Liman Da Koyi Da Liman

13262

Wanda Yafi Cancanta Da Yin Limanci

A jere su ne :

Na farko : Wanda ya fi karatun Alqur’ani, wato wanda ya fi yawan haddace shi, kuma yafi sauran fahimtar hukunce-hukuncensa.

Na biyu : Wanda ya fi sanin Sunnah, wato wanda yasan ma’anoninta da hukunce-hukuncenta.

Na uku : Wanda ya daxe da yin hijira, daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Idan ba hijira a lokacin sai a gabatar a kan wanda ya riga tuba da qaurace wa savo.

Na huxu : Idan su yi daidai a duk abin da ya gabata, to sai a sa wanda ya fi yawan shekaru.

Dalili akan abin da ya gabata hadisin Abu Mas’ud Al-ansari – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya fi mutane karatun Alqur’ani shi zai limance su, idan sun yi daidai a karatu, to wanda ya fi su sanin sunnah, in sun yi daidai a sanin sunnah, to wanda ya fi daxe wa da hijira, idan sun yi daidai a hijira to wanda ya daxe da musulunta” [Muslim ne ya rawaito shi].

Ana kula da wannan jerin yayin naxa limamin masallaci, ko in a cikin jama’a ne waxanda babu lmami ratibi a cikinsu, in akwai limami a ratibi a cikinsu, ko kuma wanda ake gidansa yana nan, ko kuma wanda yake jagora to shi za a gabatar da wanda ba shi ba [Kamar a ce sarki ne ko shugaban wurin da makamancinsa] ,

saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada wani mutum ya yi wa wani mutum limanci a wurin ikonsa, kada ya zauna a wurin zamansa a gidansa [Wurin zamansa, shi ne wurin da aka tanadarwa baqo don ya zauna], sai dai da izininsa” [Muslim ne ya rawaito shi].

Wurin Tsayuwar Liman Da Mamu

1 – Idan Mamun guda xaya ne, to sunnah ita ce ya tsaya a damar liman, yana saiti da shi, saboda hadisin Xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Na yi sallah tare da Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a wani dare, sai na tsaya a hagunsa, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kama kaina ta bayansa, ya sanya ni a damarsa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Idan mutane biyu ne ko fiye da haka, sai liman ya tsaya a tsakiyarsu saboda hadisin Jabir da Jabbar – Allah ya yarda da su – xayansu ya tsaya a daman Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) xayan kuma a hagun xin sa.

Sai Jabir ya ce, “Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kama hannayensu, ya turamu baya, har sai da ya maida mu bayansa” [Muslim ne ya rawaito shi].

Wurin Tsayuwar Mata

1 – Idan mata za su yi sallar jam’i, to a sunnah limamiyarsu zata tsaya a tsakiyarsu ne, ba za ta shiga gabansu ba.

2 – Mace zata tsaya bayan namiji idan ya limance ta. Hakanan idan za ta yi sallah da maza zata tsaya a bayan sahu ne.

3 – Idan mata za su yi sallar jam’i tare da maza, to a sunnah za su yi baya da maza, su yi sahu irin na maza.

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mafi alherin sahun mata na qarshe, mafi sharrinsa na farkonsa” [Ibnu Majah ne ya rawaitoshi].

Sallar Mata
Mace A Kusa Da Maza

Daga Hukunce-Hukuncen Koyi Da Liman

1 – Bai inganta ba bin liman daga cikin gida ta hanyar lasifika, hakanan ko ta sauraronsa a Radio.

2 – Bin liman daga waje ya inganta idan sahu ya haxu da juna.

3 – Ya inganta Mamu su bi liman a saman masallaci, ko kuma a qasan inda liman yake, idan suna jin muryarsa.

4 – Ya inganta mai farillah ya yi koyi da mai nafila, ko mai nafila ya yi koyi da mai farillah, kamar yin sallar isha a bayan wanda yake sallar asham, ko taya wanda sallar farillah ta wuce masa don ya samu ladan jam’i.

An karvo daga Jabir xan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mu’azu xan Jabal ya kasance yana sallah tare Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) , sannan sai ya je wajen mutanensa ya yi musu sallah (limanci)” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Riga Liman

Riga Liman

1 – Abin da aka shar’antawa mamu shi ne ya bi liman, wato ya aikata abin da liman ya yi bayansa kai-tsaye, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Kaxai an sanya liman ne don a yi koyi da shi, idan ya yi kabbara, kuma ku yi kabbara, idan ya yi ruku’u, kuma ku yi ruku’u, idan ya yi sujjada, kuma ku yi sujjada” [Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi].

2 – Riga liman (yin abu) haramun ne, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya tsananta akan haka, ya ce, “Yanzu xayanku baya tsoro idan ya xaga kansa kafin liman (ya xago) Allah ya mayar da kansa, kan jaki, ko kuma ya mayar da kamarsa kamar jaki” [Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi].

3 – Wanda ya riga liman (yin wani abu) da mantuwa, to ya wajaba a kansa ya koma ya yi koyi da shi.

Sallah Bayan Mai Kari
Sallah bayan wanda yake da kari bata inganta [Mai kari shi ne wanda ba shi da tsarki], sai dai in bai san da karin ba sai bayan da ya gama sallah, to a wannan yanayin sallar mamu ta inganta, liman kuma wajibi ne ya rama.


Tags: