Layya

8749

Bayanin Meye Layya

Layya

Ita ce abin da ake yanka wa na dabbobin ni'ima a ranakun salla, don neman kusanci ga Allah Maxaukakin Sarki

Hukuncin Layya

Sunna ce mai qarfi, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ka yi sallah ga Ubangijinka ka soke dabbarka” (Al-kausar : 2).

Haka saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi layya da raguna [Ragon da yake da baqi da fari, amma farin ya fi yawa] guda biyu, masu baqi da fari, masu qaho, ya yanka su da hannunsa, ya yi bismillah, ya yi kabbara, ya xora qafarsa akan wuyansu” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

Lokacin Yanka Layya

Lokacin yankan yana farawa daga bayan sallar idi, ranar sallah, zuwa faxuwar ranar qarshen kwanakin ‹yanyane, (su ne kwana na 11, da 12, 13, daga watan zul-hijja).

Dabbobin Da Suke Wadatar Wa A Layya

1 – Akuya ko tunkiya tana wadatar wa mutum xaya, kuma zai iya sa wanda yake so a cikin ladan, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yayin da ya yi niyyar yanka abin layyarsa ya ce, “Bismillahi, Allahumma Taqabbal Min Muhammad, wa Ali Muhammad, Wa min ummati Muhammad” (Ma’ana : Da sunan Allah, ya Allah ka karva daga Muhammad, da iyalan Muhammad, kuma daga al’ummar Muhammad” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

2 – Raqumi ko Sa guda xaya yana isar wa mutane bakwai. Ya halatta mutum bakwai su yi tarayya a kan raqumi xaya ko saniya xaya, saboda faxin Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarce mu, mu yi tarayya akan raqumi da saniya Kowane mutum bakwai daga cikinmu akan raqumi xaya” . [ Muslim ne ya rawaito shi]

Shekarun Dabbobin Da Suka Isa Layya

-Tirtirna daga Rago ko tunkiya, shi ne wanda ya cika wata shida

-Xan Akuya ko akuya wanda ya cika shekara xaya

-Sa ko saniya wanda suka cika shekara biyu

-Raqumi ko taguwa wanda suka cika shekara biyar.

Aibin Dabbobin Layya

1 – Aibin da yake hana a yi layya da dabba

-Mai ido xaya : wadda idon xaya yake da aibi, wadda ba ta gani ta shiga.’

-Gurguwa wadda bata iya tafiya.

-Ramammiya, ita ce wadda bata da kitse.

-Mara lafiyar da rashin lafiyarta ta bayyana.

-Dalilin haka shi ne hadisin Bara’u xan Azib – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Layya bata halatta da dabba mai ido xaya, wadda rashin idon xayan ya bayyana, da gurguwar da xingishinta ya bayyana, da maras lafiya wadda rashin lafiyar ya bayyana, da ramammiya wadda bata da mai” Wannan hukunci ya haxa da duk wani aibi irin wannan ko wanda ya fi shi” [Muslim ne ya rawaito shi]

Ramammiya
Mai Ido Xaya
Gurguwa

2 – Aibin Da Baya Hana Layya

- Dabbar da bata da jela

- Dabbar da bata da qaho

- Dabbar da aka fixiye

- Dabbar da take da tsaga a kunne ko qahonta ya karye

Wadda Qahon Ya Karye
Maras Qaho
Maras Jela
Faxakarwa :
Duk abin da aka ambata dangane da layya, na abin da yake isar wa da wanda baya isar wa, haka abin yake a wajen hadaya da fansa.

Raba Naman Layya

An shar’anta wa mai layya ya ci kashi xaya bisa uku na layyarsa, ya yi kyauta da kashi xaya, ya yi sadaka da kashi xayan, ya halatta ya yi sadaka da layyar gabaxaya, in kuma ya ci mafi yawanta to ya halatta, babu komai

-Faxakarwa :

1 – Ya kamata mai layya da hadaya ya yi qoqarin amfanuwa da naman kada ya watsar da shi a banza, kamar yadda wasu alhazai suke yi, sukan yanka hadayar su barta a wurin yankan ba tare da fixa ba ko yanyankawa ba, ba wanda zai amfanu da shi.

2 – Wanda duk ya yi niyyar layya to kada ya rage gashin kansa, kada yanke farcensa ko fatarsa, idan watan zul-hajji ya shigo, har sai ya yanka layyarsa, saboda hadisin Ummu Salamata – Allah ya yarda da ita – ta ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “idan goman farko ta watan zulhajji ta shigo, kuma xayanku ya yi niyyar yin layya, to kada ya tava komai daga jikin gashinsa ko fatarsa” [Muslim ne ya rawaito shi]

Amma wanda yi masa layya za a yi, kamar iyalai, ‘ya’ya, to waxannan ba a haramta musu rage komai ba.



Tags: