Falalar Azumi Da Hukuncinsa

26459

Bayanin menene azumi

Ma’anar kalmar "Azumi" a larabci

Kamewa da barin wani abu

Ma’anar Azumi a Shari’a

Shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faxuwar rana

Falalar Azumi

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa, rivi-rivi. Allah Maxaukakin Sarki ya rava azumi zuwa gare shi, saboda girmama shi da xaukaka shi.

Ya zo a cikin hadisi qudusi daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Dukkan aikin xan Adam ana ninka masa shi, ana ninka kyakkyawa sau goma, har zuwa ninki xari bakwai. Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai azumi, haqiqa shi nawa ne, ni ne nake ba da ladansa, mutum yana barin sha’awarsa da abincinsa saboda ni. Mai azumi yana da farin cikin biyu, farin ciki yayin buxa bakinsa, da farin ciki yayin haxuwa da Ubangijinsa. Warin bakin mai azumi ya fi almiski qanshi a wurin Allah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Hikimar Shar’anta Azumi

1 – Tabbatar da tsoron Allah, wajen amsa wa umarninsa, da biyayya ga shari’arsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “(An wajabta muku azumi ne) ko kwa samu tsoron Allah” (Albaqara : 183).

2 – Saba wa kai haquri, da qarfafa wa zuciya wajen danne sha’awa.

3 – Saba wa mutum da kyautatawa, da jin tausayin mabuqata da talakawa, saboda idan mutum ya xanxani yunwa zuciyarsa za ta yi laushi ta karkata zuwa ga mabuqata.

4 – Samun hutu a jiki da samun a lafiya a cikin azumi.

Hukuncin Yin Azumi

Azumin da Allah ya shar’anta ya kasu zuwa ga:

1 – Azumin Wajibi

Ya kasu gida biyu :

A – Azumin da Allah ne ya wajabta a kan bawa tun da farko, shi ne azumin watan Ramadan, kuma rukuni ne daga rukunan musulunci.

B – Azumin da bawa ne yake sababin wajabata wa kansa shi, kamar azumin bakance, da azumin kaffara.

2 – Azumin Mustahabbi

Shi ne dukkan azumin da shari’a take so a yi shi, kamar azumin ranar Litinin da Alhamis, da azumin kwana uku a kowane wata, da azumin ranar Ashura, da azumin goman farko a cikin watan Zulhijjah, da azumin ranar Arafa.

Sharuxxan Wajabcin Azumi

1 – Musulunci : Azumi ba ya wajaba a kan kafiri.

2 – Balaga : Azumi ba ya wajaba a kan yaro qarami, sai dai za a umarce shi da yi idan zai iya, don ya saba.

3 – Hankali : Azumi ba ya wajaba a kan Mahaukaci.

4 – Samun Iko : Azumi ba ya wajaba a kan wanda ba zai iya yi ba.

Azumin Watan Ramadan

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga rukunan musulunci, kuma farilla ne da Allah ya farlanta a kan bayinsa.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waxanda suke gabaninku don ku samu taqawa”. (Al-Baqarah: 183)

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai biyar” [Buhkari ne ya rawaito shi].

Sai ya ambaci “Azumin watan Ramadan” daga cikinsu.

Daga Cikin Falalar Watan Ramadan

1 – A watan Ramadan Ana buxe qofofin Aljannah, ana rufe qofofin wuta, ana xaure Shaixanu, zuciya tana fuskantar aikin alheri. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan Ramadan ya zo, sai a buxe qofofin sama, a rufe qofofin Jahannama, a xaure Shaixanu”.[Buhkari ne ya rawaito shi]

2 – Yin azumi da tsayuwar sallar asham saboda Allah da neman lada yana gafarta abin da ya gabata na zunubai. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi azumin watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Ya sake cewa : “Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”.[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

3 – A cikin watan Ramadan Akwai daren Lailatul Qadri, wanda Allah yake cewa a kansa “Daren lailatul Qadri ya fi wata dubu alheri”. (Alqadr : 3)

Duk wanda ya tsaya a cikin wannan dare yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya tsaya a daren lailatul Qadri yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

4 – Umara a cikin Ramadan tana daidai da yin aikin hajji tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ). Manzon Allah ya ce, “Umara a cikin Ramadan tana daidai da aikin hajji tare da ni” [Muslim ne ya rawaito shi]

5 – Watan Ramadan watan Alqur'ani ne, a cikinsa aka saukar da shi, don haka ya dace a yawaita karanta shi a cikin wannan wata.

Allah ya ce, “Watan Ramadan wanda aka saukar Alqur'ani a cikinsa, Shiriya ne ga mutane, da ayoyin bayanannu da rarrabe wa tsakanin qarya da gaskiya” (Albaqara : 185).

6 – Watan Ramadan wata ne na kyauta da ciyarwa da sadaka. An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “ Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi dukkan mutane kyauta, ya kasance lokacin da yafi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala'ika Jibrilu yake haxuwa da shi. Mala’ika Jibrilu yana haxuwa da shi a kowane dare a cikin Ramadan, ya yi karatun Alqur'ani tare da shi. Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya fi kowa kyauta lokacin da Mala'ika Jibriru yake haxu da shi, ya fi iska sakakkiya kyauta”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Da me Ake Tabbatar Da Kamawar Watan Ramadan?

Watan Ramadan ya tabbata da ganin wata, idan aka ga wata bayan faxuwar ranar ashirin da tara ga watan Sha’aban, to watan Ramadan ya kama, idan kuwa ba a ga wata ba, bayan faxuwar ranar talatin ga watan Sha’aban,

ko kuma wani abu ya hana ganinsa, kamar hadari, ko qura, ko hayaqi, to sai a cika lissafin watan Sha’aban kwana talatin.

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Ku yi azumi don ganin wata, ku sauke don ganinsa, idan an kare muku shi, to ku cika Sha’aban kwana talatin” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Karya Azumi

Karya azumi haramun ne, kuma yana daga cikin manya-manyan laifuka. Duk wanda ya karya azumin na rana xaya ba da wani uzuri ba, kuma bai tuba ba, to babu abin da zai isar masa, koda ya yi azumin zamani gabaxaya.

Saboda faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “Duk wanda ya karya azumi rana xaya daga Ramadan, ba a a kan wani rangwame da Allah ya yi masa ba, to azumin zamani gabaxaya ba zai rama masa ba” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Azabar wanda ya karya azumi da gangan mai girma ce. An karvo daga Abu Umamata Al-bahili – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Na ji Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana cewa, ina cikin barci, sai wasu mutane biyu suka zo min,…..sannan suka tafi da ni, sai kawai na ga wasu mutane an rataye su ta agararsu, muqamuqansu a tstssage, jini yana ta kwarara. Sai ya ce, na ce, su wanene waxannan? Sai ya ce, Waxannan waxanda suke karya azumi ne tun gabanin lokacin shan ruwa ya yi” [Ibn Hibban ne ya rawaito shi].



Tags: