Rukunan Aikin Hajji
1 – Harama (niyya)
saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Dukkan ayyuka basa karvuwa sai da niyya, kuma kowane mutum yana da sakamakon abin da ya yi niyya”[ Bukhari ne ya rawaito shi]
2 – Sa'ayi Tsakanin Safa Da Marwa,
saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Ku yi sa’ayi, haqiqa Allah ya wajabta muku sa’ayi” [Ahmad ne ya rawaito shi]
3 – Tsayuwa A Arafat,
saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Hajji shi ne tsayuwar Arafa” [Tirmizi ne ya rawaito shi]
4 – Xawaful Ifada,
saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Su yi xawafi ga xaki daxaxxe”. (Al-hajj : 29)
- Faxakarwa :
Wanda ya bar wani rukuni daga rukunan hajji, to hajjinsa bai yi ba, har sai ya zo da shi.
Wajiban Aikin Hajji.
1 – Yin harama daga miqati,
saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) bayan ya faxi wuraren miqati ya ce, “Waxannan miqatan na mutane garin ne, da waxanda suka zo ta hanyarsu, ga wanda yake da niyyar hajji da umara” [Bukhari ne ya rawaito shi]
2 – Tsayuwar Arfa har rana ta faxi
ga wanda ya zo da rana, saboda Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya tsaya har zuwa faxuwar rana.
3 – Kwana a Muzdalifa,
saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kwana a cikinta, ya ce, “Ku riqi yadda ake aikin hajji a wurina, don ni ban sani ba, wataqila ba zan sake haxuwa da ku ba bayan wannan shekara” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi]
Kuma saboda Manzon Allah ya yi wa masu rauni izinin tafiya bayan dare ya raba, sai wannan ya nuna cewa kwana a Muzdalifa dole ne.
sannan kuma Allah ya yi umarni da ambatonsa a wurin da ake kira “Mash’arul Haram” a Muzdalifa.
4 – Kwana a Mina a dararen Kwanakin Yanyana
saboda abin da ya tabbata daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) na cewa “Ya yi rangwame ga masu kiwon dabbobi kada su kwana a Mina” [Abu Ya’ala ne ya rawaito shi a littafinsa «Musnad»]
Wannan yake nuna cewa asali kwanar Mina Wajibi ne.
5 – Jifan wuraren jifa uku
saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ku ambaci Allah a cikin wasu kwanaki qididdigaggu” (Al-baqra 203)
kwanaki qididdigaggu su ne kwanakin ‘yanyana. Jifan majefa yana cikin ambaton Allah Maxaukakin Sarki, saboda Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An sanya xawafi ga xakin Allah da sa’ayi tsakanin Safa da Marwa da jifa don tsayar da ambaton Allah” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]
6 – Aske gashin kai gabaxaya ko saisaye
saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Tabbas zaku shiga masallacin harami – in sha Allahu – kuna masu aske kanku gabaxaya ko kuna masu saisaye” (Al-fathu : 27).
7 – Xawafin ban-kwana,
saboda abin da ya tabbata daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “An umarci mutane ya zama qarshen lamarinsu ga Makkah xawafi ga Ka’abah, sai dai an yi mai haila rangwame” [Muslim ne ya rawaito shi]
Sunnonin Aikin Hajji
Duk abin da ba rukuni ko wajibi ba, to sunna ne, kamar abubuwan da za su zo :
1 – Wanka yayi sanya Ihrami
2 – Yin ihrami a cikin kwarjalle da mayafi farare.
3 – Yin talbiyya da xaga murya da ita.
4 – Kwana a Mina daren ranar Arafa
5 – Sumbatar baqin dutse.
6 – Yaye kafaxu yayin yin xawafin qudumi ko umara, shi ne sanya mayafi qarqashin hammatar dama
7 – Yin sarsarfa a zagayen ukun farko na xawafin qudumi ko umara.
8 – Yin xawafil qudumi ga wanda yake qirani, da mai yin Ifradi
Sunnonin Hajji
Wanda ya bar sunna daga cikin sunnonin aikin hajji, babu komai a kansa, hajjinsa ya inganta
Wajiban Aikin Hajji
Wanda ya bar wajibi a aikin hajji to tilas ne ya yi yanka don ceke givin abin ya bari.