Bayanin abin da ake nufi da saura
Saura
Shi ne abin da ya rage a cikin kwano bayan an sha
A qa’ida duk abin da aka sha aka rage mai tsarki ne, sai dai abin da dalili ya nuna cewa najasa ne.
1- Sauran abin da aka sha wanda yake mai tsarki
a) Abin da mutum ya sha ya rage
Saboda abin da ya tabbata na cewa “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana shan sauran Aisha – Allah ya yarda da ita – alhali tana cikin jinin al’ada, yana sanya bakinsa a inda ta sa bakinta ”[ Muslim ne ya rawaito shi]
Abin xan adam ya sha ya rage
b) Abin da mage ta sha ta rage
Saboda abin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya faxa game mage yayin da ta sha ruwa daga wata kwarya, ya ce, “Lallai ita ba najasa ba ce, ita tana cikin masu kai-kawo a cikinku” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Abin da mage ta sha ta rage
2- Abubuwan Da Aka Sha Aka Rage Waxanda Suke Najasa Ne
a) Sauran Kare
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Tsarkin kwanon xayanku idan kare ya yi lallage [ Lallage : shi ne kare ya sanya harshensa a cikin kwano ya jujjuya shi, ko ya sha abin da yake ci ko bai sha ba.] a cikinsa, ya wanke shi sau bakwai, na farko da qasa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
b) Abin Da Alade Ya Sha Ya Rage
Qiyasi a kan kare, saboda alade da kare dukkansu najasa ne.
Abin da alade ya sha ya rage
Abin da kare ya sha ya rage