Hukunce-Hukuncen Biyan Buqata

5536

Abin Da Ya Wajaba Yayin Biyan Buqata

1- Suturce alaura daga idon mutane yayin biyan buqata, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) : “Kariya tsakanin ganin aljannu da al’aurar ‘yan adam shi ne idan xayansu zai shiga banxaki ya ce, “Bismillahi” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

2- Kiyaye tufafinsa da jikinsa daga najasa, saboda abin da “ya tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya wuce ta wajen waxansu qabubura guda biyu, sai ya ce, “Haqiqa ana yi musu azaba, amma ba saboda wani abu mai wahala ba ne, shi dai wannan ya kasance ba ya kaffa-kaffa wajen fitsari” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

3- Yin tsarki da ruwa ko hoge, saboda hadisin Anas xan Malik- Allah ya yarda da shi- ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan zai tafi biyan buqata, ni da wani yaro sa’ana muna xaukar buta da sanda [ Sanda ana nufin xan qaramin mashi], sai Manzon Allah ya yi tsarki da ruwa (bayan ya gama)” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Abin Da Ya Haramta Yayin Biyan Buqata

1- Fuskantar alqibla, ko ba ta baya yayin biyan buqata a fili. Idan kuwa a cikin gini ne to abin da ya fi kada a fuskanceta, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“Idan kun zo wurin biyan buqatarku kada ku fuskanci alqibla kada kuma ku ba ta baya, ku kalli gabas ko yamma” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

2- Biyan buqata akan hanyar mutane, ko inuwarsu ko wurin da suke taruwa, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku ji tsoron wurin tsinuwa guda biyu”. Sai suka ce, “Menene masu jawo tsinuwa guda biyu?” sai ya ce, “Wanda yake biyan buqata akan hanyar mutane, ko inuwarsu” [ Muslim ne ya rawaito shi].

3- Shiga banxaki da Alqur’ani, saboda yin hakan wulaqanta littafin Allah Maxaukakin Sarki ne.

4- Yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudu, kamar ruwan tafki wanda ake yin wanka a cikinsa, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada xayanku yayi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudu[ Ruwan da ba ya gudu : Shi ne wanda yake ba ya motsawa zuwa ko’ina.], sannan ya yi wanka da shi” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Biyan buqata akan hanyar mutane

Abin da ake so yayin biyan buqata

1- Nisantar mutane yayin biyan buqata a sahara ko fili

2- Ya ce yayin da zai shiga banxaki : “Bismillah, Allahumma Inni A’uzu bika minal Khubthi walkhaba’ith” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

3- Gabatar da qafar hagu yayin shiga banxaki, da gabatar da qafar dama yayin fitowa

4- Ya ce yayin da zai fito : “Gufranaka” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Biyan buqata a fili cikin sahara
Shiga banxaki da qafar hagu
Fita daga banxaki da qafar dama
Fitsari a cikin ruwan da ba ya gudu
Ya tabbata cewa yin fitsari a ruwan da ba ya gudu yana haifar da cutar Kurkunu.

Abin da ba a so yayin biyan buqata

1- Yin magana yayin biyan buqata, ko magana da wasu sai dai in da wata buqata, saboda hadisin xan Umar - Allah ya yarda da shi- ya ce, wani mutum ya wuce ta wajen Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “yana bawali, sai ya yi masa sallama, Ammaa bai amsa masa ba” [Muslim ne ya rawaito shi].

2- Shiga banxaki da abin da yake akwai ambaton Allah a jikinsa, sai dai in ana jin tsoron sacewa, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “ya kasance idan zai shiga banxaki sai ya cire zobensa” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

3- Shafar gaba da hannun dama, ko yin tsarki da shi, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada xayanku ya riqe gabansa da hannun damansa idan yana fitsari, kada kuma ya shafi bayan gida da damansa” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

4- Yin fitsari a cikin ramuka, don kada wata dabbar ta cuce shi ko shi ya cuce ta.

Yin magana yayin biyan buqata
Shiga banxaki da abin da yake xauke da sunan Allah
Yin fitsari a cikin ramuka
Shiga banxaki da Alqur’ani
Yin fitsari a tsaye
Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya hana yin fitsari a tsaye, sai dai idan ya aminta cewa tartsatsin fitsarin ba zai vata shi ba, to ya halatta yayi, saboda hadisin Huzaifa – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya zo wajen bolar wasu mutane sai ya yi fitsari a tsaye” [ Bukhari ne ya rawaito shi] .

Tsarkin Ruwa Da Tsarkin Hoge

Tsarkin ruwa

Shi ne gusar da abin da yake fita daga gaba ko dubura da ruwa mai tsarki

Tsarkin hoge

Shi ne gusar da abin da yake fita daga gaba ko dubura da hoge ko makamancinsa

Hukuncin Tsarkin Ruwa Da Tsarkin Hoge

Ya halAn shar’anta yin tsarki da ruwa, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan zai je biyan buqatarsa, sai ni da wani yaro sa’ana mu xaukar masa ruwa da sanda, idan ya gama sai yayi tsarki da ruwa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

- atta a taqaita a kan tsarkin dutse kaxai, da sharaxi guda biyu:

1- Ya zama fitsarin ko bayan-gidan bai wuce wurin da ya saba fitowa daga cikinsa ba, idan kuwa ya wuce to lallai sai an yi amfani da ruwa.

2- Tsarkin hogen ya zama da hoge guda uku ko sama da haka, har gabansa ko duburarsa ta tsarkaka daga najasa.

Hikimar Yin Tsarkin Ruwa Da Na Hoge

1- Don samun tsarki da gusar da najasa

2- Saboda samun tsafta da nisanta daga abubuwan da suke kawo rashin lafiya

Fa'ida

Ba a yin tsarkin don an yi tusa

Yin tsarki da ruwa ya fi yi da dutse, saboda ruwa ya fi tsarkake wa da fitar da najasa.

Sharuxxan abin da ake tsarkin dutse da shi

A – Ya zama mai tsarki, ba ya inganta a yi da abu mai najasa.

B – Ya zama halataccen abu, ba ya inganta da haramtaccen abu.

C – Ya zama mai tsarkake wurin najasar.

D – Kada ya zama qashi ko kashin dabbobi, Salman Afarisi - Allah ya yarda da shi - ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya hana mu mu fuskanci alqibla da bayan-gida ko bawali, ko kuma mu yi tsarki da hannun dama, ko mu yi tsarki da duwatsun da ba su kai uku ba, ko mu yi tsarki da kashin dabbobi ko qashi” [Muslim ne ya rawaito shi].

E – Kada ya zama abu ne mai qima, kamar abinci, ko wata takardar da aka rubuta wani abu mai qima a cikinta.0

Daga cikin abin da ya halatta a yi tsarkin dutse da shi akwai : duwatsu masu tsarki, hankici, takarda mai tsarki, da qyalle mai tsarki

Yin tsarki da qashi
Yin tsarki da abinci
Yin tsarki da takarda mai qima
Yin tsarki da qyalle
Yin tsarki da Hankici
Yin tsarki da duwatsu
Tsarki da hannun dama
Ba ya halatta a yi tsarki da hannun dama, saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “ Kada xayanku ya riqe gabansa da hannun damansa idan yana fitsari, kada kuma ya shafi bayan gida da damansa” [Muslim ne ya rawaito shi] .


Tags: