboda dukiyar bawa ta mai gidansa ce, idan aka ba shi zakka sai ta zama mallakin mai gidansa, saboda ciyarwarsa tana kan mai gidansa.

Amma an cire bawan da aka rubuta masa fansa daga wannan hukunci, shi za a iya ba shi zakkar da zai biya fansar da aka rubuta masa, haka ma wanda yake aiki a kan zakkar shi ma za a iya ba shi, don haka idan bawa yana aiki a kan zakka, za a iya ba shi, saboda ya zama kamar xan qodago, kuma ya halatta bawa ya yi qodago idan wanda ya mallake shi ya yi masa izini.

Fitar Da Zakka

Lokacin Fitar Da Zakka

Wajibi ne a fitar da zakka da zarar lokacinta ya yi, indai akwai iko, ba ya halatta a jinkirta ta sai da lalura, kamar ya zama dukiyar tana wani gari mai nisa daga inda mai ita yake, ko kuma ya zamana mai dukiyar an tsare shi, ko makamancin haka.

Dalilin wajabcin fitar da ita da wuri shi ne faxin Allah Maxaukakin Sarki, “Ku bayar da haqqinsa ranar girbinsa” (Al-an’am : 141)

da faxinsa “Ku bayar da zakka” (Annur : 56) umarni kuwa yana hukunta yin gaggawar abin da aka umarta.

Hukuncin Gaggauta Fitar Da Zakka

Ya halatta a gaggauta fitar da zakka yayin buqatar musulmi.

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aika umar karvo zakka, sai ya dawo ya kawo qarar Abbas, ya ce, “ya hana ni zakkarsa” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce “Ya umar, haqiqa Abbas mun karvi bashin zakkarsa ta shekara biyu a shekara xaya” [DaraQuxni ne ya rawaito shi]

Wurin Da Ake Fitar Da Zakka

Abin da ya fi shi ne a fitar da zakka a cikin mutanen da dukiyar take cikinsu, sai dai ya halatta a xauki zakka daga wani gari zuwa wani gari na kusa ko na nesa don wata buqata

kamar a ce garin da yake nesa xin ya fi talauci, ko kuma mai zakkar ya zama yana da ‘yan uwa talakawa a wancan garin mai nisa, saboda a cikin baiwa ‘yan uwansa akwai maslaha ta zakka da sada zumunci.

Wanda Ya Cancanta A Ba Zakka
Ya kamata wanda zai fitar da zakka ya yi qoqarin neman wanda ya fi dace wa aba shi, wanda ya fi buqata. A duk lokacin da abubuwan da suke sa a ba mutum zakka suka yi yawa a akan wani mutum, to shi ya fi cancanta fiye da wanda ba shi ba, kamar a ce talaka ne xan uwa, ko talaka ne xalibin ilimi, da sauransu.

Wasu Bayanai Masu Mahimmanci Kan Zakka

Ba da Qima A Zakka

Asali dai shi ne fitar da zakka daga cikin abin da aka wajabta, sai dai saboda wata buqata ko maslaha ya halatta a ba da qimar zakkar.

Alaqar Qasa Da Zakka

Asali dai shi ne zakkar kuxi Gwamnati ce zata kula da ita, ba za bar masu bayar da zakkar ba su yi yadda suka ga dama, idan gwamnati ta yi rauni wajen xaukan wannan nauyi, to sai ya zama a kan wuyan dukka musulmi.

Yin Kasuwanci Da Kuxin Zakka Don Maslahar Masu Cin Zakkar

Ya hallata a saka jari da kuxin zakka cikin ayyukan da zasu amfani waxanda suka cancanci karvar zakka. Idan dai babu dalilin da zai sa a gaggauta raba ta.

Shin Akwai Wani Haqqi A Cikin Dukiya Banda Zakka, Kamar Haraji?

Zakka ita ce haqqin da yake jujjuyawa a cikin dukiya, wanda kuma ya wajaba dole a kan waxanda suke da hali.

- A cikin dukiya akwai wasu haqqoqi waxanda suke bijirowa ba zakka ba, kuma ba su da wani adadi da aka iyakance su da shi, sannan ba tabbatattu ba ne kamar zakka, waxannan haqqoqi suna wajaba idan wani abu ya bijiro, daga cikinsu akwai ciyar da iyaye, 'yan uwa makusanta, mata, da kawar da bala'in da asusun gwamnati ba zai iya xaukan nauyin kawar da shi ba.

- Haraji ba ya zama a madadin zakka, saboda zakka ibada ce daga cikin ibadoji, amma haraji wani abu ne na zamani, don haka wannan ba ya wadatarwa ga barin wannan.



Tags: