Lalurorin Da Suke Sa Asha Azumi A Ramadan

5947

Lalurorin Da Suke Sa Asha Azumi A Ramadan

1 – Rashin Lafiya

An halattawa marar lafiya ya sha azumi, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Wanda ya zama ba ya da lafiya a cikinku, ko kuma yake kan tafiya, to ya rama wasu kwanakin daban” (Al-baqara : 184).

- Rashin lafiyar da aka yi rangwame a sha azumi saboda ita, ita ce rashin lafiyar da mai azumi zai yi wahala da ita, ko kuma zai cutu da ita.

- Shan Ruwan Marar Lafiya :

Idan marar lafiya ya sha azumi, kuma rashin lafiyarsa ta zama ana sa ran ya warke, to wannan zai rama kwanakin da ya sha, a duk lokacin da ya warke, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Wanda ya zama ba ya da lafiya a cikinku, ko kuma yake kan tafiya, to ya rama a wasu kwanakin daban” (Al-baqara : 184).

Idan rashin lafiyar ya zama ba wanda ake san ran warke wa ba ne, ko rashin lafiya ne na dindindin, ko kuma tsoho ne wanda ba ya iya azumi a koyaushe, to zai ciyar da miskini rabin sa’i a kullum [Sa’i xaya shi ne, gwargwadon tafi huxu na mutum matsaikaci], na shinkafa ko kuma makamancinta daga abin da ake ci a garin.

2 – Tafiya

An halattawa matafiyi ya sha ruwa a Ramadan, amma wajibi ne a kansa ya rama, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Wanda ya zama ba ya shi da lafiya a cikinku, ko kuma yake kan tafiya, to ya rama a wasu kwanakin daban” (Al-baqara : 184).

Tafiyar da ta halatta a sha azumi saboda ita, ita ce wadda ake yin qasaru a cikinta, wadda a alada ake ce mata tafiya, sannan ta zama tafiya ce ta halal. Idan tafiyar savo ce, ko kuma tafiyar da za a yi don kawai a sha azumi, to ba ya halatta a sha azumi a wannan tafiya.

Idan matafiyi ya yi azumi, azuminsa ya yi, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna tafiya tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ). Mai azumi a cikinmu bai aibata wanda ba ya azumi, hakanan wanda ba ya azumi bai aibata wanda yake azumi” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Sai dai da sharaxin kada azumin ya yi masa wahala, idan ya yi masa wahala, ko kuma ya cutu da shi, to ya ajiye azumin shi ya fi.

Saboda Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ga wani mutum a tafiya yana azumi, an masa rumfa saboda tsananin zafin rana, mutane sun kewaye shi, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ba ya cikin aikin alheri yin azumi a halin tafiya” [Bukhari ne ya rawaito shi].

3 - Ciki Da Shayarwa

Mai ciki ko mai shayarwa idan suka ji tsoron cutuwa idan suka yi azumi, to sai su sha azumin, su rama kamar yadda marar lafiya yake ramawa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Haqiqa Allah Maxaukakin Sarki ya sauke wa matafiyi azumi, da rabin sallah, haka ma an sauke wa mai ciki da mai shayarwa azumi” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Idan kuwa mai shayarwa ta ji tsoron cutuwar xanta, sai ta sha ta rama, ta kuma ciyar da miskini a kullum, saboda faxin Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – “Mai shayarwa da mai ciki idan suka ji tsoron cutuwar ‘ya’yansu, su sha azumi, su ciyar” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

4 – Haila Da Jinin Biqi

Wajibi ne macen da jinin haila ko biqi ya zo mata ta ajiye azumi, haramun ne a kanta ta yi azumin, in kuma ta yi bai inganta ba, sai ta rama, saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – an tambaye ta dangane da rama azumi da mai haila take yi,

amma ba ta rama sallah, sai Nana Aishatu ta ce, “Hakan yana samun mu, sai a umarce mu da rama azumi, amma ba a umartarmu da rama sallah” [Bukhari da Muslim suka rawaito shi].



Tags: