Kwanuka

3582

Bayanin Kwanuka

Kwanuka

Abubuwan da ake ajiye ruwa ko wani abu a cikinsu

Amfani da kwanon zinare da na Azurfa

1-Amfani Da Kwanon Zinare Da Azurfa Wajen Ci Da Sha

Haramun ne a yi amfani da su, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) : “Kada ku sha da kwanon zinare da azurfa, kada ku ci a cikinsu, saboda ta su ce (kafirai) a duniya, a lahira kuma tamu ce” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Da faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Wanda yake shan wani abu a cikin kwanon azurfa to yana kwankwaxar wutar Jahannama ne a cikinsa” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Sha da kwanon Azurfa
Ci a cikin kwanon zinare

2-Amfani Da Kwanon Zinare Da Azurfa Ba A Wajen Ci Ko Sha Ba

An halatta a yi amfani da su ba a wajen ci ko sha ba, kamar yin alwala da sauransu, saboda hadisin da ya gabata ya taqaita hanin a kan ci da sha, kuma ya tabbata cewa “ Ummu Salama Allah ya yarda ita tana da wani [ Wani xan qaramin kwano ne kamar qararrawa] asusu na azurfa, a cikinsa akwai gashin kan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ” [ Bukhari ne ya ruwaito shi].

Butar azurfa saboda yin alwala

Amfani Da Kwanon Da Aka Liqe Shi Da Azurfa

Ya halatta a yi amfani da kwanon da aka liqe shi da ‘yar azurfa kaxan don wata buqata, saboda abin da ya tabbata cewa “akushin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fashe, sai a ka sanya wata sarqa ta azurfa a wurin da ya fashe xin” [ Bukhari ne ya rawaito shi].

Amfani da kwanon da aka liqe da azurfa


Tags: