Hukunce-hukuncen aikin hajji da umara

4921

Hajji

Bayanin Mene ne Hajji

Kalmar Hajji a larabci

Ita ce nufar wuri da fuskantarsa

Ma'anar Hajj a shari'ance

Nufatar Makkah a wani lokaci sannanne, don yin wasu ayyuka kevantattu.

Hukuncin Aikin Hajji Da Falalarsa

Hajji rukuni ne daga rukunan musulunci, Allah ya wajabta shi a kan bayinsa. Allah ya ce, “Allah ya wajabta wa mutane ziyartar xakinsa ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, duk wanda ya kafirce (ya qi) to Allah mawadaci ne daga talikai”. (Ali- Imran : 97).

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An gina Musulunci a bisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Muhammad Bawansa ne Manzonsa ne Tsaida sallah Bayar da zakkah Ziyartar xakin Allah Azumin watan Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi hajji, bai yi maganganun banza ba [Maganganun Banza], bai yi fasiqanci ba [Savon Allah] , an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Sharuxxan Hajji

1 – Musulunci

Hajji baya wajaba akan kafiri, kuma bai inganta daga gare shi ba.

2 – Hankali

Hajji baya wajaba akan mahaukaci, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “An xauke alqalami a kan mutum uku, daga mai barci har sai ya farka, daga yaro har sai ya yi mafarki, daga mahaukaci har sai ya yi hankali” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

3 – Balaga

Hajji baya wajaba akan yaro qarami, idan ya yi niyyar hajjin to hajjinsa ya inganta, sai dai ba zai wadatar masa ba daga hajjin da musulunci ya wajabta masa ba, sai dai ya zama nafila, saboda hadisin Xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Wata mata ta xaga wa Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) wani yaro qarami, ta ce, «Wannan yana da hajji?» sai Manzon Allah ya ce, “Eh, kuma kina da lada” [Muslim ne ya rawaito shi]

Ya Halatta Yaro Ya Yi Niyyar Hajji

4 – ‘Yanci

Hajji baya wajaba akan bawa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Duk bawan da ya yi aikin hajji, sannan aka ‘yanta shi, to a kansa akwai wani hajjin daban” [Muslim ne ya rawaito shi]

5 – Iko

Shi ne samun guzuri [Guzuri : shi ne abin ake buqata na abinci da abin sha da tufafi]da abin hawa [Abin Hawa shi ne : Abin da mutum zai hau na mota ko jigin sama ko na ruwa], saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Allah ya wajabta wa mutane ziyartar xakinsa ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, duk wanda ya kafirce (ya qi) to Allah mawadaci ne daga talikai”. (Ali- Imran : 97).

6 – Samun Muharrami Tare Da Mace

Saboda hadisin Xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, na ji Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana huxuba yana cewa : “Kada mace ta yi tafiya sai tare da muharraminta”

sai wani mutum ya tashi ta ce, “Ya Manzon Allah, matata ta fita hajji, ni kuma an rubuta ni zuwa yaqin kaza da kaza”.

Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce masa : “Je ka, ka yi hajji tare da matarka” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Sanya Wani Ya Yi Wa Wani Aikin Hajji

Wanda ya kasa yin hajji ko umara saboda tsufa, ko rashin lafiya wanda ba tsammanin za a warke, ko kuma saboda raunin jikinsa, ba zai iya hawa abin hawa ba, to wajibi ne a kansa ya wakilta wanda zai masa aikin hajji da umara, kuma hakan ya wadatar masa koda kuwa ya warke, bayan wakilinsa ya yi niyyar hajji ko umarar.

An karvo daga Fadlu xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, wata mace daga qabilar khas’am ta ce, “Ya Manzon Allah, farillar aikin hajji ta samu babana ya tsufa, baya iya daidaita a akan bayan raqumi” sai ya ce mata “ki yi masa hajji” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

Mutumin Da Ba Zai Iya Aikin Hajji Ba

Sharaxi ne duk wanda zai wakilci wani a aikin hajji ya cika waxannan sharuxxai :

1 – Ya zama ya cika sharuxxan aikin hajji da suka gabata.

2 – Wakilin ya zama ya yi aikin hajji a kansa. Idan wani ya yi wa wani aikin hajji, alhali bai tava yi wa kansa ba, hajjin da ya yi wani bata yi ba, hajjin ya zama na shi, ya sauke farillar hajji a kansa.

Dalili shi ne abin da ya tabbata daga Xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ji wani mutum yana cewa : “Allah na ansa maka a madadin Shubruma” Sai Manzon Allah ya ce, “Waye kuma Shubruma? Sai ya ce, “Wani xan uwana ne, ko makusanci na” sai Manzon Allah ya ce, “Kai ka yi aikin hajjin a a kanka” sai ya ce, “a’a” sai ya ce masa “Ka yi wa kanka hajji, sannan ka yi wa shubruma” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Umara

Bayanin Mene ne Umara

Umara a larabci

Ita ce Ziyara

Umara A Shari’ance

Ita ce, ziyarar xakin Allah mai alfarma a kowane lokaci, don yin wasu ayyuka kevantattu.

Hukuncin Umara Da Falalarta

Umara wajibi ce sau xaya kamar hajji, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Musulunci shi ne, ka shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Muhammad Manzon Allah, Ka tsayar da sallah, ka bada zakkah, ka ziyarci xakin Allah, ka yi umara, ka yi wankan janaba, ka cika alwala, ka yi azumin Ramadan” [Ibnu Khuzaima ne ya rawaito shi]

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sake cewa : “Tsakanin umara da umara yana kankare zunubin da yake tsakaninsu Hajjin da ya kuvuta daga laifi bai da wani sakamako sai Aljannah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]



Tags: