Ihrami

5764

Bayanin Mene ne Ihrami

Ma'anar Ihrami A Larabci

Shi ne : Hanawa ko Kariya

Ma'anar Ihrami A Shari'a

Shi ne niyyar shiga aikin hajji, tare da wani abu na ayyukan hajji

Abubuwan Da Ake So Mai Ihrami Ya Yi

1 – Wanka

An karvo daga Kharijah xan Zaid, daga babansa, ya ce, “shi ya ga Annabi (SAW) ya cire kayansa ya yi wanka saboda ihrami” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

2 – Tsaftace Jiki

Ta hanyar cire gashin hammata da mara, da yanke gashin baki da farce

3 – Turare

Saboda hadisin Aisha – Allah ya yarda da shi – “Na kasance ina sa wa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) turare, saboda zai sanya ihraminsa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Amma kada ya sanya wa kayansa turare, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada ku sanya kayan da turaren Za'afaranu ya shafe su, ko kuma turaren wars”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Turare

4 – Namiji Zai Tuve Xinkakken Kayan Dake Jikinsa, Kafin Ya Sa Ihrami, Ya Sanya Zaninsa Da Mayafinsa Farare Da Takalmansa

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Xayanku ya yi Ihrami da zani da mayafi da takalma faxe, idan bai samu faxe ba, to ya sanya huffi, amma ya yanke su zuwa idon qafa” [Ahmad ne ya rawaito shi]

Mace kuwa zata yi ihrami da tufafin da ta ga dama, babu wata kala da aka ayyana, sai dai ta nisanci yin kama da maza, da kayan da suke ado ne, kada kuma ta sanya abin rufe fuska (niqabi) [Shi ne abin da mace take sawa don rufe hannayenta] kada ta sanya safar hannu .

Kwarjalle Da Mayafi na Mai Ihrami
Takalmin Mai Ihrami
Safar Mace mai ihrami
Niqabin Mace Mai ihrami

Abubuwan Da Aka Hana Mai Ihrami Ya Yi

1 – Rufe kai da wani abin da zai mannu da kan

Saboda hadisin xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, wani mutum ya cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) «Waxanne tufafi ne mai ihrami zai sanya?» sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Kada ku sanya riguna, ko rawani, ko wanduna, ko kuma rigunan da suke haxe da hula” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce dangane da mai ihramin nan da ya mutu, ya ce, “kada ku rufe kansa, saboda za a tashe shi ranar alqiyama yana talbiyya” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Hular Mai Ihrami
Rawanin Mai Ihrami
Lemar Mai Ihrami
Sanya Wando Ga Mai Ihrami

2 – Sanya xinkakken Abu ga Maza

Abin da ake nufi da xinkakke shi ne duk abin da aka xinka shi don sa wa a wata gava ko a jiki, kamar riga, wanduna, huffi, safa, safar hannu da makamantansu, saboda hadisin Xan Umar da ya gabata : “ Kada ku sanya riguna, ko rawuna, ko wanduna, ko kuma rigunan da suke haxe da hula, ko huffi”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Idan mai ihrami bai samu kwarjalle ba to zai iya sanya wando har zuwa lokacin da zai samu kwarjalle, haka nan idan ban samu takalma faxe ba, to ya sanya huffi, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “ Idan bai samu takalmi faxe ba, to ya sanya huffi, amma ya yanke su zuwa idon sau”[Ibnu Khuzaima ne ya rawaito shi]

Sanya Xinkakken Abu
Takalma Guda Biyu
Riga Mai Haxe Da Hula
Huffin Mai Ihrami

3 – Kashe dabbar tudu ko farautarta

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Kada ku kashe dabbar farauta alhali kuna cikin ihrami” (Al-ma’idah : 95).

Ma’ana kun yi haramar aikin hajji ko umara. Hakanan da faxin Allah Maxaukakin Sarki : “An haramta muku farautar dabbobin tudu matuqar kuna cikin ihrami”. (Al-ma’idah : 96)

abin da ake nufi dabbar da take jeji wadda ba a saba da ita ba, hakanan ma tsuntsaye.

Amma dabbobin da aka saba da su, waxannan ba farauta ba ne. Ya halatta mai ihrami ya yanka kamar irin su kaza, ko wata dabbar gida da makamantansu.

Dabbobin da suke cikin ruwa ma ya halatta mai ihrami ya yi farautarsu.

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “An halatta muku farautar dabbobin ruwa da mushensa (dabbar da mutu a cikin ruwa wadda take rayuwa a ciki” (Al-ma’idah : 96).

Amma dabbobin da aka haramta cin su kamar maciji, kunama, ya hallata a kashe su, kuma ya halatta mai ihrami ya kashe duk wata dabba da ta taso masa, idan ba zai iya ture ta ba sai da hakan.

Kunama
Maciji
Ya Halatta A Yanka Dabbar Gida
Tsuntsayen Da Ake Farauta
Su ya halatta ga mai ihrami

4 – Aski Ko Saisaye

Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Kada ku aske kawunanku har sai dabbar hadaya ta isa mahallinta”. (Al-baqara : 197).

Wannan hanin ya haxa dukkan jiki gabaxayansa, idan aka yi qiyasi da gashin kai.

Aski Ko Saisaye

5 – Yanke Farce

Farcen qafa ne ko na hannu.

Yanke Farcen Qafa
Yanke farcen Hannu

6 – Sanya Turare A Jiki Ko Kaya

An hana mai ihrami ya sanya turare a jikinsa ko tufafinsa bayan ya shiga ihrami, ko kuma ya shaqi turare, saboda hadisin xan Umar – Allah ya yarda da shi – wanda ya gabata, a cikinsa Manzon Allah ya ce, “Kada ku sanya kayan da turaren Za’afaranu ya shafe su, ko kuma turaren wars”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Da hadisin mutumin nan da ya mutu yana cikin ihrami, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Kada ku sanya masa turare”[Bukhari ne ya rawaito shi]

Sanya wa Jiki Turare
Sanya wa Riga Turare

7 – Xaura Aure

Saboda hadisin Usman – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mai ihrami baya aura, ba a aurar masa, baya neman aure”[Muslim ne ya rawaito shi].

8 – Saduwa Da Mace

Shi ne tarawa da mace, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Duk wanda ya shiga aikin hajji a cikinsu to babu saduwa da mata”. (Al-baqara : 197)

Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Ana nufin jima’i” kuma shi ne mafi tsananin abin da aka hana mai ihrami

9 – Rungumar Mace Ba Tare Da Saduwa ba

Kamar sumba da shafa, saboda hanya ce ta zuwa saduwa.

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mace Mai Ihrami

Mace a wajen abin da aka hana mai ihrami kamar namiji ce, sai dai ta bambanta da shi ne a abubuwa masu zuwa :

1 – Zata sanya xinkakken kaya.

2 – Zata rufe kanta.

3 – Ba za ta rufe fuskarta ba (Niqab), ba za ta sanya safa ba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Mace mai ihrami ba za ta rufe fuskarta ba, (niqab) ba za sanya safar hannu ba”[Bukhari ne ya rawaito shi]

Amma za ta rufe fuskarta a wajen mazajen da ba na ta ba, ta hanyar sakin mayafinta, ba niqabi zata sanya ba, kuma an halatta mata yin ado da zinare.

Faxakarwa

1 – Abin da ake kira raka’a biyu bayan Ihrami bai da asali, kamar yadda babu wata addu’a da aka ayyana yayin Ihrami.

2 – Idan mutum yana tafiya a jirgi, kuma ya ji tsoron ba zai samu damar sanya Ihrami ba idan ya isa miqati, to ya sanya ihramin daga gidansa ko filin jirgin sama, amma bai zama mai ihrami ba har sai ya yi niyyar aikin hajji kafin ya wuce miqati.

3 – Wasu alhazai suna yaye kafaxunsu da zarar sun sanya ihraminsu, abin da ake kira da larabci «Alix-xiba’i».

To yin hakan ba daidai ba ne, saboda ana yaye kafaxu a buxe a wurin xawafi kaxai, a sauran wurare kuwa sai alhaji ya rufe kafaxunsa.

Fito Da Kafaxa Waje Yayin Ihrami

Wasu Daga Hukunce-Hukuncen Ihrami :

Idan gashi ya faxi da kan mai ihrami saboda ya shafar kansa yayin alwala ko wanka, to wannan ba zai cutar da shi ba, haka nan idan gashin bakinsa ya cire ko na gemunsa ko farcensa, babu komai, matuqar ba da gangan ya cire shi ba.

Mace da namiji duk hukuncinsu xaya, saboda mace ma idan gashinta ko farcenta ya cire babu komai a kanta.

Ya halatta mai ihrami ya sanya maxauri a qafarsa idan yana buqatar hakan, ko kuma saboda wata maslaha.

-Sanya Sharaxi Yayin Niyya :

Wanda yake da rashin lafiya, ko ya ji tsoron faruwar wani abu da zai hana shi gama aikin hajjinsa, to an so ya yi sharaxi yayin sanya ihrami, ya ce, «Allah na amsa maka da umara ko hajji, amma idan wani abu ya tsare ni, to wurin cire ihrami na shi ne inda aka tsare ni».

An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah (SAW) ya shigo wajen Duba’a ‘yar Zubair, ya ce mata, “Ko zaki je aikin hajji ne?” sai ta ce, “Wallahi ina ji na bani da lafiya” sai Manzon Allah (SAW) ya ce mata, “Ki tafi hajji, ki sanya sharaxi, ki ce, “Ya Ubangiji wurin cire ihramina shi ne wurin da aka tsareni (Wato wurin rashin lafiya ta taso min) idan kin faxi haka, kuma wani abun da zai hana ki ya faru, to ya halatta ki fita da ihraminki, babu wani abu a kanki”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]



Tags: